Dalilin da yasa Farashin Shinkafa ya karu a daga 19,000 zuwa 23,000-’Yan kasuwa

 Dalilin da yasa Farashin Shinkafa ya karu a daga 19,000 zuwa 23,000-’Yan kasuwa

‘Yan kasuwar Shinkafa dake casheta, RIFAN sun bayyana cewa dalilin da yasa farashin shinkafar ya karu daga 19,000 zuwa 23,000 shine shinkafar da suke sayowa me buntu, watau Sanfarera ta kara farashi.

Daya daga cikin membobin RIPAN, Alhaji Abba Dantata ne ya bayyana haka a ganawar da hukumar yaki da rashawa ta jihar Kano, PCACC ta shirya.

Yace buhun shinkafar ba zai saidu a kasa da Dubu 23 ba saboda kudin kayan sarrafata sun karu sosai.

Ya kara da cewa, Hauhawar Farashin dala da, Injin Casa, da tashin Dala duk sun taimaka wajan karawa shin kafar tsada.

Ya kuke ganin wannan bayanin na yan kasuwa? 

Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top