Yadda Akeyin meat pie

Meat pie

YADDA AKEYIN MEAT PIE

Abubuwan hadawa

Nikakken nama (minced meat) rabin kilo

Fulawa kilo daya

Albasa daya(mai dan girma)

Dankalin turawa guda uku (Manya)

Karas guda 3 (madaidaita)

Bota ko margarine 500g

Maggi 2

Gishiri daidai dandano

Man miya cokalin miya daya

Taim (thyme) rabin cokali

Baking powder cokali biyu (tea spoon)

Koyi guda daya

Yadda ake hadawa

Filling

Da farko ki bare dankalinki da Karas ki yayyankasu kamar kanana. Ki wanke ki ajiye a gefe

Sai ki dora manki a wuta, idan ya yi zafi sai ki yanka albasa ki zuba.

In albarsan ya soyu (ya dan fara golden brown) sai ki zuba nikakken namarki ki soya har sai ya soyu.

A wannan lokaci sai ki sa thyme na ki da Maggi da ruwa kamar kwatan kofi. A barsu su nuna kamar na minti 30.

Sai ki zuba yankakken dankalinki da yankakken karas naki a ciki a basu kamar minti 20. Sai a dan kwaba Fulawa kadan da ruwa a zuba a ciki don ya yi kauri. A nan sai a sauke a ajiye a gefe. Filling ya kammala.

Kwaba Fulawa (dough)

Ki samu robarki mai fadi ki tankade Filawarki, kisa baking powder, da gishiri ki hada su sosai.

Sai ki zuba bota, ki hada su sosai su hadu. Sai ki zuba ruwa kadan kadan kina hadawa har sai kin samu hadi mai taushi kamar na cincin (non sticky).

Abu na gaba shi ne gurzawa( rolling). A gurza shi fale-fale. Sai a rinka yanka shi kamar girmar murfin kofi (round ke nan).

Ki fasa Koyi ki kada.

Sai a dibi fillings dinnan kamar cokali daya da rabi a zuba a kan yankakken dough din nan, sai a dangwali Koyi kadan a shafa a bakin sai a rufe. 

A anan za ki iya anfani da cokali mai yatsa a daddatsa bakin don bakin ya rufu da kyau kuma ya bada kamanni mai kyau. Ki rika jera su a oven tirai (a shafe tiran da bota kafin a jera meat pies din). In kin kare jerawa ki shafe kan pies din da koyi

Sai ki sa a cikin oven mai zafi (preheat oven) a barshi har sai ya yi dan brown ko kuma misalin minti 25 za ki ji gida ya baje da kamshi. Shi ke nan meat pie ya kamala.

A na iya cin meat pie kamar snacks ko kuma ana iya amfani da shi a bukukuwa kamar suna da aure. Sannan za a iya duba: Yadda ake special cin-cin da fanke (puff-puff) da sauransu.

 

Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top