RIKICIN CIKIN GIDA A JAM’IYYAR APC TA JIHAR SAKKWATO NA ƘARA ƊAUKAR ZAFI

 RIKICIN CIKIN GIDA A JAM’IYYAR APC TA JIHAR SAKKWATO NA ƘARA ƊAUKAR ZAFI

APC Sokoto

Zamu Cigaba da Tafiyar Siyasa a APC Don Kokarin Kifar Da Siyasar Uban Gida a Jahar Sokoto~ inji Salame, da Manya Achida Sun Jaddada Aniyar Su Ta Kin Bin Siyasar Sanata Wamakko a 2023.

Shuwagabannin ɓangare guda na jam’iyyar adawa ta APC a jihar Sakkwato sun jaddada aniyar su ta ci gaba da zama tsintsiya maɗauri ɗaya wajen wuntsilar da siyasar uban gida a jam’iyyar su ta APC.

Kakakin majalisar dokokin jihar Sakkwato Hon.Aminu Muhammad Manya Achida tare da ɗan majalisar wakilai na Gwadabawa/illela Hon. Balarabe Salame sun raba ƙafa tun tuni da tsohon gwamna Sanata Wamakko a jam’iyyar APC, bisa zargin da suke yiwa Wamakko na juya su tare da rashin basu haƙƙoƙan su a siyasance, wanda tun a farkon shekarar nan sun faɗi cewar basa tare da Wamakko a siyasar 2023.

Salame da Manya Achida a yau Alhamis 17 ga watan Yuni 2021, sun sake jaddada aniyar su ta ƙoƙarin kifar da siyasar Wamakko a 2023, a wani taro daya gudana na masu ruwa da tsaki na ɓangaren nasu a cikin Otel ɗin Giginya Corel dake nan Sakkwato da zummar cigaba da nuna ɓangaren su a APC reshen Sakkwato.

Salame da Manya Achida sun tsawatar da magoya bayan su akan kada su kuskura su lamunce ga duk ɗan wani ɓangaren Wamakko wanda yazo da zummar karɓar katin su na zamaan jam’iyya, sun ce yaudara ce kawai.

Hon.Abdullahi Balarabe Salame dai yna ɗaya daga cikin ƴan takarar kujerar Gwamnan Sakkwato a zaɓen 2023, ƙarƙashin Jam’iyyar APC mai adawa a jihar, ya fito ne don haramtawa ƴan siyasar Sakkwato gudanar da siyasar uban gida~ inji shi.

Source: Abdulkarim mai kulki facebook

Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top