Bakin kadangare complete hausa Novels

 

AIHAUSANOVELS is website consists of hausa novels note, the reason of launching this site is to Entetaint, Motivate and Educate our readers.
We provided hausa novels of many type, Such Adventure, love, romance, fiction, non-fiction, mystry, fantasy, action e.t.c from hausa Authors
We provided a new and old novels both softcopy and hardcopy from our Author with thier permission.
 AIHAUSANOVELS shafin yanar gizo ne wanda yake ɗauke da littattafan hausa, dalilin bude wannan shafin shine domin Kayatar masu karatu da kuma ilimantar da su.
 Mun samar da littattafan hausa na nau’uka daban-daban, kama daga littafin, soyayya, tatsuniya, almara, Hikayoyi, gyara kayanki (yadda mata zasu kula da kansu a gidan mijinsu) da dai sauransu, daga Marubutan hausa.
ZAMANI writer’s association
Short Novel
Shafin farko 1.
Wata mata c wadda a shekaru,ba zata wuce shekara 40 Da dori ba naga ta fito daga daki, wasu bakaken maguna Su uku suna biye da ita.
Wata tsohowar Langa taje ta Bude idanuna suka yi arba da wasu narka-narkan kadan garu guda biyu a ciki,da alamun mutattu ne har ma da jini a jikinsu,zai ankarar da sun ci mugun kafin su mutu din.
 Ba tsoro balle fargaba Ta tura hannu ta shako Jelar daya ta daga sama yana Reto, magunan nan sai tsalle suke iya karfin su da niyar Chafko wa,Ita kuwa daga taga daya zai kamo sai ta kara daga kadan garen sama. Alamun dai wasa take da Magunan wajen basu kadan garen hannun nata,
Dai-dai lokacin Wata yar budurwa wacce bata kaita shekaru ba ta fito daga daki da kwanuka a hannunta ta kai gurin wanke-wanke juyowar da zata yi ta ga abinda take faruwa said ta kwalla ihu”Ahhhhhhhh! ” Da matukar karfi.
Ita kuwa matar lokacin data fahimci tsorata ta yi sai tayi dariya, Ba zato ba tsammani sai kawai ta cillo mata Kadangaren, Wani ihun! ta sake yi a karo na biyu, Garin gocewa Ta fadi a nan ai kuwa kadan garen ya fado kanta.
Burin karfi da yaji ta farayi tana ihu tana kakabe-kakabe, Ita kuwa datijiwar matar ba abun da take in ba dariyar mugunta ba, Ta kusan mintuna biyar tana dariya inda ita kuma waccan sai zazage-zazage take, Domin ita a zatanta har yanzu kadan garen na jikinta,
Maimuna Cikin dariya tace “Haba Dije kamar dai ba jarumar mace ba? kinga fa ga kadan garen can Har maguna sun kusa cinye shi” Ta bi hannun nata da kallo, magunan sai faman Cin kadan garen suke Suna fada a tsakanin su, Lokacin taga Uwar magunan ta saka kan kadan garen a baki ta tauna, Sai ji kake Kaaaats-kaats! Tana taunawa, Da sauri dije ta Kauce kanta,
“Haba Aunty Maimuna Ko so kike ki kashe ni ne? Kinsan fa ina tsoran kadan gare amma kike Shuna min,?”
 Wata dariyar mugunta maimuna ta sake yi tace “Ke yanzu ki rasa abun da zaki dinga jin tsoro sai kadangare? Ni ai ba abunda na raina kamar kadan gare wallahi, Yanzu ma na Tura su Kabiru Daji su kamo wasu domin sun kare saura daya ya rage maguna na basuda abincin Rana”
 Dije ta girgiza kai tace”Aunty ke fa babba ce kuma kinsan alhaki kadangarun nan fa suma Rai ne da su. Kiji tsoran allah ki daina sa yaranki suna kashe su Hakan babu kyau, Koma ba komai Ki sani A kadan garu akwai *ALJANIN KADANGARE* bakya Tsoran Wataran su fada mishi?”
Maimunta tace, “Ke Rabani da wannan Zancen wai wani Akwai aljanu a kadan garu inji wa?. Ai da akwai to da tuni Yarana sun hadu da shi Domin tun bayada Shekara biyu kafin a auro ki nake Turasu su kamowa mage ta kadangaru.”
Deeje ta “Hmm to allah ya kiyaye amma ni gaskiya kar a kara Wullo min kadan gare bana so” Ta shige dakinta.
 
Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top