Har yanzu babu dan Siyasar da ya kai ni farinjini a Afrika—Buhari
![]() |
Shugaba buhari |
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya yi ikirarin cewa, har yanzu babu dan siyasar da ya kai shi dubun dubatar tarin masoya a fadin nahiyar Afrika inda ya ce, “Ina matukar godiya ga dubun dubatar tarin masoya na na ciki da wajen Najeriya sakamakon irin so da kaunar da suke nuna min”.
Wannan ya nuna cewa har yanzu babu dan siyasar da ya kai ni tarin magoya baya a nahiyar Afrika saboda haka ina matukar godiya ga irin so da kaunar da magoya baya na suke nuna min” in ji shi kamar yadda ya bayyana a wani jawabi da ya gudanar a jihar Borno.
Shugaban dai yana wata ziyarar aiki a birnin Maidugurin jihar Borno, inda zai kaddamar da wasu ayyukan raya kasa da gwamnatin jihar ta yi.
Menene ra’ayoyinku?