Bikin Sallah: Fitilar Danbatta ta shirya tseren keken matasa karo na biyu

 Bikin Sallah: Fitilar Dambatta Ta Shirya Tseren Keke Karo Na Biyu

 

Tseren keken Fitilar Danbatta

Mujallar yaɗa labarai a matakin ƙaramar hukumar Dambatta wato FITILAR DAMBATTA ta sake shirya gasar tseren keke a karo na biyu (2) a Karamar Hukumar Dambatta da Makoda.

Da yake magana shugaban kwamitin tsare tsare na gudun tseren, Auwalu Nakarkata Dambatta ya ce, nan bada jimawa ba za’a sanar da lokacin da za’a fara sayar da form din shiga gasar kamar yanda aka yi a baya.

Auwalu ya ƙara da cewa; ana shirya wannan gasa ne domin sada zumunci tsakanin matasa da nishadantar da al’ umma da nunawa jama’a mahimmanci motsa jiki ga lafiyar ɗan Adam.

Auwalu ya ƙara da cewa; a wannan karon mun faɗaɗa wasan har zuwa Ƙaramar Hukumar Makoɗa dan kara dankon zumunci da karfafa alaƙa tsakanin matasan yankunan biyu.

A karshe akwai kyaututtuka masu yawa ga wanÉ—anda suka lashe wannan gasa daga gurbi na daya (1) har zuwa na Uku (3). 

Sannan akwai shaidar karramawa da za a ba kowane Ɗanwasa. Kwai kyaututtukan da muke sa rai za a samu daga hannun jama’a kamar yanda aka samu a waccan karon.

 A wannan karon idan an samu da yawa za duba yiwuwar bayar da kyauta har zuwa na biyar (5).

Wannan tseren keken matasa yana taka muhimmiyar rawa sosai wurin hadinkan al-ummar Danbatta dakuma makoda harda kara dankon zumunci nishadi dasauransu.

Haka zalika za’ayi iya kokari wurin tabbatar da gaskiya da Adalci kamar yadda aka saba wurin tantancewa dakuma fitarda gwarajen mahaya keke din.

Wannan tseren keken Fitilar yana fito da shahararrun mahaya na wannan yanki tareda tantancesu.

Agajahub publisher zasu kawo muku bayanin yadda ta kaya tsakanin mahayan dakuma kyaututtukan da zasu samu.

Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top