Jerin kalolin Abinci 7 na zamani da yadda akeyinsu da yadace kuyi shagul-gulan Sallar bana dasu

Kalolin Abinci 7 na zamani da yadda akeyinsu da yadace kuyi shagul-gulan Sallar bana dasu

Yadda ake yin  chocolate-cake

Chocolate cake

 Abubuwan hadawa

Filawa kofi biyu

Rabin butter

Kwai takwas

Sugar Kofi daya

Cocoa powder kofi daya

Butter milk kofi daya

Baking powder karamar cokali daya

Nescafe daya (irin na sachet dinnan)

Chocolate brownie colouring babban cokali biyu in kina dashi

Vanilla flavour karamar cokali daya

Vinegar babban cokali daya in kina dashi

Yadda ake hadawa

Ki sa filawa, baking powder, cocoa powder a roba ki yi mixing na su sai ki ajiye a gefe.

Ki dauko wata roban din ki sa butter da sugar ki yi mixing na su in ya zama fluffy sai ki sa kwai ki juya su hade, sai ki dauko filawa mixture can ki na zubawa ki na mixing harya kare.

Ki zuba 1 strip nescafe a cikin butter milk ki juya sai ki zuba akan kwabin na ki, ki sa vanilla flavour, vinegar, dark chocolate brownie colouring ki juya su hade.

Sai ki dauko pan ki sa cupcake papers, ki zuzzuba. Ki yi preheating oven, in ya yi sai ki sa ki gasa.

Karin bayani

In bakida butter milk ki samu madarar gari 5 tbsp da vinegar ko white ko apple cider 1 tsp ki sa ruwa ki dama 1 cup sai ki yi amfani da shi

In kina so chocolate na ki ya yi moist kada ki cika masa wutan sama .

Bayan kin cire ki bari ya sha iska kadan sai ki samu kwano ki zuba in ba a lokacin za a ci ba.

 

Yadda Akeyin CIN-CIN

Abubuwan hadawa

Filawa mudu daya

Kwai 4

Suga

Baking powder

Gishiri

Man gyada

Kwakwa 1

Filebo (favour)

Butter

Yadda ake hadawa

Da farko za ki sami roba mai dan fadi sai ki tankade fulawarki ki fasa kwanki ki sa butter da gishiri kadan da baking powder da filebo.

Sai ki jika suganki da ruwa Idan ya narke sai ki kwaba fulawarki ya yi tauri ba canba yanda za ki iya murzashi a tire.

Sai ki dauko tirenki mai fadi ki shafa mai kadan, sai ki rika murzawa in ya yi fadi kamar kaurin tafin hannu ko kasa da haka, sai ki yanka kanana kamar yankan suga cube.

Idan kin gama sai ki dauko kaskonki ki dora a wuta ki sa manki idan ya yi zafi sai ki zuba ki soya har sai ya yi brown sannan ki kwashe. Haka za ki ta yi har yak are.

Ana iya ci da juice, ko shayi ko dai da duk wani drink da mutun ya ke so

WAINAR SHINKAFA 

Wainar shinkafa

1. Shinkafa tuwo Mudu/loka daya 

2. Shinkafar dafawa gwangwani biyu

3. Yeast tea spoon daya

4. Oil, albasa da kanwa.

PROCEDURE: Farko za a sheqe shinkafar tuwo, a dauraye sannan a jiqa yayi awa biyu zuwa uku, sannan a sake wankewa a kai niqa, sai a dafa shinkafar ci a zuba a kai. A yanka albasa isashe a ciki sai a kai injin niqa. Niqa mai kauri za a miki kada a sa ruwa ko kuma ki tabbata ba a lafta ba. Bayan an amso sai a jujjuya a zuba yeast a sanya shi a rana ko wurin dumi yanda zai tashi. Idan kuma gobe ne zaki yi kamar da safe ko da rana to zaki iya barin sa ya kwana qullun yanda zai tashi da kyau.

Washe gari sai a jujjuya, zaki iya niqa albasa ki zuba a kwano daban, ki sake samun kwano da zaki rinqa diban qullun, ki dandana in akwai tsami ki zuba ruwan kanwa, sai ki debi niqaqqen albasa kadan ki zuba, ki saka sugar kadan in kina so, ko ki jujjuya su sannan in tanda ya fara zafi a fara suya, kuma a kula sosai a tabbata wuta bayyi yawa ba, sannan idan manya kike yi to ki dan samu tsinken da zaki rinka sokawa a ciki don ki tabbatar cikin ya nuna kafin ki kwashe. Zaki iya yi a tandar qarfe a risho.

Note: Wasu basu zuba albasa lokacin niqa sai in za a soya kamar yanda na fadi, wasu kuma suna saka duka, a niqa da lokacin suya. Kuma wasu da baking powder suke kashe tsamin ba kanwa ba.Wannan shine simple way na yin waina.

SINASIR

Duka kwabin waina da sinasir ďaya ne, iyaka dai sinasir yafi sauqi, babu hayaki babu komai, shi zaki samu frying pan ne ki sa mai kamar table spoon sai ki zuba qullu daga nan ki rufe, ki sa wuta kadan kadan, a hankali zaki ga qullun yana tsotsewa har ya zama fari babu kullum a sama sai ki cire. Ba a juya sinasir haka ake yin sa.

Note: Yana da kyau ki samu non stick frying pan saboda gujema kamawa, sannan in sun sha iska zaki iya hada bibbiyu kina sakawa a cikin ledan santana.

WAINAR SEMOBITA

 

Wainar semobita

Abubuwan hadawa

Garin semobita

Yis (yeast)

Sukari

Gishiri

Albasa

Man gyada

Ruwan dumi

Yadda ake hadawa

Dafarko zaki zuba garin semobitanki acikin kwano mai fadi

Sai ki zuba yeast da sikari da gishiri daidai misali kamar dai yanda zaki zuba idan dai zaki yi wainar shinkafa

Sai ki kawo ruwan duminki ki zuba ki na mai juyawa da muciya a hankali har sai kwa6in ya yi daidai da kullin wainar (ruwan dumin yana taimakawa kullin wajen tashi da wuri amma idan akwai rana zaki iya kwabawa da ruwan sanyi). Sai ki yi ta juyawa har na tsawon minti 15.

Idan yayi zaki ga ya yi mulmul yana kamshi, sai ki rufe ki barshi a rana har sai ya tashi

Idan ya tashi sai ki yanka albasa a cikin kullin, sai kuma ki dora tanda ko kasko (frying pan)

Zaki ga tayi washar da ita kamar wainar shinkafa 

Ana cinta da miyar taushe ka romon naman kan rago ko kulikuli

WAINAR GERO

Wainar rogo

Kayan Hadi:

Gero (hatsi) gwangwani 4

Karkashi cokali 3

Kanwa

Suga Yadda kike so

Yadda Akeyi:

Zaki bayar a surfo miki geronki ki wankeshi ki gyara ma ana ki regeshi ko yana da tsakuwa sai ki bayar amarkado miki karkisa masa komai, idan an markado sai ki ajeshi waje me dumi, amma dake yanzu lokacin sanyine sai ki sa masa yeast idan gwangwani 4 ne sai kisa masa yeast karamin cokali daya,sai ki jika karkashin shima ki zuba, idan kuma ki gwanace wajan iya sarrafa karkashi to ba matsala zaki iya zubashi ba sai kin jikashi da ruwaba sai ki dinga juyawa zakiga yana dada yin kauri da danko sai ki aje zuwa lokacin da zaki soya, idan kinzo suya dama kin jika yar kanwarki saboda tsamin kullu sai ki dan sakata tare da suga yadda kikeso sai ki dinga diba kina soyawa shikenan za’a iyacinta da farfesun kan rago ko kuma miyar da ta dace.

 

YADDA AKEYIN ALKUBUS

1. Alkama gwangwani 5

2. Yeast tea spoon 1

3. Flour gwangwani 3

4. Mai, gishiri da ďan mai.

PROCEDURE: Farko zaki kai alkama a niqa miki sai ki tankade da rariyan laushi shima flour a tankade shi a ciki. Sai ki juye yeast a ciki ki zuba ruwa kiyi ta juyawa har sai ya hade sosai. Kwabin kamar na fanke amma yafi fanke tauri sosai. Domin idan ya kumburo kwabin zai saki, don haka da kauri zaki yi shi.

Sai ki rufe a barshi ya tashi sosai. Idan da daddare ne zaki dafa da safe kina tashi ki đan buga shi. In kuma da safe kika yi kwabin zaki yi da rana duk ďaya. Sai a shafa mai a gwangwani a rinka rinka zuba kwabin kamar dai alale. Sai a ci da miyan da ake so bayan ya dahu.

Note: Idan a tukunyar dambu zaki yi ki samu buhu ki saka shi ya zauna a ciki sai ki jera su, ya zama buhun ya hau har sama sai ki rufe duka gwangwanin ki ‘bame da murfin tukunya. Idan kina son yayi kamar cake wato babba guda ďaya duk zaki iya yi in yayi sai ki yanka. In baki da tukunyar dambu ki samu itatuwa ki jera su sai ki saka buhu kamar irin waccen ki jera alkubus ďin a sama ki rufe. Zaki ga ya taso sosai yayi manya. Sannan ba dole bane kiyi da buhu zaki iya yi yanda kike so. Alkaman in so 

Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top