Karanta jerin sunaye dakuma Hotunan masu taimakawa ‘yan Ta’adda da makamai a zamfara

 Karanta jerin sunaye dakuma Hotunan masu taimakawa’yan Ta’adda a zamfara da gwamnatin jahar tayi ikirarin kamawa

Gwamnan jahar zamfara Alhaji Bello matawallen maradun
Jihar zamfara dai nacikin jerin jahohin nigeria dasukayi suna a fannin noma kafin bisani matsalar tsaro tazo ta addabi yankin, wanda yanzu a iya cewa jahar nacikin jerin jahohin Arewacin Nigeria mafi matsalar tsaro kama daga kidnapping, Robbery, dakuma satan shanun makiyaya dadai sauransu.
Matsalar tsaron ta zamfara state tafara kamarine tun lokacin mulkin tsohon gwamnan jahar Abdulazizu yari indama wasu suka Rika zarginsa da sakaci akan lamarin tsaron jahar yayinda yake nuna cewa gwamnatin tarayya ce keda alhakin tsaron jahar bashiba.
Abaya bayannan gwamna maici wato Alhaji Bello matawallen maradun yayi Rantsuwar wanke kai inda yanuna bayada hannu a matsalar tsaron jahar kokuma wata Alaka da yan bindiga kana yayi Alkawarin zakulo dakuma ganin an hukunta masu hannu a matsalar.
Yanzudai gwamnatin ta jahar zamfara tayi nasarar gano tare da kama wasu mutun 7 da suke taimakawa yan bindiga daga cikinsu akwai
Dagacin wani kauye
Wani ma’aikacin kaki
Ma aikacin Asibiti wato likita dadai sauransu.
Ankama ma’aikacin kakin ne lokacin da yake kokarin hannanta bollet ( Alburusai) ga wani sanannen dan Ta’adda inda yasanarda cewa yasayi Alburusan ne akan kudi Naira dubu dari daya (100,000).
Haka zalika ma’aikacin lafiya ma an sameshi da rakalumman sojoji har taki goma abunda ke kara tabbatar da Alakarshi da ‘Yan Ta’addar.
Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top