Babbar mahana: Gwamna Ya Sha Alwashin Rushe Gidaje a Jiharsa Saboda Masu Garkuwa da Mutane

 Gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun, ya sha alwashin zai rushe duk wani gida da aka gano masu garkuwa suna buya a cikinsa, kamar yadda daily trust ta ruwaito.

Gwamnan yace ba zai yuwu mutanen da suka hana jama’a zaman lafiya kuma ace suna samun wurin ɓoyewa ba.

Gwamna Abiodun ya roƙi al’ummar jihar musamman masu gidajen haya, su tabbatar sun san waɗanda suke baiwa gidajen su.

Gwamnan yayi wannan gargaɗi ne yayin da yake jawabi a wurin wani taron kiristoci karo na 11 a Yewa, jihar Ogun.

Wannan ba shine karon farko da gwamnan Ogun yayi wannan gargaɗi ba na rushe duk wani gida da masu garkuwa ke amfani da shi.

A shekarun baya gwamnan yayi wannan gargaɗi, inda har yayi barazanar kama mamallakin gidan, wanda ya baiwa baragurbi maɓoya a gidansa.

Source: Isyaku.com

Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top