*WASU DAGA CIKIN ABUBUWAN DA YA KAMATA MUTUM YA SANI GAME DA DECENTRALIZED EXCHANGE (KASUWA MARA SHINGE, KAMAR PANCAKE SWAP) DA SUARANSU
1 – Liquidity : Shine kudin da ake sa wa / warewa don tafiyar da kasuwa yadda ya kamata. Misali : Idan mutum ya sayar da coins Na kwatankwacin 20,000 kuma liquidity da aka yi adding 2,000,000 ne , to za’a cire/rage 20,000 daga ciki sai ya rage saura 1,980,000 kenan.
2 – Slippage : Shine banbancin dake tsakanin Farashin kasuwa da kuma Farashin da ake tsammanin zai iya kai wa. Alal misali : lokacin da ka zo swapping ma coins naka Farashin yana 1 Naira, Kafin ka karasa swapping Ya koma 2 Naira. Idan price yana fluctuating sosai shine ake saita slippage sosai sabida komai ya tafi yadda ake so.
3 – Charges fee : Kamar yadda nayi bayani a baya, kana bukatar gas fee Kafin ka yi amfani da Decentralized Exchanges.
Misali : Duk token din da yake kan Binance smart chain *BEP20* zaka ajiye BSC naka kwatankwacin Na 2k sabida covering Na gas fee.
Duk wani Token din da yake kan Ethereum *ERC20* zaka tanadi Ethereum kwatankwacin Na $5 zuwa sama don biyan gas fee.
Token din da ke kan Tron kuwa *TRC20* zaka tanadi Tron kamar 7 zuwa sama don biyan gas fee.