TAKA HOTON KWANKWASO: “YAN NIGERIA NACI GABA DA YIWA GANDUJE TOFIN ALA TSINE

Gwamnan Kano Alhaji Abdullahi ganduje ya jagoranci taron karbar mambobin PDP dasuka koma APC.

Gwamnan Kano Alhaji Abdullahi ganduje

Yayin gabatarda taron an hango gwamnan Kano ya taka hoton kwankwaso inda mutane dadama suka tofa albarkacin bakinsu,

Al’umma daban-daban a shafukan sadarwa na zamani na cigaba da Allah wadai da matakin gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya ɗauka na taka hoton tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.

Tun da farko a yammacin jiya ne bayan da aka kammala taron ranar demokraɗiyya tare da karɓar wasu ƴan siyasa da su ka sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC Gandujiyya, wani hoton da gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya taka hoton Sanata Rabi’u Kwankwaso ya fara yawo a shafukan intanet.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ke nan a lokacin da ya ke taka hoton tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso

Bayyanar wannan hoto ya sanya al’umma fara bayyana ra’ayinsu akan wannan sabon salon adawa da jam’iyyar APC Gandujiyya ta ɗauka akan jagoran na Kwankwasiyya.

Jaridar Labarai24 ta tattaro wasu daga cikin ra’ayoyin mutane akan wannan batu. Ga su kamar haka:

“Ka kyauta kwarai da gaske. Gwamna bai samu mashawarta nagari ba anan bangaren” In ji Muhammad Bashir Amin

Ita kuwa Huraira Adamu cewa ta yi “Haba a shekarun shi ya na aikita wannan??? Allah ganar da shi”

“Ba abin mamaki bane shi butulci ba abinda baya sawa, amma dai karshe baya kyau, a kwai lokaci, kuma har gobe Kwankwaso yana gaban ku ya muku nisa. Allah ya kara dorashi akan makiya Amin” In ji Abubakar Dan Msulmi.

A ra’ayin Salisu Rabi’u Limanchi cewa ya yi “Wallahi ka yi adalci sam wannan ba daidai bane kuma ba girmansa bane, mugwayen fadawa wadanda lokacin rabuwa na daf da zuwa su suke zugashi. Haka ma sanda ya zagi ƴan kwankwasiyya abin haushi jikokinsa koma tattaba kunne suka ringa zaginsa. Don ALLAH masoya gwamna na gaskiya ku ringa tunatar dashi daraja da girman dayake dashi a idon al’umma”

“Gaskiya maigirma gwamna masu baka shawara basuda amfani atare dakai saboda giyar mulki bazata bari ka ganesu yanzuba amma inada yakinin wlh zakayi nadamar haduwa dasu nan gaba.kuma babu wani shugaba akasar nan da zaiyi tuna nin hada mu amala dakai yayi tunani in akasi yasamu tsakaninka dashi baza kayi masa abinda yafi wannan ba” In ji Ishaq Abdullahi

Shi ma Muhammad Muzammil Mandawari cewa ya yi “Masu bawa gwamna Ganduje shawara a siyasan ce sun barshi yayi kuskure”

Shi kuwa Malam Isma’il Lamido cewa ya yi “Magana ta gaskiya duk Wanda Suka shirya wa Gwamna Wannan basu yi daidai ba Wannan ba Siyasa bace an sauka da kan layi”

“Ya kamata ayi hamayya cikin mutunci, yadda kwankwaso da Malam Suka sauka wani ya hau Haka shima gwamna Ganduje zai sauka wani ya hau kuma baka san waye zai zama anan gaba ba. Na tabbata ba za kaso ayi maka irin haka ba. Gyara kayan ka”

Idan za a iya tunawa dai tsohon gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso da tsohon mataimakinsa kuma gwamna mai ci, Abdullahi Umar Ganduje sun kwashe shekaru hudu suna jan ragamar jihar Kano wato daga shekarar 1999 zuwa 2003, kafin gwamna Ibrahim Shekarau ya kayar da su.

Haka kuma bayan faduwarsu a neman tazarce, mutanen biyu sun kwashe shekaru kimanin 8 suna aiki tare a tsohuwar gwamnatin tsohon shugaba Olusegun Obasanjo, kafin 2011 lokacin da suka sake samun nasara suka yi dawayya kan karaga.

Hakazalika a shekarar 2015 ne kuma Kwankwaso ya daga hannun Ganduje inda ya zama gwamnan jihar ta Kano, kuma shekara daya bayan nan ne rashin jituwa tsakanin abokan siyasar biyu ta kunno kai har zuwa lokacin 2019, wani lokaci da rikicin ya fi ta’azzara.

Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top