Jerin Abubuwa 20 da Gwamnatina Tayina Alheri Baya, NLC Bata Yababa- El-Rufa’i

HALIN DA AKE CIKI A JIHAR KADUNA daga Nasir El-Rufa’i

Nasiru El-Rufa’i

Gwamnan jahar KADUNA malam Nasir El-Rufa’i ya fitarda Jerin Abubuwa 20 da gwamnatimsa tayiwa jahar KADUNA na Alheri wanda ko kadan NLC basuyi maganar yabo akai ba.

Yasanarda hakan ne a shafinsa na facebook page mai suna The KADUNA State government.

Ga bayanin malan 

 Rubutaccencencen jawabi ga manema labaru da kwamishinan Kananan Hukumomi da kuma Shugaban Ma’aikata suka gabatar, 15 Mayu 2021

‘Yan Jarida/Manema Labaru,

1. Muna masu gabatar muku da wannan jawabi a madadin Gwamnatin Jihar Kaduna:

2. A watan Satumba na 2019, gwamnatin jihar Kaduna ce ta zama gwamnati ta farko a kowanne mataki a Nijeriya wajen biyan sabon albashi mafi karanci tare da yi wa albashin gyaran da ya kamata don sauke nauyin da ke nan. Ba tare da wani jinkiri ba, aka kara kudaden fansho ya koma Naira dubu 30 mafi karanci ga ‘yan fansho da ake biya da tsohon tsari. Haka nan kananan hukumomi 23 na jihar Kaduna suka bi sahu suka soma biyan sabon albashin. Duk da dinbin matsaloli na kudi da muke ta fama da su cikin shekaru shida da suka gabata, gwamnatin jihar Kaduna ta ci gaba da ba da muhimmanci ga kokarinta na gudanar da manyan ayyuka da biyan hakkoki na ma’aikata musamman albashi.

3. Har ila yau jihar Kaduna na daya daga cikin jihohi da ba su taba fasa aiwatar da tsarin nan na fansho na karo-karo ba, tsakanin gwamnati da ma’aikaci ba, tun daga 1 ga watan Janairu na 2017. Kuma ba ta yi sanya ba, ta yunkura wajen biyan Naira Biliyan 14 kudaden da ta gada na hakkokin ma’aikata da suka riga mu gidan gaskiya da na wadanda ke raye, da suke bi bashi tun shekarar 2010. Aka soma da biyan wadanda suka fi dadewa da barin aiki. Daga shekarar 2015, Gwamnatin jihar Kaduna ta biya fiye da Naira Biliyan 13 hakkoki na ma’aikata da suka riga mu gidan gaskiya, da na wadanda sun bar aikin suna raye.

4. A kokarin da ta dukufa yi wa bangaren aikin gwamnati sanin muhimmancinsa ga isar da ayyuka masu inganci da alfanu ga al’umar jihar Kaduna, wannan gwamnati ta bullo da tsare-tsare na yin gyara da farfado da tsarin a shekarar 2016. Babban burin shi ne sabunta bangaren da sanya shi ya zama mai inganci fiye da yadda yake da tafiyar da sabuwar hanyar sadarwa ta intanet. Bayan malamai da ma’aikatan lafiya, wannan gwamnatin ta ci gaba da daukar kwararru da ake bukata a hukumominta. Ta samar da sabbin ayyukan yi, da kawar da ma’aikata daga matakin da suka tsofe ko daina aiki. Ta ci gaba da kashe kudi ga horas da ma’aikata, da sadaukar da kashi 2 cikin 100 na kason da ake samu duk wata daga gwamnatin tarayya, da dagewa wajen zuba jari ga gina ma’aikata, da bunkasa kwazonsu.

5. A matsayin ma’aikata da ke zaune a gidajen haya, gwamnatin jjhar Kaduna ta sayar wa ma’aikatan yawancin gidajen da ba su zama tilas gwamnati ta ci gaba da mallakarsu ba a shekarar 2017, kuma gwamnati ta musu tsarin da za su iya biyan gidajen cikin sauki, ba da wata muguwar riba ba.

6. Saboda haka, wannan gwamnatin ta nuna a zahiri cewa ita mai kaunar kyautata jin dadin ma’aikatanta ne. Sai dai ta dage cewa hakan zai ci gaba da dorewa ne, kadai, ta la’akari da jin dadin sauran mazauna jihar Kaduna da gwamnati ke da alhakin yi musu aiki da kula da jin dadinsu. Saboda haka ba za a iya dorewa da kashe kashi 84 zuwa kashi 97 cikin 100 na kason da gwamnatin jihar Kaduna ke samu duk wata daga gwamnatin tarayya a albashi na ma’aikata da sauran abubuwa nasu ba. Kuma tun daga watan Oktoba na shekarar 2020 abin da ake ta yi ke nan. Ba an zabi wannan gwamnatin ba ne don sadaukar da yawancin kudaden da take samu ga biyan ma’aikatan gwamnati albashi ba, a yi watsi da raya jiha da al’umarta.

7. Saboda neman mafita saboda raguwar da kudaden da ake samu daga gwamnatin tarayya, ga makudan kudin da ake kashewa bangaren ma’aikata, a watan jiya na Afrilu, gwamnati ta sanar cewa za ta rage yawan ma’aikatanta, da rage yawan masu mukamai na siyasa. Ana nan ana kan yin aikin tantance takardun shaidar karatu na ma’aikata domin cikakkiyar aiwatar da wannan shawara da ta zama wajibi kuma ba mai dadi ba. Ba a tantance jimillar jami’an da abin zai shafa ba tukuna. Haka nan ba a dakatar da biyan albashi mafi karanci ba, duk da watsi da kiran ta dakatar da biyan albashi wanda ya saba wa dokar biyan albashi mafi karanci ta kasa.

Gwamnatin jihar Kaduna ta gwammace ta dauki matakan da ba su saba wa doka ba, da kuma sanin ya kamata, domin daidaita abin da take samu da yawan ma’aikatanta daidai ikonta don rage abin da take kashewa a albashi.

8. Sai dai tun daga lokacin da ta bayyana wannan niyya tata aka dora gangamin yi wa Gwamnatin jihar Kaduna karya da kage iri-iri. Da har ita kanta kungiyar kwadago ta ari karyar ta yafa, har take bayani a kan wata takarda ta bogi da aka ce daga gwamnatin jiha ce, da aka soma ganinta a shekarar 2019, da ke zargin za a mayar da ma’aikata da ke kan matakin albashi na 1 zuwa na 6 ma’aikata ba na dindindin ba wato kajuwal, da cewa ba a son ma’aikatan kowacce karamar hukuma su wuce su 50, da yin ritayar dole ga ma’aikatan da suka haura shekara 50 a duniya.

9. Wasu ‘yan gwagwarmaya na kungiyoyi sun ta yada wadanan karairayi da kage na kungiyar kwadago ta kasa NLC, da suka ci gaba da kaga karyar cewa korar ta shafi ma’aikata 4,000 ko 20,000 har ma 60,000. Wannan ba gaskiya ba ne haka nan ma bayanin da suke yi cewa Gwamnatin Jihar Kaduna, ta dakatar da biyan albashi mafi karanci. Gwamnatin jihar Kaduna ce ta ciri tuta wajen soma biyan ma’aikatan jiha, kuma ta ci gaba da biyan ma’aikatan har da na kananan hukumomi, da wasu ‘yan kungiyar kwadago ke ta shirme a kai. Watakila ana fakewa ne da guzuma don a harbi karsana a kan batun na ma’aikata. Mun riga mun sani tun daga abubuwan da suka faru a 2017 da wasu ‘yan kwadago suka nuna kirikiri kansu suka fi so fiye da jin dadin jama’a.

10. Wadannan ‘yan kungiyoyin kwadago sun ta amfani da labarun da aka kitsa don gangani na batanci. An sanar da Gwamnatin jihar Kaduna shirin da suke yi karkashin jagorancin Ayuba Wabba, su kuma sake ta da zaune tsaye, a jihar Kaduna, shigen wanda suka yi ranar 8 ga watan Nuwamba na shekarar 2017. A wannan rana suka tabka abin kunya suka auka harabar Majalisar Dokoki ta jihar Kaduna a kokarin da suka yi, wanda kuma ba su samu nasara ba, ta yunkurin tilasta wa gwamnati kada ta kori malaman makaranta su dubu 21 da dari 780 da suka fadi jarabawar da aka musu ta ‘yan firamare aji 4. Gwamnatin jihar Kaduna ta kori malaman, ba tare da bata lokaci ba, ta dauki sabbin malamai su dubu 25 domin maye gurbin wadanda aka kora, da daukaka ‘yancin da :ya’yan talaka ke da shi na samun ingantaccen ilimi.

11. Bayan wannan abin kunya da suka yi, akwai umarnin kama Wabba saboda lalata dukiyar gwamnati, da ta saba dokokon kasa, da sauran laifuffuka.

12. Kamar yadda ya dace a yi an sanar da hukumomin tsaro shirin da wasu ‘yan kungiyoyin kwadago suka yi na daukar nauyin zauna gari banza har daga wasu jihohi domin barna da ci gaba da yayata abubuwan da suka kitsa a kan aikin gwnati da matsalar tsaro.

13. Wasu kungiyoyin kwadago sun bai wa gwamnatin jihar Kaduna tabbacin ba za su shiga wannan zagon kasa ga rayuwa ta zamantakewa da tattalin arziki ba. Muna godiya da kuma yabawa da wannan tabbaci.

14. Gwamnatin jihar Kaduna na so ta yi karin hasken cewa, wannan shiri da aka yi na kai hari da tufe tashoshin samar da lantarki, da asibitoci, da ofisoshi na gwamnati da sauran wurare irin su ma’aikatar ruwa da fitilu na kan titi, ba za su girgizata ba ko kadan.

Muna sane da barazanar da aka yi wa kamfanoni masu zaman kansu, da ma’aikatansu da kayayyaki da yin watsi da hakkoki da bukatun abokan huldarsu.

15.Jarin da Gwamnatin jihar Kaduna ta zuba a makarantu, da asibitoci, da hanyoyi da sauran abubuwa na more rayuwa, shaida ce ta namijin kokarin da gwamnati ke yi bangaren mulki, da za a iya yarda da abin da take fadi a kan albashi. Gwamnatin jihar Kaduna na biyan ma’aikatanta albashi, tana kuma kashe kudi wajen raya jiha da duk mai hankali yana gani tare da yabawa. Sai dai idan kudaden shigarta sun ragu, za ta yi abin da duk wani mai hankali da tunani zai yi ta hanyar rage hidindimunta/hidimominta. Saboda haka gwamnatin jihar ke yin kira ga mazauna jihar su bijire wa masu son tashin hankali, su kuma yi abin da ya dace don kare kayayyakin gwamnati.

16. A ranar 20 ga watan Disamba na 2020, Gwamnatin Jihar Kaduna, ta bukaci ma’aikata da ke kasa da mataki na 14 du zauna a gida daga 21 ga watan Disamba 2020 a kokarin rigakafin kwaronabairos kuma tun lokacin ba a kira su, su koma wajen aiki ba. An kuma ci gaba da biyansu albashi. Har da wadanda ke matakin albashi na 14 zuwa sama, ma’aikatan da kwamishinoninsu, da shugabanin hukumominsu suka nuna aikinsu na da muhimmanci kuma ake bukatar su dinga zuwa aiki.

17. Dokar kwadago ta fayyace cewa doka ba ta amince ma’aikata da ke gudanar da muhimman ayyuka su tafi yajin aiki ba. Har ila yau doka ta hana a hana mutum walwala ko take masa hakkinsa na neman halaliyarsa saboda yajin aiki.

18. Shirin da aka yi na yajin aiki da tsayar da komai ya tsaya cik ba zai yi tasiri ko nasara ba, kamar yadda Ayuba Wabba bai yi nasara a 2017 ba. Gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da hukumomin tsaro da za dauki matakan dakile tashin hankalin da aka shirya. Bayan dokokin takaitawa na kwaronabairos an kuma hana jerin gwano a wannan jiha. An hana ne saboda yawan tashin hankali da kan auku sakamakon irin waman jerin gwano, ko da kuwa an fara ne da kyakkyawar manufa.

19. Gwamnatin jihar Kaduna a nata bangaren za ta kare dukiyarta da ‘yancin da ma’aikata ke da shi ma shiga wuraren aikinsu. Saba wa doka ne a yi kokarin hana ma’aikaci shiga ko fita daga ofishinsa. Ofisoshin gwamnati ba kayan wani dan kungiyar kwadago ba ne, saboda haka kada wani cikinsu ya yi kulle/rufe ko lalata wani kaya ko dukiya ta gwamnati.

20. Kamar shekarar 2017, Gwamnatin jihar Kaduna, saboda wani taro na yuyuyu ta fasa yin abin da ta sanya a gaba ba. Gwamnati ba ta so ta yi karyar cewa tana da kudin da za ta ci gaba da biyan mutum dubu dari ta yi watsi da kyautata jin dadin mutum miliyan 10.

Dokokin kungiyar kwadago na kasar nan, ba mabuya ce ta rashin sanin ya kamata ba, saboda haka ya kamata duk wanda abin ya shafa ya kula da kyau da sa shi a hanya.

Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top