SAMFARIN KALAMAN SOYAYYA

 Amincin Allah ya tabbata a gare ki ya ke wacce ta fi tauraro da duk wani haske. 

SAMFARIN KALAMAN SOYAYYA

Haske a idanuwa na, Ina fatan dai ba fushi kike da ni ba.

Zan iya manta komai amma ka sani ba zan iya mantaka ba haka kuma zan iya jure rashin komai amma ba zan iya jure rashinka ba, hakika daga jiya zuwa yau ina cikin kunci mara misaltuwa, bakin ciki y ziyarci zuciya ta wanda har kawo i-yanzu ba na jin zan iya kula wani cikin walwala. Idan har na ce zan iya na yi karya domin ni kadai na san irin halin da nake ciki na rashin jin dadin tafiyarka.

 

 

 

Zuciyata na tafasa har nakan ji tamkar na fashe da kuka ka sani cewa, wannan sakon duciyata na sanar da kai, hannu aikinsa rubutawa ba wai ina fada ne don tsari ko don ka ji dadi ba.

Daga lokacin da ka hada yanaka-yanaka ka yi gaba ni ma daga wannan lokacin na tattara duk wani walwala na da farin ciki na na ajjiye su a can gefe barin da ba za su taba kusanto ni ba.

Don haka ina sanar da kai ban yi fushi da abin da ka aikata ba kuma ban kiraka don ka bar abin da kake ba, illah na kira ka na ji laifin ba daga gare ni yake ba.

 

 

Ka kasance cikin farin ciki ka huta lafiya.

Na gode da kulawa, amma  ina ga ba ki kai ni shiga kewa da zullumi ba, dama an ce ba a sanin muhimmancin mutum sosai sai a lokacin da ya yi nisa da kai.Hakika jiya na kara gasgata wannan maganar.

Domin nisanta da na yi da ke na yini daya sai na ji kamar shekaru dubu ne, Kin riga kin zama fatar jikina duk wanda ya raba ni da ke kamar ya raba ni da kyauna kwarjini na hade da suturata.

Ke garkuwa ce a gare ni mai kare ni daga abubuwa da dama, Hasken zuciyata farin cikin raina, annashuwa da jin dadi na.

 

Ina sonki ina kaunar ki, ba zan iya nisa da ke ba.

 

Ba zan bar ki ba duk rintsi duk wuya, Sai dai in ke kika bar ni  zuciya kuwa ba ta fatan ko mafarkin hakan balle a gaske.

Ina so ki sani cewa soyayyarki ta yi nisa cikin zuciyata.

A hankali – a hankali ina ta ba ki filayen zuciyata ina so in rasa kaina a garin yin hakan ta yadda ba zan taba samuwa ba da sannu sannu dai ina ta mika rayuwata izuwa gareki ya masoyiyata kinzama abar kaunata wannan duk saboda karamcin kine a gare ni a yayin da nake kara kusantuwa dake duk tunane-tunane na suka fara bayyana ya masoyiyata kin zama abar kaunata kamar giza-gizai haka kika zamo inuwa a gare ni kamar ruwan sama haka kika jike ni da farin ciki kamar iska haka kika tafi da tunani na kin sabunta kaddarata ta hanyar samar da sabuwar safiya a rayuwata. Dake kawai nake son kare rayuwata ya masoyiyata kin zama abar kaunata

 

 

Kada ki taba mantawa da cewar wani na rayuwa ne kawai saboda ke ko ina zaki je ki tuna da hakan wani na rayuwa ne kawai saboda ke a duk inda kike ina miki fatan aminci addu’ar da zuciyata keyi kenan tamkar kyakkyawar abokiyar alaka haka rayuwa take idan kina tare dani a duk lokacin da kika yi nesa dani rayuwar sai ta zame mun ba dadi irin son da nake miki ta yaya zan iya bayyana shi wadannan idanuwan nawa tsahon dare suna tsayawa cur! kuma sunayin kuka duk da kasancewar ina tare dake me yasa nake jin kewarki? na kasa fahimtar miye hakan ki fada mun har na same ki duk da haka ina nesa da ke.

Yayin da kika iso bakin kofar zuciyata na sadaukar da rayuwata ga sunanki na koyi yadda zan rayu masoyiyata ada ban taba koyon yaya zan rayu ba ban taba koyon yadda zan rayu ba tare dake ba, masoyiyata wadannan yabo ne na gaskiya nake miki da zuciyata yayin da na same ki sai duniyata ta kawatu matuka duniyata ta cika burinta duk kanmu ba a ciki muke ba yanzu ne da muka hadu muka zama daya.

Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top