DALILAI GUDA 5 DAKE IYA HANA APC LASHE ZABE MAI ZUWA NA 2023

DALILAI GUDA 5 DAKE IYA HANA APC LASHE ZABE MAI ZUWA NA 2023

 Jerin dalilai biyar dake barazana wa nasarar lashe Zaben 2023 babbar jam’iyya mai mulki wato APC a zabe mai zuwa.

APC/ Shugaban Nigeria Muhammadu buhari

Wannan shafi na Agajahub publisher yayi nazari akan abubuwa bakwai dake iya zama sanadiyyar rashin nasara a zabe mai zuwa, haka zalika zamu kawo muku cikakken bayani akan bincikenda Agajahub publisher.

Jerin dalilai bakwai dake barazana wa nasarar lashe Zaben 2023 ga jam’iyyar APC mai mulki

 1. Matsalar tsaron 

Matsalar tsaron dake addabar Nigeria kamar kidnapping, fashi da makami, bokoharam da sauransu, itace babbar barazana ga wannan gwamnati mai mulki dakuma kasa baki daya.
Gwamnatin shugaba buhari ta gaji wannan matsalar ne daga hannun gwamnatinda ta gabata ta Good luck Jonathan a shekarar 2015.
Matsalar kidnapping takarayin kamarine a wannan gwamnati inda har kidnerpers suka fara kame garuruwa a jahohin Arewacin Nigeria kamar su zamfara state dakuma Niger state.
Wannan matsalar tasaka karan tsana tsakanin talakawa dakuma gwamnatin APC inda har jam’iyyar adawa kesamun bakin suka dukda cewa sun tafka nasu shirmen.
Atakaice dai zuwa campaign a wasu kauyuka nada wuya ga jam’iyyar APC yana kuma da sauki ga jam’iyyar adawa ta PDP.
 TA’ADDANCI
‘Yadda rashin tsaro ya yi wa tattalin arzikin arewacin Najeriya illa’
‘Monday Market’ daya daga cikin kasuwanni mafi girma da kuma bunkasar hada-hada a birnin Maiduguri dake jihar Borno, wadda ta fuskanci jerin hare-haren ‘yan kunar bakin wake na kungiyar Boko Haram, sai dai barazanar tsaron bai hana ta cigaba da wanzuwa ba. 26/7/2019.
‘Monday Market’ daya daga cikin kasuwanni mafi girma da kuma bunkasar hada-hada a birnin Maiduguri dake jihar Borno, wadda ta fuskanci jerin hare-haren ‘yan kunar bakin wake na kungiyar Boko Haram, sai dai barazanar tsaron bai hana ta cigaba da wanzuwa ba. 26/7/2019. RFI/Fati Abubakar
Zubin rubutu:
Bashir Ibrahim Idris
Minti 7
Kafin shekara ta 2007, Yankin Arewacin Najeriya ke sahun gaba wajen ayyukan samar da abincin da ya shafi noma da kiwo ga daukacin Najeriya da kasashen dake makotaka da ita, tare da gudanar da harkokin kasuwanci.
Sai dai rikicin Boko Haram da a yanzu haka ya kai shekaru 14 ba tare da gushewa ba, yayi kuma matukar illa ga Jihohin Borno da Yobe da Adamawa wadanda ke sahun gaba wajen harkar noma da kiwo ganin yadda yayi sanadiyar mutuwar mutane kusan dubu 40,000 da kuma raba sama da wasu miliyan biyu da rabi daga matsugunan su a yankin.
Sansanin Muna dake garin Maiduguri mai dauke da dubban ‘yan gudun hijirar da rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu. 1/12/2016.
Sansanin Muna dake garin Maiduguri mai dauke da dubban
  ‘yan gudun hijirar da rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu.
1/12/2016. © REUTERS/Afolabi Sotunde/File Photo

 
Wannan rikici ya kuma hana dubban mutane zuwa gonakinsu, matsalar da ta taimaka wajen rage gonakin da aka saba nomawa da kuma takaita abincin da ake samarwa ta hanyar noma da kiwo.
Harkokin kasuwanci ma basu tsira ba a wannan yanki mai dimbin jama’a, ganin yadda rayuwa ta tagayyara, zirga zirga suka takaita, mu’amala ta fuskanci koma baya, jama’a suka koma zama cikin mummunan yanayin fargaba da kuma shakku kan abinda kan iya zuwa ya komo.
Yayin da ake kokarin shawo kan wannan matsala ta Boko Haram da ta takaita a Jihohi 3 na Arewa maso Gabashin Najeriya, da kuma wasu sassan kasashen Nijar da Kamaru da Chadi, sai kuma matsalar ‘yan bindiga barayin shanu ta bullo a Yankin Arewa Maso Yammacin Najeriya, kuma nan da nan ta yadu zuwa daukacin Jihohin Zamfara da Katsina da Kaduna da kuma Niger wajen kashe makiyaya ana kwashe shanunsu.
Hoto domin misalin dake siffanta ‘yan bindiga a Najeriya.
Hoto domin misalin dake siffanta ‘yan bindiga a Najeriya
 REUTERS/Goran Tomasevic/File Photo

Ganin yadda matsalar ta fadada ta sanya akasarin makiyayan dake wadannan yankunan suka rabu da dabbobin su da suka saba rayuwa da su, yayin da wasu da dama kuma suka rasa rayukansu, ba tare da hukumomin da alhakin ya rataya kansu sun dauki matakan da suka dace ba wajen dakile wannan aika aika.
Wannan ya sa wasu da aka raba su da dabbobinsu, suma suka dauki makamai suka shiga cikin jerin masu aikata laifuffuka na fashi da makami da garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa da kuma kai munanan hare hare garuruwa suna kashe mutane baji ba gani.
Yayin da ake fama da wannan matsalar, harkokin yau da kullum a wadannan yankuna sun gagara, manoma sun kasa zuwa gonakinsu, ‘yan kasuwa sun daina tafiye tafiyen da suka saba domin gudanar da harkokin kasuwancinsu, saboda yadda ‘yan bindiga ke tare hanya suna farautarsu suna kuma kashe mutane da kuma garkuwa da wasu.
Rahotanni sun ce wasu yankunan har haraji suke baiwa wadannan ‘yan bindiga kafin zuwa gonakin da za su noma, haka kuma suke biyan kudi kafin girbi domin kawo abincin da suka noma zuwa gida.
Wasu makiyaya yayin kiwon dabbobinsu a wajen garin Zaria dake jihar Kaduna a Najeriya.
 15/11/2016.

Wasu makiyaya yayin kiwon dabbobinsu a wajen garin Zaria dake jihar Kaduna a Najeriya. 15/11/2016. REUTERS – AKINTUNDE AKINLEYE
Sannu a hankali wannan matsala ta fadada zuwa akasarin Jihohin dake arewa maso yamma da kuma wasu jihohin dake Arewa ta Tsakiya, harma da birnin Abuja, cibiyar gwamnatin Najeriya, saboda yadda ake kai hari ana sace mutane a gidajen su ko kuma a tare su akan hanya.
Shi kuwa yankin Arewa ta Tsakiya na fama ne da rikicin manoma da makiyaya da kuma kabilanci da na addini wanda yayi masa matukar illa ganin irin asarar rayuka da kuma dukiyoyin jama’a da ake yi.
Wadannan dimbin matsaloli yanzu haka sun yiwa yankin arewacin Najeriya matukar illa wajen hana noma da kiwo a sassa daban daban da kuma hana harkokin kasuwanci saboda hatsarin dake tattare da tafiye tafiye a yankin baki daya sakamakon ayyukan ‘yan bindiga.
Bakin ‘yan kasuwa na fargabar zuwa Najeriya saboda rashin tsaro
Wannan tashin hankali ya kuma hana bakin ‘yan kasuwar da suka saba zuwa daga kudancin Najeriya zuwa yankin da ma masu zuwa daga kasashen dake makotaka da Najeriya, harma da masu zuba jari dake shigowa Najeriya daga kasashen duniya.
Yau ta kai ga dubban mutanen da wadannan matsaloli suka addabi yankunansu, sun talauce saboda asarar ‘yan uwansu da dukiyoyinsu da ma gonakinsu da basa iya zuwa nomawa saboda fargabar abinda ke iya faruwa da su daga irin wadannan mahara.
Dalilin wannan matsala, tattalin arzikin yankin arewacin Najeriya na cigaba da tagayyara, rayuwar jama’a na dada shiga halin kunci da fargaba a koda yaushe, yayin da harkokin kasuwanci suka tsaya cik a yankin.
Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI
Mazauna wannan yankin sai dada talaucewa suke sakamakon wadannan matsaloli, yayin da wasu ke kaura zuwa wasu yankunan koma barin kasar baki daya domin samarwa kan su mafita daga wannan al’amari.
Wani kauye da ‘yan bindiga suka tilastawa mutane masu yawan gaske tsrewa a karamar hukumar Jibiya dake jihar Katsina a Najeriya.
Wani kauye da ‘yan bindiga suka tilastawa mutane masu yawan gaske tsrewa a karamar hukumar Jibiya dake jihar Katsina a Najeriya. © Daily Trust

 
Rahotanni sun ce yanzu haka garuruwa da kauyuka da dama dake yankunan karkara a Jihohin Arewa maso Yamma sun zama kufai sakamakon tserewar da mazauna garuruwan suka yi domin kaucewa hare haren wadannan ‘yan ta’adda da basu mayar da ran Bil Adama komai ba.
Yau gidaje da dama sun talauce saboda yadda gidaje suke karyar da kadarorinsu da suka hada da gidaje da gonaki da ababen hawa suna sayarwa domin biyan kudaden fansar kubutar da ‘yan uwansu da suka fada tarkon masu garkuwa da mutane domin ceto rayukansu. Wasu daga cikinsu ma basa kubuta ko da an biya kudin fansar sai an kasha su.
Wasu sojojin Najeriya.
Wasu sojojin Najeriya. © AFP

Gwamnatin Najeriya dai tace tana iya bakin kokarin ta wajen ganin ta shawo kan wadannan dimbin matsalolin da suka addabi Yankin da ma kasa baki daya, amma ga alama har yanzu akwai sauran aiki, domin kuwa dambu idan yayi yawa baya jin mai, a daidai lokacin da aka toshe wata kofa, sai wata ta bude dangane da dimbin matsalolin tsaron da suka addabi Yankin arewacin Najeriya da kuma kasar baki daya.

2. Tsadar Rayu dakuma kayan masarufi

Ysadar rayuwa a Nigeria

MATSALAR YUNWA DA TSADAR RAYUWA YA KAMATA MU FADAWA JUNA GASKIYA.
Daga Muazu Umar Hardawa Bauchi.
Halin da muke ciki na tsadar rayuwa da talauci wasu na ganin babu laifi daga shugabanni Allah ne ya kawo har suna danganta lamarin da cewa lokacin annabi anyi irin wannan wahala, alhali wancan lokaci kowa ya sani annabi da sahabbai basa ci sai kowa ya ci.
Kuma annabi ya ce kowane shugaba zai zo daure ranar lahira adalci da yayi wa talakawa shine zai kunce shi, idan har mun yarda da wannan hadisi mu danganta shi da wannan lokaci da sanata daya ke karbar.milyan 30 albashi a wata daya kudin kusan farfesa 50 da ke koyarwa a jamia.
Sanin kowane lokacin annabi saw babu rufe boda saiko a samu fari ko talauci da raahi,a tafi sham a tafi madina ko habasha kasuwanci halas ne. Amma yanzu ance yin kasuwanci haramne da wata kasa kowa yayi noma ya cida bakinsa alhali ba kudin nomar ba abinda za a ci ayi nomar wani wajen ba filin nomar me ake nufi kenan.
Don haka yanzu kowa ya sani gangancine kowa ya rufe kasarsa babu abinci yasan dole Wanda ya saya ya tara yayi rashin tausayin talakawa. Bayan haka Kuma dole a samu rashin tsaro da aikata miyagun ayyuka don ciyar da kai. Saboda idan wani ya rage buri ya nema daga halas ko ya kwana da yunwa wasu zasu shiga aikata laifi musamman matasa da Yan mata da zawarawa don neman abin da za su cida bakinsu.
Ko rantsuwa na Yi nasan bazan yi kaffara ba, nasan kudin da ake kashewa wajen gyara tarbiyya da yaki da ya taadda wadanda rufe kan iyaka ya karya su, ribar nomar shinkafa ba zata cike gurbin kudin da ake kashewa wajen sayen makamai da kayan aiki don seta mutane ba.
Baa maganar rai da dukiyar da ake rabawa danlalacewar tarbiyya da zinace zinace da shaye shaye don neman biyan bukata.
Idan da Saudi da kuwait ko German ko ingila ko Dubai da sauransu sun rufe kasa suce baza su shigo da abinci daga wata kasa ba suga yadda za su kasance da talakawa, kowa ya sani kudin biredi da mai shugaban Sudan Albashir.ya kara sanadiyyar zamga zanga kenan saida ya bar mulki ya faru a kasashe da dama mun gani gwamnati da yawa sun rushe saboda tsadar rayuwa da karancin abinci.
Rashin kishi da tausayin talakawa da rashin imani ya kawo tsadar abinci da kayayyaki saboda an sa jari hujja masu hali.sun noma wasu sun saye abinci an barsu sai farashin da suka da suke sayarwa kanan Yan kasuwa masu neman.su sayar su sami abinci. An bar wasu shafaffu da mai sai abin da suka dama suke Yi. Masu tausaya wa su sayo su sayar su samu abinci mutane su samu rangwame duk an karya su, sun koma cikin talauci su day iyalansu da yaransu sun dukufa da addua Allah ya bi musu kadi shi yasa idan yau an toshe nan sai gobe can ta bude amma an kasa hankalta a nemi masana tattalin arziki da zantakewa da kasuwanci da malaman jamia da na addini a nemi shawarar su a dauka don a samu mafita saboda su shugabanni basa cikin wahala.
Idan gwamnati ta ga dama cikin kankanen lokaci farashi zai sauka a koma walwala kamar yadda suka samu kasar. Saboda ko abinci da kwastam suka kama aka rabawa maaikata a farashi mai.sauki ya watsu a cikin kasa dole farashin kayan masarufi ya sauka.
Ko yau idan kana da dan uwa kwastam idan ya ga dama zai iya maka dalilin sayen shinkafa da suka kama a dubu takwas buhu da manja da taliya da sauransu duk suna sayarwa masoyansu ko su tura musu kyauta a birni muna kallo.
Amma kada ku mance kayan masarufi na Yan kasuwa ne da suka sayo don su sayar su cida iyalansu aka kame harda motocin da ke dauke da irin wannan kaya duk Wanda yasan akwai ofishin kwastam a garin su ko daga bakin hanya ya leka zai hango kayan birjik suna ta lalacewa. Idan a Bauchi mutum yake yaje yalwa gidan kwastam daga kan kwalta zai hango kayan mutane da aka kama
A irin su Kano da Katsina da legas suna da manyan store da ake Kira ware house cike yake da kayan bayin Allah Yan kasuwa da aka kama Kuma an karya su da iyalansu da maaikatan su da Yan uwansu. A baya konawa ake Yi saida kumgiyoyin kare hakkin Dan adam suka tsaya kafin ake turawa Yan gudun hijra Wanda ya Dan lalace Kuma a kona. Wani lokaci har inda ake kona kayan masarufi talakawa ke bi su tone Wanda wutar bata Kai gare Shi ba su kwasa suje su ci.
Idan kaje mashigin ruwa a kudu da filayen jiragen sama da kan iyakoki sama da dubu wato bododin Nigeria duk zaka ga irin wannan kaya na Yan kasuwa da aka kama wanima Yana niger ko kamaru ko chadi ko cotona Yana ta.lalacewa an Hana a shigo da Shi Kuma dukiyar Yan kasuwa ne da za su amfani kasa a fita daga wahalar Amma saboda mugunta an musu jiki magayi an karya su.
Kada ku mance duk Wanda aka zalunta ba zai ce Allah ya Yi albarka ba saiko Allah ya tsine ko Allah ya Isa kuma Allah zai bi kadin sa.
Shi ya sa ko abinci suka ci baya maganin yunwa ko a sayarwa mutum kayan araha aci a gamu da lalura saboda kullum dan kasuwar da aka karya muguwar addua yakewa kasar da shugabannin wanima yasin zai sa ayi ta saukewa Allah ya bi masa kadi don haka kullum lamarin ke.kara lalacewa, talakawa kuka me mulki kuka jamiin tsaro kuka hatta dan banga kuka yake Yi.
Wanda baizo duniya bama Yana cikin uwarsa idan an mata scanning sai ace bshi da lafiya. Kai hatta jaririn da aka aifa uwa bata ci ba balle ya samu ruwan nono idan an gwada shi Sai ace yana da ulcer, wannan wane irin balaine a kasa me arzikin mai da noma da maadinai irin Nigeria.
Abin takaici karamin mudun shinkafa yar gida me tsakuwa naira 700 masara garinta 400 a nijer buhun shinkafa dubu 13 a Nigeria dubu 23 buhu. Kuma kowa ya sani mafi karancin albashi naira dubu 15 zuwa dubu 30. Me digiri a jaha albashi dubu 37 a federal dubu 60. Kurtun Dan sanda ko soja an bashi bindiga ya kwana a daji Yana tsaron kasa da jamaa albashinsa dubu 60 hakama ta yiwu ba a biya shi a kan lokaci ba idan ka je gidansa yana da iyali da Yan uwa dake gani yana aiki kullum suma masa waya abinci ya kare Kuma ace an samu nasarar yaki da cin hanci da rashawa. Ya kamata mu daina yaudarar kan.mu mu gayawa juna gaskiya a daina dorawa Allah laifi mu fito mu gayawa shugabanni gaskiya don su gyara.
Wallahi bana ganin laifin shugaban kasa Buhari saboda duk wahala da ake sha talakawa akwai Wanda basu yarda akwai matsala ta shugabanni bane cewa suke Allah ne. Alhali sai an gayawa shugabanni ana cikin wahala kafin su gyara don kada su gamu da boren talakawa tunda sun fi kowa.son zama a kujerar mulki cikin salama.
Amma tun da talaka yace ba laifin shugabanni bane talauci da tsadar abinci daga Allah ne to shi yasa Allah ya bar talaka da dabarar sa ya jira Allah ya masa ruwan kudi ko abinci daga sama shikenan, Amma a sani talakawa a arewa kirista da musulmi suna da hakuri da yiwa gwamnati uzuri saboda sun yarda da Allah. Amma Yan kudu ba za su ci gaba da zuba ido suna gani talauci da ganganci na musu cin kaca su zuba ido har Nan da shekara uku cikin wannan yanayi ba dole su fusata su kalubalanci gwamnati a kotu ko Kuma ta kowace hanya da suke ganin za su iya.
Ya kamata Yan arewa su lura Yan kudu sun koma.gefe sun Yi bakam sun Yi shiru hatta mataimakin shugaban kasa ya Yi shiru sun zuba mana ido don haka ya kamata mu hankalta mu nemi mafita a gyara kasa tun dare Bai yiwa Yan arewa ba.
Saboda duk da wahalar da ake sha wani lokaci da kudin ana neman abinci a saya babu. Abin takaici a jiya Ministan Noma Nanono ya fito a radio yana cewa baza su bari a shigo da abinci ba duk wahala da za a shiga saiko a shiga me yake nufi da wannan kalami ya nuna duk mutuwa da za a Yi saboda yunwa ayi bata dame su ba.
Nigeria ba Niger bane mutum milyan 200 ba wasa ba idan noma ake Ina taki Ina kudi ina kwanciyar hankali ko filin nomar. Wanda ke Lagos ko kalaba.da kudanci ina zai yi nomar. A arewa an kawo yanayin da kana gonar idan aka sace ka sai an sayar da gonar da gidanka ba a fansheka ba, to ance milyan daya zuwa goma a kauye Wanda gidan da gonar suka Kai wannan.kudi sai attajirin gaske.
Shawara a nan mu fadawa kan mu gaskiya Allah ya kawo mana mafita ya mana maganin duk me hannu a cikin wannan wahala da tsadar abinci ko shi wanene Allah ya mana maganinsu tunda a cikin su babu annabi ko sahabi ko tabii Allah ka gaggauta kawo mana karshen duk wani shugaban da bai damu da halin talauci da yunwa da kunci na rayuwa da rashin aikin Yi da ake fama da shi ba. Allah ka kawo mana mafita cikin gaggawa ba don halin.mu ko halin.wawayen cikin mu ba.
Ya Allah ka sani ko rantsuwa na Yi ba zanyi kaffara ba gidajen shugabanni ba a fiskantar barazanar yunwa ba a cin shinkafa yar gida. Allah ka bi mana kadi cikin gaggawa kasa su gane, idan ba masu ganewa bane Allah ka gaggauta kawo mafita ka mana maganinsu a ruwan sanyi don mu samu salama a rayuwa.
Daya Muazu Umar Hardawa Editor ALHERI newspapers Bauchi Nigeria 07011546797
3. TALAUCI
  
Matsalar TALAUCI zatayi tasiri sosai wurin canja tunanin talakawa domin zabawa jam’iyyar adawa saboda mastin talauci da talakawan Nijeriya ke ciki.
Kabiru Sa’idu Sufi, mai sharhi kan lamuran yau da kullum kuma Malami a kan harkokin siyasa a Kwalejin Share Fagen Shiga Jami’a da ke Kano, ya ce talauci ne babbar matsalar da ta fi addabar arewacin Najeriya a yanzu idan aka kwatanta da ɓangaren kudanci.
“Matsalar tattalin arziki ce ta ɗaya a Arewa idan aka kwatanta da Kudu, saboda ƙididdiga ta nuna cewa talauci ya fi yawa a Arewa ɗin,” in ji shi.
“Idan kana tahowa daga Legas ko Fatakwal za ga kana kusanto Arewa kana ƙara ganin bambancin tattalin arzikin.”
Game da hanyoyin da za a bi wurin maganin matsalolin, masanin kimiyyar siyasar ya ce sai an samar da yanayin da matasa za su ƙirƙiri harkokin kasuwanci da kansu.
“Lallai sai an ƙirƙiri masana’antu na zamani kamar na harkar sadarwa da sauransu, kar a dogara da harkar saye da sayarwa kawai.”
Ya ƙara da cewa “shi kansa saye da sayarwar da akwai kuɗi a hannun jama’a zai inganta sosai, saboda haka wajibi ne gwamnati ta samar da wasu hanyoyi ta yadda matasa za su iya buɗe harkokin kasuwanci da kansu”.
 Daga BBC Hausa.
4. MAGUDIN ZABE 
MAGUDIN ZABE

Duk lokacin da aka yi batun magudin zabe a Nigeria, babu wandanda ake hange a matsayin su kadai ke da hannu kamar yan siyasa da jami’an tsaro da kuma jami’an hukumar zabe.
Sai dai matasa sune ake ga yan siyasar na amfani dasu wajen kwace akwatuna da ma sauran hanyoyi na magudi, inda su kuma suke basu na goro.
Matasa da dama dai su kan bari ayi amfani dasu wajen magudin zabe, inda suke fakewa cewa talaucine ya tilasta musu yin hakan.
Wakilinmu a Kano Yusuf Ibrahim Yakasai ya hada mana rahoto kan yadda yan siyasar kan yi amfani da matasa wajen magudin zabe a Nigeria.

5. Cin hanci da rashawa

Matsalar cin hanci da rashawa babban kalubale ce ga zabukkan Najeriya kama daga sayen katin zabe, Alkalan zabe, yan daba jami’an tsaro dasauransu.
Wani abin da ake yaba wa gwamnatin Muhammadu Buhari a kai shi ne rawar-ganin da take takawa wajen yaƙi da cin hanci da rashawa.
Wasu dai na ganin an samu nasara, don kuwa a karon farko an gurfanar da wasu manyan jami`an gwamnati da alkalai har ma da shugabannin siyasa da ake zargin sun tafka almundahana da dukiyar ƙasa a gaban kotu.
Amma wasu na zargin cewa yaƙin ya fi karkata a kan `yan adawa ko waɗanda ba sa ɗasawa da sabuwar gwamnati.
Sai dai Shugaba Buhari ya ce bai kullaci kowa ba, don haka ba shi da niyyar ramuwar gayya.
Shugaban Nijeriyar ya yi yunkurin sauya tsarin kyautata rayuwar al`ummar yankin Niger-delta mai arzikin mai.
Sai dai wannan albishir na inganta rayuwar al`ummar Niger-Delta bai ratsa zukatan masu ta-da-kayar-baya ba, idan aka yi la’akari da irin luguden bama-baman da suka yi ta yi a kan bututan mai da iskar gas da ke yankin.
Hakan dai ya haddasa asara mai yawa tare da rage yawan man da Najeriya ke fitarwa, ga kuma jefa al`ummar ƙasar a cikin matsalar ƙaranci ko rashin wutar lantarki. 
Amma har yanzu akwai rina a kaba saboda masu yaki da abun suke yimasa zagon kasa.
Ko da yake, za a iya cewa harin ya lafa a ɗan tsakanin nan, bayan wani rangadi da muƙaddashin shugaban ƙasar Yemi Osinbajo ya kai yankin.
Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top