YADDA AKEYIN SHAWARMA

 SHAWARMA

Shawarma

Kayan Hadi:

Nikakken nama

Labanese bread

Cream salad

Koran tattasai

Cucumber

maggi,

Gishiri

Curry

Mai

Yadda Akeyi:

Ki soya naman da kika daka da maggi da curry ki soya sosai zuwa ruwan ya kame, ki sauke ki dauko wannan gurasar da kikayi idan kuma kina da ta kanti sai kiyi amfani da ita sai ki ajeta akan faranti ki ki debo naman ki zuba ki debo koran tattasai da cucumber da kika yanka kanana ki zuba akai ki kawo cream salad ki yaryada sai ki nade gurasar a tsaye ki sakata a oven ki gasata zuwa 10 mints ta gasu, ana ci da tea zaki iya yi da safe domin karin kumallo.

 

 

EGG ROLL SHAWARMA

Abubuwan hadawa

Kwai

Shawarma bread

Naman shanu Ko kaza (dafaffafe, ki yanka kanana)

Tarugu

Albasa

Maggi

Kabeji (ki yanka ki wanke da gishiri)

Tumatur

Tomato ketchup

Koren tattasai

Cucumber

Karas (carrot)

Yadda ake hadawa

Ki gyara, ki wanke sai ki yanka su carrot na ki, kabeji, albasa ajiye a gefe.

Ki sa non stick pan na ki akan wuta ki sa butter kadan (cokali daya), sai ki sa yanka albasa ki dan soya sama sama, ki sa tarugu ki juya , sai ki sa ruwa kamar (cokali biyu).

Sai ki kawo namanki tare da kayan kamshi, maggi (iya dandano da zai mi ki) sai ki juya ki rufe nadan wani lokaci sai ki kawo kabejin, cucumber da ki ka yanka ki sa a ciki ki juya ki rufe nadan wani lokaci har sai ruwan ya shanye ki sauke ki ajiye a gefe.

Ki dauko wani kwano daban ki fasa kwanki a ciki sai ki sa gishiri kadan, ki yanka albasa ki yanka tarugu ki sa a ciki sai ki buga ajiye a gefe.

Ki sake daura non stick pan ki sa man gyada kadan sai ki dauko hadin kwanki (wanda ki ka yanka albasa da tarugu a ciki) ki zuba dan dai dai a cikin non stick pan na ki (wanda ki ka sa man gyada) sai ki dauko shawarma bread naki ki daura akan kwan dake kan wutan.

Sai ki dauko cokali ko kuma ki sa hannunki ki na danna shi a hankali har sai Kwan da shawarma bread din sun hade da juna. Haka za ki yi har sai kin gama da sauran.

Sai ki dauko ki daura a kan plate ko tire ki dauko hadin kabejinki ki sa akan shawarma bread din (wanda ki ka manne shi da kwai) sai ki dauko su koren tattasai albasa da carrot na ki ki sa a gefe (idan ki na so za ki iya sa tomato ketchup, salad cream naki a wannan mataki).

Sai ki masa nadin tabarma (za ki iya sa foil paper bayan kin gama nadawa don kar ya ware). A ci dadi lafiya.

Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top