Major General Farouk Yahaya: ya zama sabon babban hafsan sojin ƙasan Najeriya
![]() |
Major general YAHAYA FAROUK |
Buhari ya naɗa Manjo Janar Farouk Yahaya a matsayin sabon babban hafsan sojin ƙasan Najeriya.
Rundunar sojin ƙasar ce ta sanar da hakan a shafinta na Tuwita a yau Alhamis.
NaÉ—in na zuwa ne kwana shida bayan rasuwar Janar Ibrahim Attahiru mai jagorantar rundunar.
Janar Attahiru ya rasu ne a wani hatsarin jirgin sama da ya rutsa da shi a Kaduna, da kuma wasu mutum 11 cikin har da janar-janar uku.
Tun bayan rasuwar Manjo Attahiru Æ´an Najeriya suka fara tsokaci kan waÉ—anda ake hasashen za su maye gurbinsa.
Kafin naɗin nasa, Manjo Janar Faruk Yahaya shi ke jagorantar yaƙi da Boko Haram a arewa maso gabashin Najeriya.
Ya taɓa riƙe muƙamin kwamandan rundunar sojin kasa ta matakin farko.