LABARI DA DUMI-DUMIN SA: An Kama Jirgi Makare da Buhuhuwan Kudaden Kasar Waje a Filin Sauka da tashin Jiragye na Jahar Kano.

 LABARI DA DUMI-DUMIN SA !

“An Kama Wani Jirgi Makare Buhuhuwan Kudaden Kasar Waje a Filin Jirgin Jahar Kano”

Jami’an tsaro sun yi Nasarar cafke wani katon jirgi makil da buhuhuwan kudaden kasar waje a filin jirgin jihar kano dake Arewacin Najeriya.

Rahotanni sun bayyana cewar, tun da misalin karfe 2 na ranar yau har zuwa 6 na marece jami’an hukumar EFCC ke lissafin kudaden kuma ba’a kai karshe Ba.

Jami’an tsaron sun yi ram da Buhuhuwan kudaden kasar wajen ne lokacin da jirgin ya sauke kudade yai tafiyar sa.

Kawo Yanzu ba’a fitar da ko adadin nawa ne kudaden ba, sai zuwa gobe idan hukumar ta EFCC ta kammala lissafin kudaden.

Mi Zaku Ce?

Source: Jaridar Sokoto

Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top