EFCC ta gurfanar da manyan ma’aikatan Sokoto 5 kan miliyan 500 da aka karkatar

 EFCC ta gurfanar da manyan ma’aikatan Sokoto 5 kan miliyan 500 da aka karkatar

EFCC Nigeria

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasa EFCC ta gabatar da wasu ma’aikatan gwamnatin jiha dake hukumar kula da fanshon ma’aikatan Furamari kan zargin almundahana ta naira N553.985,644.1.

Kuɗin an ware su ne domin a biya malaman da suka ajiye aiki waton ritaya haƙoƙonsu na garatitu da Fansho.

Ma’aikatan sun haɗa da Abubakar Aliyu, Hassana Moyi, Haliru Ahmad, Kabiru Ahmad da Dahiru Muhammad Isa waton sakatare, da daraktan kuɗi da mataimakinsa da Ma’aji da Kashiya na hukumar.

Ma’aikatan an gurfanar da su gaban babbar kotun Sokoto kan tuhuma 28 da suka hada da zamba cikin aminci dayin hulɗar jabu da suka saɓawa sashe 92 (2), 311 kundin dokar Arewa da sashe na 351, 353, 348 a daftarin dokar Sokoto shari’a 2019.

Shugaban yankin Sakkwato na hukumar EFCC Usman Bawa Kaltungo ya ce ma’aikatan sun yi amfani da bococin ƙarya sun fitar da kudin da aka ajiye domin biyan fansho da garatitu suka raba abinsu.

Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top