Najeriya Ta Fara Katin SIM, Wayar Salula
![]() |
Najeriya Ta Fara Katin SIM, Wayar Salula |
Mutane da yawa ba su sani ba, yanzu Nijeriya na kera wayoyin komai da ruwanka.
Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Kasa, Isa Pantami ne ya bayyana hakan a jiya.
Baya ga kera wayoyi, ya kuma bayyana cewa a yanzu kasar na da karfin kera katinan SIM, ba ga Najeriya kadai ba har ma da Afirka baki daya.
Pantami, wanda ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai a sakatariyar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta kasa ya kara jaddada cewa Najeriya na da karfin samar da a kalla katinan SIM miliyan 200 duk shekara.
Ya kuma bayyana cewa gwamnati ta kammala shirye-shirye don tabbatar da cewa kashi 60-70 na abubuwan da ake bukata a bangaren sadarwa za a samar da su a cikin gida.
“Mun fito da wata manufa wacce muke so Najeriya ta yi a cikin shekaru biyu zuwa uku masu zuwa, cewa mafi karancin kashi 60 zuwa 70 na abin da muke bukata a bangaren sadarwa, wanda za a samar da shi a cikin gida. Mun fara shi.
“Lokacin da wannan gwamnatin ta hau jirgi, hatta katinan SIM an shigo da su Najeriya amma kamar yadda yake a yau, gwamnatin tarayya ta samar da yanayi mai kyau ga kamfanoni masu zaman kansu kuma kamar yadda yake a yau, muna da karfin samar da katinan SIM ba kawai don amfani da mu amma ga nahiyar Afirka baki daya.
“Muna da karfin da za mu iya samar da akalla SIMS miliyan 200 a duk shekara. Mun samar da yanayi mai kyau ga kamfanoni masu zaman kansu don fara samar da wayoyin zamani. A yau a Najeriya, muna samar da wayoyin zamani, ”inji shi.