Ghali Na’Abba Ya Bayyana Yadda Gwamnoni Suka Jefa Najeriya Cikin Matsaloli

 Tsohon kakakin majalisar wakilai, Alhaji Ghali Umar Na’Abba, ya caccaki gwamnoni a Najeriya yana mai cewa sun lalata dimokiradiyyar kasar, Daily Trust ta ruwaito.

Na’Abba, yayin da yake magana a wata hira da Sashen Hausa na BBC a ranar Talata, ya ce gwamnonin jihohi sun lalata dimokiradiyya, suna yin magudi a zabukan fidda gwani na jam’iyyunsu na siyasa don wanda suke so ya fito.

“Gwamnoni sun ja layi a siyasa wanda in kai ba yaronsu bane, ba za ka zama kowa ba ko kuma a zabe ka a dukkan matakai. Wannan yana faruwa a duka PDP da APC.

“Dimokiradiyya ya kamata ko yaushe ta ba da damar mu’amala tsakanin mutane kuma a ba su damar zaben mutumin da suke so. Amma gwamnoni tun tuni sun canza wannan tsarin, babu dimokiradiyya a Najeriya yanzu,” inji shi.

Ya kara da cewa gwamnonin sun kuma toshe damar da matasa za su iya shiga siyasa “wanda hakan babbar barazana ce ga makomar kasar.”

Da yake amsa tambaya game da kasancewarsa a jam’iyyar siyasa, Na’Abba ya ce shi ba ya cikin wata jam’iyyar siyasa.

“Na kwashe shekaru da yawa a PDP sannan daga baya na koma APC, amma sai na bar su duka saboda ba dimokradiyya suke yi ba. Babu zabe cikin gaskiya a dukkanin tsarin kuma ba zan iya shiga jam’iyyar da babu adalci da gaskiya ba,” inji shi.

Na’Abba ya nuna takaicinsa game da gazawar wannan gwamnati mai ci a yanzu, inda ya ce, “Mun yi wa gwamnati nasiha a daidai ko a kungiyance amma ba su saurara ba.”

A wani labarin, Gabanin zaben gwamna a 2023 a jihar Kano, gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya ce wakila da jam’iyya ne za su tsayar da wanda zai fito a matsayin wanda zai gaje shi.

Daily Trust ta ruwaito cewa gwamnan na Kano ya bayyana hakan ne a yayin tattaunawa da ‘yan jarida a ranar Litinin, 14 ga watan Yuni.

Legit.ng ta tattaro cewa Gwamna Ganduje ya yi wannan bayanin ne bayan tsoffin ‘yan takarar gwamna uku a zabukan da suka gabata a karkashin jam’iyyun siyasa daban-daban sun sauya sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulki.

Source: Isyaku.com

Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top