Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya nemi kamfanin sadarwar MTN ya ragewa ‘yan Najeriya kudin sayen Data.
Shugaban ya bayyana hakane a ganawarsa da shugaban Kamfanin, Ralph Mufita a ziyarar da suka kai masa fadarsa a yau, Juma’a Bisa jagorancin Ministan Sadarwa da tattalin arzikin Zamani, Sheikh Isa Ali Pantami.
Shugaba Buhari ya bayyana cewa, a matsayin Najeriya na babbar kasuwar MTN yana so a rika baiwa ‘yan Najeriya sabis me kyau a farashi me sauki.
Yace musamman bangaren sayen Data, yana son a ragewa ‘yan Najeriya inda yace kuma yana son Kamfanin na MTN su baiwa gwamnatin tarayya goyon bayan samar da abubuwan Amfani na kasa.
Ya kuma sha Alwashin samar da yanayin kasuwanci me kyau a Najeriya.
Shugaba Buhari ya nemi MTN ta ragewa ‘yan Najeriya kudin Data
Agajahub publishers