INEC: Hukumar zaɓe mai zaman kanta a Najeriya ta fidda tsarin sabunta rijistar zabe ta internet

 INEC: Hukumar zaɓe mai zaman kanta a Najeriya ta fidda tsarin sabunta rijistar zabe ta internet

Muhammad Yakubu

Hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya INEC ta bayyana cewa ta shafe tsawon shekara guda tana gudanar da aikin sabunta rijistar masu kada kuri’a, domin tunkarar zaben shekarar 2023, wanda matakin farko zai kasance ta hanyar amfani da shafin intanet ne.

Daraktan hulda da jama’a na hukumar, Mista Nick Dazan ya shaida wa BBC Hausa cewa za a fara sabunta rijistar ne a ranar Litinin 28 ga watan Yunin wannan shekarar.

Ya kuma ce za a yi wa wadanda ba su taba yin rijista ba, da wadanda suka kai shekara 18, ko kuma wadanda suke so su kaura da rijistarsu daga wani gari zuwa wani, da kuma wadanda ba su kai shekara 18 a wancan lokacin ba, da ya sa ba a samu an yi musu rijistar ba.

“Tsarin shi ne na daya, za a yi shi kamar yadda aka yi a baya, yadda duk wanda shekaraunsa suka kai 18, ko kuma suka kai 18 amma a baya bai yi ba rijistar ba kuma dan Najeriya ne, to zai bayyana a cibiyar da za a yi wannan rijista domin a yi masa,” in ji Mista Nick.

Mista Nick Dazan ya kuma yi wa BBC karin bayani cewa ana iya shiga shafin intanet na hukumar zaben domin a yi wannan rijista amma ta wucin gadi, inda daga baya za a je cibiyoyin da aka tanada don yin rijista domin su kammala.

“Na wucin gadi ta yanar gizo shi ne za ka shiga wata manhaja ta musamman, inda za ka bayar da bayananka kamar suna, da unguwarka, da shekarunka, da makamantansu,” in ji shi.

Ya kuma kara da cewa: “Amma daga bisani idan ka gama za ka garzaya zuwa ciboyinmu na rijista a dauki hoton zanen yatsunka, da kuma fuska. Idan aka kammala wannan za a ba ka kati na wucin gadi kamar yadda muke yi a baya, daga baya idan an tantance sai a ba ka kati na dun-dun-dun wanda za ka yi amfani da shi wajen kada kuri’a.”

Ya mazauna karkara za su yi?

Ganin cewa a kauyuka da dama babu wutar lantarki ballantana intanet ko kuma masu amfani da shi, hukumar ta INEC ta ce hakan ba zai hana mazauna karkarar sabunta rijistar ba.

Mista Dazan ya bayyana cewa sun yi la’akari da wannan, sun kuma san cewa yanzu babu intanet a akasarin yankunan karkara, amma da yake akwai intanet a cikin birane, haka zai sa a samu saukin cunkoson masu yin rijistar.

A cewarsa: “Ai makasudin amfani da intanet din ma shi ne don a rage cunkoso wajen yin rijistar a cibiyoyi kamar yadda aka samu a baya, to ina ga idan aka yi amfani da intanet din za a kawar da wannan matsala.”

“To muna ganin idan aka yi amfani da yanar gizo, mutane da dama za su samu su yi rijista, kuma kawo yanzu a bisa binciken da muka yi mutane masu amfani da intanet a Najeriya daga shekarar 2020 ya kai miliyan casa’in da tara, kuma ana hasashen nan da zuwa 2023 za a samu karuwar masu amfani da intanet din miliyan biyu da talatin da daya,” in ji Mista Nick.

Ya kuma ce wani abu mai muhimmanci a nan shi ne matasa su suka fi amfani da intanet wadanda kuma su ne a baya suka fi yin kira ga hukumar zaben a kan ta ci gaba da yin wannan rijista kana ta yi amfani da intanet din.

“Shi ya sa aka kirkiro wannan tsari na yin rijista ta hanyar amfani da intanet don saukaka wa wadanda ba su da halin amfani da wannan hanya su samu su yi ba tare da fuskantar matsalar cunkoso a cibiyoyin rijistar ba,” a cewar Nick Dazan.

Hukumar ta INEC ta ce ya zuwa yanzu ta yi wa ‘yan Najeriya kimanin miliyan tamanin da hudu rijistar zaben, kuma tana da burin yi wa al’umar kasar fiye da miliyan dari rijista kafin zuwa zaben shekarar 2023.

Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top