Kwararru a fannin tattalin arziƙi a Najeriya sun nuna damuwa fara kan sabon rahoton Bankin Duniya da ya yi gargaɗi cewa mutum miliyan bakwai sun sake faɗawa talauci a bara kawai saboda ƙaruwar hauhawar farashi a ƙasar.
![]() |
Getty images |
Bankin ya ce a cikin watan Afrilun da ya wuce an samu hauhawar farashi mafi yawan da ba a taɓa gani ba a cikin shekara huɗu.
Rahoton na Bankin Duniyar ya yi nuni da abin da ya kira da fitattun garanbawul na gwamnati, da nufin shawon kan tasirin anobar cutar korona da kuma tallafawa wajen farfado da tattalin arziki, cikin su har da matakan rage tallafin man fetur, da daidata farashin wutar lantarki.
Dukkansu kuma in ji rahoton don bunkasa kafofin samun kudin shiga da nufin aiwatar da ayyukan da za su inganta rayuwar talaka ne.
Sai dai a tattaunawar su da BBC, wani masanin tattalin arziki a Najeriya Dakta Mohammed Shamsuddeen na Jami’ar Bayero ta Kano a arewacin kasar ya ce lamarin ba haka yake ba.
”Domin kuwa tuntuni dama hukumar kididdiga ta kasa NBS ta fitar da bayanai cewa hauhawar farashi har ya haura kaso 18 bisa 100 a Najeriya,” in ji Dakta Shamsuddeen.
Ya kuma kara cewa: ”Kuma ma dama ga mai bibiyar al’amura ya san cewa dole za a kai wannan matsayi saboda dokokin tattalin arziki da Najeriya ta riÆ™a yi daga baya-bayan nan da kowa ya san cewa ba za su amfana wa talaka ba.”
A nan in ji masanin tattalin arzikin yana nufin canza taswira ko fuskar tattalin arziki daga inda gwamnati ke da ƙarfin fada a ji da yawa a harkar tattalin arziki ya zuwa zare hannun gwamnati daga kusan komai na tattalin arziki.
BBC Hausa ta binciki yanayin farashin kayayyakin abinci da aka fi amfani da su a ƙasar, amma ta duba farashin jihar Kano ne duba da cewa ita ce cibiyar kasuwanci ta arewacin Najeriya.
Ga farashin wasu daga cikin kayayyakin abinci a arewacin Najeriya:
Shinkafa ‘yar gida 23,000 kilo 50
Gero buhu 22,700
Masara buhu 22,500
Dawa buhu 22,700
Shinkafa ‘yar waje 28,000 kilo 50
Semo buhu 4,000
Man gyada lita 25 22,000
Indomie 3,500
Spaghetti katan 4,300
Ga kuma farashin wasu kayayyakin abinci a shekarar 2017 da shi ma BBC Hausan ce ta yi bincike tare da yin labarin yadda Hauhawar farashi ta sa Æ´an Najeriya suka É—anÉ—ana kuÉ—arsu a wancan lokacin.
Farashin wasu abubuwa a watan Janairun 2016 zuwa Janairun 2017
Buhun shinkafa babba N8000 – N19,500
Buhun Semovita N1,300 – N3000
Buhun fulawa N6,000 – N12,000
Kwanon dawa – N140 – N600
Kwanon wake N400 – N800
Kwanon sikari N400 – N900
Indomie N35 – N70
Tulun gas matsakaici (kilo 12.5) N2,500 – N5,300
Litar kananzir N100 – N500
Ga wani rahoto na jihohin da suka fi tsadar kayan abinci da BBC Hausa ta yi duba a kai a watan Maris É—in 2021.
Source: BBC Hausa