Tallafin Naira million 30 da dubu casa’in da wani abu aka samu a inda na gabatarda tafsirin Azumin watan ramalana na wannan ahekarar ta 2021.
![]() |
Sheikh Kabir HARUNA gombe |
Bayaga tallafin kayayyakin Abinci da sutura da aka samu ankuma tara wadannan makudan kudade domin tallafawa marayu inji shiekh Kabir HARUNA gombe.
Alhamadulilah Alhamadulilah
Alhamadulilah Daga fara Tafsir na nabana Zuwa yau da
na rufe an Tara gudunmawan Naira Miliyan Talatin da Dubu Chasa’in da Daya (N30,091,000).Wanda aka taimakawa Marayun ( dubu 70 ) Mugodewa Allah Alhamdulillah Wannan banda gudunmawan kayayyaki,da kayan abinci. Alhamdulillah Wannan majalisi 1 ne a cikin majalisosin Izala a fadin Najeriya, lallai Izala uwar alheri ce Izala Uban Marayun
Najeriya. Izala Sarkin Aiki Yar izala mugodewa Allah Alhamdulillah Alhamadulilah ya Allah kasaka wa duk wa’enda sukayi wannan ga garimin taimako, Allah ka saka musu da gidan Aljannah, Ameen summa.
Bayan hamdala da godiya ga Allah mallamin yace mutun dubu saba’in aka taimakawa karkashin wannan tallafin da kudi dakuma kayan abinci da sauransu.
Malan yace Izala uwar marayuce duba da yadda take taimakawa marayun kamar iyayensu na raye.
![]() |
Sheikh Kabir HARUNA gombe tafsirin Azumin watan ramalana na wannan shekarar 2021. |