Tsigitsila hausa novels complete

 👹 *TSIGITSILA* 👹

 *Shaidaniya Uwar Shaidanu*

~~~~~~~~~~~~~~~~~

          Short story

~~~~~~~~~~~~~~~~~

{Tsafi Shirka Ne, Duk Mai Yi Ya Halaka}

👨🏻‍💻 KING BOY ISAH ✍🏼

PART 1

°°°°°°°°°°

 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*

 

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

 ~*NOTE* Labarin Nan Bai Faru A Zahiri Ba, Jan Kunne Ne Ga Masu Mugun Hali~

Da sunan Allah mai rahma mai jin kai, tsira da amincin Allah su kara tabbata ga Shugabanmu gatanmu Annabi Muhammadu S.A.W

👍 Gaisheku Masoya Ko Ba Komai Kun Bani Kwarin Gwiwar Cigaba Da Rubutun. Muje Zuwa 

Kishi wani abu ne da Allah ya halitta haka zalika ya zama wajibi ga duk dan adam. kamar yadda so ya zama wajibi ga duk talikin da ke dauke da dunkulalliyar zuciya a cikin kirjinsa. Amma kuma ga wasu matan kishiya ya zama wani sinadari dake juyar da kwakwalwarsu, ya gusar da tunaninsu, kana ya mayar da su cikakkun shedanu. Kamar yadda ta kasance ga Kubura.

 Kishi Hassada Kyashi da rashin yarda da kaddara, game da taimakon malam boka da shedaniyar aljanarta Tsigitsila sun mayar da ita hatsabibiyar shaidaniya, marar tsoro mai kuma iya aikata komai domin biyan bukatarta. Kamar yadda Allah ya hore dare ga yan adam da wasu dabobbin ya zama lokacin hutu a garesu, ita kuwa Kubura lokacin ne garinta ya waye. Domin lokaci ne da take samun damar gudanar da shedancinta cikin sauki ba tare da wani cikas ba. 

Tafe take cikin duhun dare tsirara haihuwar uwarta tun daga gida ta ratso cikin gari ta nufi wata hanya da ta nufi jeji. Bata zame ko ina ba sai bakin makabartar kauyen nasu. Ba tare da tsoro ko fargaba ba ta kutsa kai cikin makabartar tana tafe tsirara bakinta na fadin wasu kalmomi a hankali cikin rada wanda basuyi kama da larabci ba haka zalika basuyi kama da cananci ba, balle indiyanci. Bata zame ko’ina ba sai bakin wani sabon kabari wanda take da tabbacin shine sabon kabarin da aka binne mamaci da rana.

 Tana zuwa ta juyawa kabarin baya nan take ta runtse ido tana cigaba da karanto dalasuman tsafi yayin da ta durkusa ta debo kasar kabarin da hannun hagu. Da debowarta ta tahowarta duk daya, yayin da ta canza kalmomin da take karantowa zuwa wasu kala daban a ciki tare da ambaton sunan Rakiya Jafi-Jafi. Bata zame ko’ina ba sai gida, ba tare da fargaba ko tsoron kar wani ya ganta ba ta afka gidan ta kutsa kai cikin dakinta.

Tana isa bakin wani kaskon wuta dake ci ta fara barbada wannan kasar kabari da ta debo tana cigaba da ambaton sunan Rakiya. Ta dakko wani tsumma ta saka a wutar, ta bude wani dan bokiti nan take ta kamo wani bera da ranshi amma an rubuta sunan rakiya a bayanshi ba shakka da jini akayi rubutu. Wuyan beran ta kama da karfi ta fuske nan take ta jefa kan beran a cikin kaskon wutar sannan ta tsiyaya jinin dake zuba a sama.

 Da faruwar haka nan take wata gigitacciyar dariya ta barke a dakin marar dadin saurare sannan wani jan hayaki ya dunkule waje daya ba jimawa ya jirkice zuwa wata mummunar tsohuwa yakunanna siririya marar kyan kallo. Fatar jikinta tsanwace mai ratsin baki, wasu manyan kuraje masu kama da maruru watse a fuskartata suna motsi sai kace zasu fashe. Hancinta dogo ne da ya gangaro ya kusan rufe bakinta lokaci bayan lokaci wani bakin jini na kwararowa daga ciki. Kwala-kwalon idanunta sunfi kama da idanun mujiya duk da kuwa sunfi na mujiya muni da ban tsoro. Domin kuwa kwayar idon yar karamace wani ruwan dorowa ya zagayeta. Gashin kanta da bai wuce a kirga ba dogone har kasa wanda ya kasance fari fat. Hakoran bakinta basu fi hudu ba, bakake marar kyan gani a bakinta da take faman wangala dariya da shi. Yanayin dage kai da tayi tana kyalkyala dariya irin ta marar imani shi ya kara mata muni gami da ban tsoro. Yanayin halittarta ko a cikin halittun aljannu mummuna ce ta karshe irin wacce gani na farko idan mutum yayi mata nan take zai sume ya fita hayyacinsa in akayi rashin dace ya sume.

 Amma kubura ko gizau batayi ba saboda ta saba ganinta haka zalika ita kanta yanzu shedaniya ce abar tsoro a cikin shigar bil adama. “Kubura tabbas bukatarki zata biya kinyi dukkan abinda nace kiyi. Ina gashinta da farcenta da na bukaci ki kawo min”. Aljanar mai suna Tsigitsila ce tayi wannan furucin yayin da ta mika zankalelen hannunta mai zara-zaran yatsu da farcina dogaye ga Kubura. 

Nan take Kubura ta mika mata wata leda dauke da gashi da kuma farce a ciki. Zuba su tayi a hannu kana ta runtse ido tana karanto wasu kalmomi nan da nan dakin ya rude da hayaniya gami da ihu da kururuwa iri-iri. Watsa gashin da farcen aljanan tayi cikin kaskon wutar nan take wani ihu da sautin kara marar dadi ya tashi hade da bayyanar wani bakin hayaki dake fitowa a hankali daga cikin wutar. 

Da faruwar haka Aljanar ta fashe da wata rikitacciyar dariya gami da cewa, “Sai ni Aljana Tsigitsila uwar shegu, kanwar shedanu, kakar azzalumai da mugaye. Kubura bukatarki ta biya”. Ko da fadin haka wacce aka kira da Kubura ta Fashe da dariyar farin ciki. “Rakiya karshen jin dadinki ya zo, karshen jin dadin yayanki ya zo,karshen haihuwarki ya zo. Tabbas lokacin fara ganin uku bala’i da masifu iri-iri gareki ya zo. Iko mulki da jan ragamar gidan nan daga yau ya dawo hannuna”. Hahahahaha! Nan take ta kara fashewa da dariya

~~~~~~~~~~~~~~~~~~~

👹 *TSIGITSILA* 👹

 *Shaidaniya Uwar Shaidanu*

~~~~~~~~~~~~~~~~~

          Short story

~~~~~~~~~~~~~~~~~

{Tsafi Shirka Ne, Duk Mai Yi Ya Halaka}

Part 2

°°°°°°°°°°

👨🏻‍💻 KING BOY ISAH ✍🏼

 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

 ~*NOTE* Labarin Nan Bai Faru A Zahiri Ba, Jan Kunne Ne Ga Masu Mugun Hali~

~~~~~~~~~~~~~~~~~~~

Kwance take da tsohon ciki haihuwa yau ko gobe a kan tsohon gadon katakonta wanda yaji jiki, karamin yaro wanda ba zai wuce shekaru biyu ba a gefenta. Can kasa kan tabarma wata yar budurwa ce wacce ba zata wuce shekaru goma ba. Sharar baccinsu suke hankali kwance. Wata razananiya kara ce ta kada hade da iska mai dan karfi wanda nan take fitilar dake kunne a dakin ta mutu. Kasancewar dakin a kulle da kofar katako ta tsakanin yan kananun kofafin da kasar kofar wani bakin hayaki ya fara shigowa dakin yayin da yake tafe dauke da wani gunji wanda ba kuka ba haka zalika ba dariya ba. Kai tsaye hayakin ya nufi Rakiya dake kwance rairan tana sharar bacci. Nan take hayakin ya fara duruwa hanci, baki, kunne da cikin zaninta. Ko da gama shigar hhayakin nan take Rakiya ta mimike yayinda jijiyoyin jikinta suka fara sauyawa zuwa baki. Ji tayi kawai an daga ta sama cikin iska an rabata da gadon. Yayin da tayi yunkurin ihu taji bakinta tamkar an daure. Lokaci guda azaba zafi radadi ya ziyarce yayin da taji tamkar ana yayanka hanjin cikinta. Ba dadewa jini ya fara kwarara daga kasanta tamkar da bakin kwarya. Ihu ko magana ya gagareta juyi take tana dunkule hannuwa tare da mimikewa cikin masifar zafi da azaba, tamkar ana yanka yaron dake cikinta. Hawaye kawai ke gangarowa daga cikin idanunta. Bayan dan lokaci taji an kado ta da karfi kan gadon, yanayin fadowar da tayi daga saman iska yasa Sale ya fado kasa daga kan gadon. Yayin da ya kwalla ihu tare da fashewa da kuka saboda zafin da yaji. Kukanshi ne ya tayarda Saude dake sharar bacci, ko da ta tashi taga daki duhu rudum ga Sale nata kwalla ihu nan take ta fara kiran “Mama-Mama”. Amma taji shiru ta jima a zaune tukun ta wartsake saboda kukan Sale da lalube ta lalubo fitilar da taji a kashe ta sake kunnawa. Duk da kasancewarta yarinya halin da taga mamar tata a cikin yayi mugun daga mata hankali. Kwance take cikin jini tana juya kai dakyar bisa ga dukkan alamu tana jin azaba. Da gudu Saude ta fito daga dakin ta nufi dakin Kubura tana kwalla kira “Inna Kubura-Inna Kubura Mama zata mutu”. Cikin kuka. Tuni ta tattare kayan tsafin ta sa cikin akwati ta tura karkashin Gado ta kwanta tamkar mai bacci kamar tasan abinda zai faru. Tana ji Saude tana buga kofa tayi murmushi hade da tashi cikin kidima ta bude dakin tamkar ba itaba tana jijiga Saude hade da tambayar me ya faru. Cikin in-ina “Ma—ma za… ta mutu”. Duk da kasancewarta dattijuwa a guje ta kwasa ta nufi bangaren Saude cikin tashin hankali irin na karya. Tare suka shiga dakin da Saude tana haska mata fitila. Kubura ta tallafo Rakiya tana fadin “Na shiga uku me zan gani haka, Rakiya me ya same ki? ko haihuwarce ta zo”. Kamar da gaske ta rasa yanda zatayi ta kalli Saude hade da cewa “Maza ruga da gudu ki kira Inna Haule watakil Haihuwa ce”. Saude najin haka ko fitilar bata karba ba ta fito ta sheka da gudu ta nufi gidan Inna Haule ko tsoron duhun daren bataji. Da fitarta Kubura ta tsaya kikam ta tsare Rakiya da kallo irin halin da ta shiga tuni ta hada jibi jini na kwararowa ta kasanta tana ta juyi cikin azaba amma baki yaki daguwa domin ta kasa cewa uffan sai nishi take hatta ihu ya gagareta. 

“Hahahahaha!” Dariyar farin ciki Kubura ta gagabe da ita, irin ta mugayen mutane wanda suka cika hade da tumbatsa a fannin zalinci, “Na dade ina jiran rana mai kamar ta yau, ganinki a cikin wannan halin ya yaye min kunci da bakin cikin da nayi shekaru sha takwas a ciki. Rakiya tun ranar da kika sako kafarki cikin gidan nan farin ciki da natsuwa suka gushe daga gareni. Ban kara shiga tashin hankali ba sai lokacin da kika Haifi Binta. Daga lokacin duk wata dariya da kika ga nayi iya hakuri ne bata isa zuciya ba. Tsawan shekarun nan kin tara ‘ya’yan kin shigo gida daga baya amma kin fini matsayi a wajen mijina saboda kina haihuwa ni bana yi. A duk tsayin shekarun nan ba irin maganin da ban nema ba nayi abubuwa kala-kala domin samun haihuwa hakan bata samu ba, don haka kamar yanda ba zan haihu ba yanzu na yanke hukuncin kashe duka ‘ya’yan da kike takama da su kuma a gaban idanunki, babu abinda zaki iya. in kashe ki, kamar yanda kika kika shigo gidan nan kika sameni mu biyu ni da mijina haka zaki tafi lahira ki barmu mu biyu. Kuma……”. Bata karasa maganar….

👹 *TSIGITSILA* 👹

 *Shaidaniya Uwar Shaidanu*

~~~~~~~~~~~~~~~~~

          Short story

~~~~~~~~~~~~~~~~~

{Tsafi Shirka Ne, Duk Mai Yi Ya Halaka}

👨🏻‍💻 KING BOY ISAH ✍🏼

Part 3

°°°°°°°°°°

 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

 ~Note- Babu Abinda Ya Faru A Gaske Daga Cikin Labarin Nan, Gargadi ne ga masu mugun hali~

Daga Karshe in kashe ki. Kamar yanda kika samemu mu biyu da mijina haka zaki tafi lahira ki barmu mu biyu da shi. Kuma ki…”. Bata karasa fadin abinda zata fada ba ta canza salo jin karan gudu da alamu su Saude ne suka dawo. Suna shiga dakin suka sama Kubura ta rike hannun Rakiya tana kuka tana fadin “Sannu Rakiya Allah ya baki lafiha ba zaki mutu ba”. Tana ganin sun shigo ta nufi Inna Haule tana kora mata bayani. Inna Haule tayi matukar kaduwa ganin irin jinin da Rakiya ta zubda. Nan take ta cigaba da dubata, idan nakuda ce Inna Haule bata taba ganin irin nakudar nan ba. Baki daya hankalinsu a tashe yake Saude ma dake yarinya ta dauki Sale ta Goya amma hankalinta sam ba a kwance ba. A tsaye suka kwana har safe Inna Haule tayi duk yan dabarunsu na ungozomai amma shiru Rakiya bata haihu ba.

 Kubura banda kukan karya babu abinda take tana nuna damuwa tamkar a jikinta ciwon Rakiya yake. Kande wata mai maganin gargajiya kasancewar kauyen nasu ba Asibiti. Itama ta zo tayi iya kokarinta amma ta gaza gane matsalar. Kauye da hadin kai cikin lokaci kankani mata suka cika gidan duk wacce taga halin da Rakiya ke ciki sai ta zubda hawaye. Duk ta fita hayyacinta banda nishi babu abinda take har karfinta ya kare. Zuwa lokacin sun zubawa sarautar Allah ido. Cikinta ne ya fara motsawa da karfi yayin da wani sabon bala’in ya kara turnuketa. Juyi ta fara tana nishi da kyar, kubura ta rike mata hannu cikin tausayawa tana mata sannu. Wani nishi ta saki mai karfi wanda nan take lumfashinta ya dauke na yan dakiku, daga kasanta Inna Haule ta kwalla ihu hade da wuntsilawa baya ganin wani katon bera ya fito daga mahaifar Rakiya maimakon taga jariri.

 Ai kuwa ta tashi tayi waje da gudu matan dake tsakar gida suna tofa albarkacin bakinsu ganin duk tsufan Inna Haule ta fito a guje tana ihu hade da cewa “Bera Bera ta haifa Bera”. sai ido ya koma kanta. Duk basu fahimci me take nufi ba sai bayan da sukaga murgujenen beran da ya fito daga cikin dakin cikin jini. Wanda girmansa ya kai girman jariri. Kafin kace kwabo gidan ya hautsine da guje-guje da ihu. Nan take ko wacce ta watse harda Kubura cikin yan gudu. Beran ya nufi bandaki yana zuwa ya zama hayake yabi iska. Saude dake rike da Sale yana kuka ganin kowa na gudu an bar gidan ta fada daki nan take ta iska mahaifiyar tata bata lumfashi a tunaninta ta mutu. Ai kuwa ta rungume ta itama tana kuka abun tausayi.

Malam Isiya jin abinda ke faruwa a matsayinsa na makwacin Malam Iro gashi kuma baya gida hakan yasa ya garzaya cikin hanzari ya nufi gidan malam Garzali wanda shine limamin garin haka zalika babu malamin da ya kaishi ilimi a garin. Ko da Malam Isiya ya gama korawa Malam Garzali bayani yace tabbas aikin aljannu ne. Dan haka cikin hanzari suka nufo gidan Malam Iro. Ya gama duk yan dube-dubenshi har ban dakin ya leka amma basuga wannan bera ba, don haka ya isa daki wajen Rakiya ya tofa mata addu’o bayan ya tabbatar wa malam Isiya cewa ba mutuwa tayi ba suma tayi. 

Bayan ya kare mata kallo yace tabbas wannan aikin sihiri ne ture akayi mata, amma zaiyi iya bakin kokarinsa ta hanyar rubutu da addu’oi ana bata tana sha. Godiya Malam Isiya yawa Malam Garzali kana ya rakashi. Daga karshe ya samu matan dake tsaitsaye a kofar gida suna tofa albarkacin bakinsu ciki harda Kubura. Ya shaida musu cewa Ture akayiwa Rakiya aikin asiri ne kuma ya tabbatar musu da cewa an nemi beran sama ko kasa an rasa. Da kyar ya shayo kan mata biyu kubura da matarshi cikon na hudu suka yarda suka koma gidan domin kura da Rakiya suma a tsorace suka shiga. 

Washe gari Mahaifin Rakiya Malam Audu tare da matarsa Hajja Kulu da kuma Kubura ne zaune sun sa Rakiya tsakiya cikin tausayawa. Wacce ta farka tun jiya amma magana ta gagara haka zalika sassan jikinta ba inda yake motsi, an dura mata abinci kala-kala amma sai dai ta amayo shi da kyar ake samu kadan ya tsaya a cikinta mai dan ruwa-ruwa. Cikin kwana guda har ta rame. Kubura ta nuna tamkar tafi kowa damuwa da halin da Rakiya ke ciki dan duk abinda ake na ba Kubura abinci ita ke yi. Malam Audu sai saka mata albarka yake. Hatta mutanen gari suna yaba mata yadda take hidima da kishiyar tata. Ko dake tun asali zubin salahai gareta an sansu da zaman lafiya ba’a taba jin kansu tsakaninta da Rakiya ba, hatta gardamar baki bata shiga tsakaninsu.

 Lokaci zuwa lokaci takan faki Idon Malam Audu Da Hajja Kulu ta watsawa Rakiya Harara wacce ita kanta Rakiya binta kawai take da kallo ciki da mamaki da bakin ciki. Bata taba tunanin Kubura zatayi mata haka ba musamman tsawon lokacin da suka dauka ana zaman mutunci. Shin wane irin kyautatawa ne batayi wa Kubura. Shin ko Kubura ta manta har yaro ta bata kawai saboda ta rage radadin haihuwa. 

A zuciya take tunani domin ba halin magana, shin ko dan ‘Dan da ta ba Kubura ya mutu shiyasa zata biyo mata ta wannan sigar, ita kam a irin zamansu na mutunci zata iya mallakawa Kubura duk ‘ya’yanta domin bayan mutuwar Muhammad me ta so ta ba Kubura Saude Malam Iro ne ya hana. Hawaye kawai ki gangarowa daga cikin idanunta dake runtse. Nan dai malam ya tafi ya bar Hajja Kula domin kula da Rakiya don kar aiki yayi wa Kubura yawa…….

👹 *TSIGITSILA* 👹

 *Shaidaniya Uwar Shaidanu*

~~~~~~~~~~~~~~~~~

          Short story

~~~~~~~~~~~~~~~~~

{Tsafi Shirka Ne, Duk Mai Yi Ya Halaka}

👨🏻‍💻 KING BOY ISAH ✍🏼

Part 4

°°°°°°°°°°

 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

 ~*NOTE* Labarin Nan Bai Faru A Zahiri Ba, Jan Kunne Ne Ga Masu Mugun Hali~

WAI-WAYE

Shekaru sha takwas baya lokacin da Iro ya bayyana bukatar iyayensa ta ya kara aure ga Kubura, Ta rikice ta gigice tamkar zatayi hauka don firgita, a zahiri kuwa murmushi tayi game da mai fatan alkhairi. Tabbas tasan cewa Inna Laure Da Babanshi suna bukatar ganin jikansu amma bata taba zaton zasu bullo mata ta wannan hanyar ba. Ko kadan bai lura da yanayin canjin fitar lumfashinta dake sama yana kasa ba. Haka zalika lokaci zuwa lokaci tana hadiye makwallaton bakin ciki dake zuwa mata wuya. Duk da kuwa har a zuciya baiyi zaton cewa idan Kubura taji zancen karin auren, magana mai dadi zata fito daga bakinta ba.

 Saboda haka ne ma ya kwantar da murya cikin sanyi yace, “Kubura kiyi hakuri banyi niyar kara aure ba iyayena ne suka tursasa sai na kara aure, saboda sun matsu su ga jikansu kinsan cewa ni kadai na rage a cikin ‘ya’yansu duk yan uwana sun rasu, na tabbata wannan dalilin yasa suka matsa lamba domin ganin na haihu. Na sha shaida musu cewa haihuwa ta Allah ce idan Allah ya kawo ta ba mai iya dakatar da ita, haka zalika idan Allah bai kawo taba, babu wani malam ko boka da zai iya jawo ta. Ni damuwata har yanzu ma bamu tabbatar da waye mai matsalar rashin haihuwa a tsakanina dake ba. Tana iya yuyuwa in karo aurenma aje nine mai matsala”.

 Ajiyar zuciya tayi game da furzar da iska a hankali ta rarumo jarumta da karfin hali ta budi baki tamkar babu abinda ke damunta tace, “Karka ce haka kabi umarnin iyayenka ni kaina zanyi farin ciki ace yau gashi ka haihu ka sama magaji ka tara zuri’ah kamar kowa. Ni kuma nasan cewa Haihuwa ta Allah ce idan ya nufe ni da yi zan iya haihuwa a ko da yaushe”. Tabbas ya tausaya mata, nan take ya cigaba da lalashinta kafin ya fito domin yasan abun da ciwo yadda wasu matan suka tsani kishiya a wannan zamanin ko mutuwarsu basu tsana haka ba. 

Yana fita ta fashe da matsanancin kuka tamkar ranta zai fita. A irin soyayyar da sukayi da Iro bata taba tunanin zai iya kallon kwayar idonta yace zai mata kishiya ba. Ko lokacin da suke soyayya tasha bayyana mai irin tsananin kishinta da yadda ta tsani kishiya. Amma saboda rashin kunya irin ta da namiji shine yau zai tunkareta da batun kishiya wai don bata haihuwa. Wuni tayi a daki tana kuka. Kwana biyu duk walwalarta ta dauke. 

Lokaci kadan aka sa auren Iro da Rakiya aka daura aure, auren kauye ba wuya. Allah kadai yasan irin tashin hankalin da Kubura take ciki ranar daurin aure amma ta boye a ciki da ita ake shagulgula. Bayan wata biyar zamansu lafiya duk da kasancewar Kubura na fama da bakin ciki da kunci amma bata taba yarda ko musu ya shiga tsakaninsu da Rakiya ba. Wasan ya fara ne daga lokacin da ciki ya bayyana jikin Rakiya. Murna a wajen Iro da iyayensa ba’a magana. Kowa Rakiya yake tarairaya bama kamar Inna Laure yadda ta maida hankali ga kula da Rakiya magunguna da yan dabaru irin na manyan matan kauye na masu ciki kullum cikin kawowa Rakiya take, musamman magani da turaren mayu da na baki. 

Kubura kuwa tun daga lokacin taji imani ya fita daga zuciyarta taji zata iyayin komai domin ta sama haihuwa. Karfe sha biyun dare ta nufi gidan Malam Garzali, kasancewar baya da aure bayan ta waiga ko’ina taga ba mai kallonta kai tsaye gidan ta fada da sallama. Yana jin muryarta ya fito ko da ya haska fitila yaga Kubura ce, nan take ya fashe da dariya gami da cewa, na dade ina jiran wannan rana Kubura nasan dole wannan rana zata zo kuma zaki sake nemana mu shiga daga ciki. 

Ba musu ta bishi cikin dakin bayan sun zaune. Ta dube shi cikin hawaye tace, “Yau na zo gareka da bukatu biyu, na farko ina son haihuwa ko ta halin yaya ne, ko da kuwa kai zaka sadu dani kamar yanda ka bukata a farko naki amincewa. Na biyu kuma ina so ka kashe mun iyayen Iro daya bayan daya”. Dariya ya kyalkyale da ita irin ta mugayen mutane. Zai iya aikata komai domin ya mallaki Kubura ya dade yana hadiyar yawu a kanta saboda irin tsarin halittar da Allah yayi mata. Kasancewar shi malami a garin yasa bai taba bayyana wannan mummunan kudiri gareta ba har sai lokacin da ta kawo mai bukatar neman haihuwa……..~~~~

👹 *TSIGITSILA* 👹

 *Shaidaniya Uwar Shaidanu*

~~~~~~~~~~~~~~~~~

          Short story

~~~~~~~~~~~~~~~~~

{Tsafi Shirka Ne, Duk Mai Yi Ya Halaka}

👨🏻‍💻 KING BOY ISAH ✍🏼

Part 5

°°°°°°°°°°

 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

 ~*NOTE* Labarin Nan Bai Faru A Zahiri Ba, Jan Kunne Ne Ga Masu Mugun Hali~

A CIKIN WAI-WAYE

…. Bukatar neman haihuwa, don haka yayi amfani da damarshi ya bayyana mata cewa idan har tana son haihuwa to tilas ta amince ta rika zuwa suna aikata zina. A cewarsa ta haka ne kadai zata samu haihuwa, Ya tabbatar mata da cewa mijinta ne baya haihuwa. A wannan lokacin Kubura ta nuna rashin amincewarta haka zalika ta nuna fushi game da mamakin jin furuci irin wannan daga bakin Malam Garzali a matsayinsa na babban malami a kauye. Lokacin da yaga ta hassala ta nuna bacin rai da kin amincewa nan take ya nemi afuwarta da bukatar ta rufa mai asiri karta tona mai asiri. Da kyar da magiya ta yarda ta amince ba zata tona mai asiri ba, sai gashi yau Allah ya kawo ranar da ta kawo mai kanta. Kallonta yake yana hade yawu yace, “Bukatunki baki daya zasu biya idan har kin yarda da sharuddan da zan gindaya miki Kubura. Na farko batun kashe Iyayen Iro abu mai sauki ne abu biyu kacal nake bukata daga gareki. 

Na farko sunayensu, na biyu wani abu nasu kamar gashi ko farce ko fatar jikinsu ko kuma jinin jikinsu. Haka zalika za’a iya yin amfani da kayan sawansu ko matajin kai ko dai wani abun da suke ta’amali da shi yau da kullum. Da zarar kin kawo wannan ki sa a ranki bukatarki ta farko ta biya.

Bukatarki ta biyu kuma kamar yanda na fada a baya dole zaki rika zuwa duk bayan kwana biyu ina saduwa dake, nasan cewa bakya haihuwa amma akwai yan dabarun da zanyi ta hanyar tarawa dani ki sama ciki har ki haihu a cikin lokaci kankani”. Kubura ta sauke ajiyar zuciya sannan tace “Duk babu matsala zan iya aikata komai domin bukatuna su biyu”. Dariya Malam Garzali ya fara yi sannan ya fara cire riga. Nan take suka fara aikata zina kamar yadda ya bukata. Da dingishi Kubura ta fito daga dakin malam, domin ji tayi tamkar da wata katuwar halitta sukayi lalata ba Malam Garzali ba. Haka dai ta daddaure ta nufi gida bisa sharadin zata kawo mishi abinda ya bukata domin kashe Iyayen Iro. 

A cikin sati biyu ta hado abinda Malam Garzali ya bukata, domin mayar da gidansu iyayen Iro tayi wajen wunin ta. Su kansu sunyi mamaki yadda take zuwa ta wuni tana taya Inna Laure ayyuka, diban ruwa shara wanke-wanke, Duk da kuwa irin kyara da tsangwama da take sha wajen Inna Laure. A ranar da Allah ya bata sa’a Inna Laure na tsefe kai taje ta amsa tamkar abun kwarai tana taya ta a haka ta samu ta mallak’e gashin kan Inna Laure. Yayin da shi kuma Baban Iro ta lalaba dakinshi ta sace mai hula domin tabi duk hanyoyin da zata bi domin samun wani abu na jikinshi amma abu ya gagara. Kamar yanda ta saba tsakar dare wajejen karfe biyu kafa ta dauke ta nufi gidan Malam Garzali ta kai mai hula da gashin Inna Laure da ta makale, Sannan ta fadi mai sunayensu. Yau ma bai kyaleta ta fito haka kawai ba sai da suka aikata fasikanci dama satin da ya gabata taje sunyi. 

Duk da kasancewar daurewa kawai take domin neman biyan bukatar kanta amma ita kadai tasan irin bala’in da take ji idan suna aikatawa. Gida ta tafi cikin farin ciki ta kwnata domin Malam Garzali yayi mata albishir da mutuwar Baban Iro. Da fitarta Malam Garzali ko kayan jikinsa bai mayar ba ya jawo wata kwarya dake ciki da wani ruwa ja mai kamar jini……..

👹 *TSIGITSILA* 👹

 *Shaidaniya Uwar Shaidanu*

~~~~~~~~~~~~~~~~~

          Short story

~~~~~~~~~~~~~~~~~

{Tsafi Shirka Ne, Duk Mai Yi Ya Halaka}

👨🏻‍💻 KING BOY ISAH ✍🏼

Part 6

°°°°°°°°°°

 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

 ~*NOTE* Labarin Nan Bai Faru A Zahiri Ba, Jan Kunne Ne Ga Masu Mugun Hali~

Hular Baban Iro ya jefa cikin ruwan sannan ya daukko tawada da takarda ya rubuta sunan Baban Iro Malam Dalha kamar yadda ta fada mishi, takardar ya jefa cikin ruwan. Wuka ya daukko ya yanka yatsarshi ya disa jinin a cikin ruwan. Nan take ya rufe ido yana karanto wasu maganganu wanda bayan sunan Dalha babu abinda zaka fahimta a ciki. Da faruwar haka wata irin iska mai karfi ta fara kadawa a dakin nan take wuta ta kama ci a cikin kwaryar, yayin da wani irin ihu da hayaniya yaci gaba da fitowa. Malam Dalha yana kwance kan tsohon gadonshi wata bakar halitta ta bayyana nan take ta shake mai wuya yayi halbe-halbe har ya gaji ya kasa kwacewa a haka har ya mutu.

Kukan mutuwa ne ya tashi Kubura daga bacci da asuba, Rakiya ce mai kukan da ihu, ta tabbatar zuwa akayi aka fadi mutuwar. Al’adar kauye kuwa idan bakayi kuka da ihun nan ba ya zama abun magana dan jahilci. Maimakon ayiwa mamaci addu’a sai dai ihu da fadin na shiga uku. Haka itama Kubura ta fito duk da kuwa tasan abinda ya faru ana fadi mata itama ta fara kururuwa da ihu game da kukan karya. Malam Garzali ne da kanshi yayiwa Baban Iro sallah akaje aka binne shi. Bayan kwana biyu Malam Garzali ya sake yin tsafi ya kashe Inna Laure. Mutanen kauye kuwa a tunaninsu bakin cikin mutuwar Malam Dalha ne yayi ajalin Inna Laure. 

Iro yayi bakin ciki sosai bisa rasuwar mahaifanshi ba tare da ganin jikansu ba. Kubura ba karamin farin ciki tayi ba ganin wannan aiki da tasa malam Garzali anyi nasara yasa ta sakankance cewa zata sama haihuwa. Dan haka duk da azabar da take ji ta daure ta cigaba da zuwa wajen malam suna fasikanci. Abinda bata sani ba kuwa da wani aljani take aikata zina ba da Malam Garzali ba. Dan a duk lokacin da zasu aikata aljanin ke shiga jikin malam Garzali domin wata biyan bukatarshi. 

Shekaru uku suka shude Kubura bata sama ciki ba, lokacin Rakiya ta haifi yarinya har ta sake samun wani cikin ya girma. Hankalin Kubura yayi matukar tashi dan haka taje tasa Malam Garzali ya zubar da cikin Rakiya kuma ya tsayar mata da haihuwa bayan sunye kulle-kullen su da asiri.  

Bisa ga mamaki sai gani tayi Rakiya ta sake samun ciki inda nan take ta sake komawa Wajen Malam Garzali da bukatar kawai ya kashe su baki daya daga Rakiya har yarinyarta, zuwa lokacin ita tama hakura da samun haihuwa. Malam Garzali ya amsar bukatarta inda ya bukaci ta daukko mai wani abu da suka taba tabawa kamar kayan sawa ko wani abu mallakin Rakiya da diyarta Bintu. Kasancewarsu a gida daya bata wani sha wahala wajen samowa ba. Bayan ta kai mai yayi bokancinshi tsakar dare washe gari Kubura na jira taji kuka mutuwa amma taji shiru har gari ya waye rana tayi. Dare na yi ta sake komawa inda ya bayyana mata cewa shi kanshi baisan dalilin da yasa asirinshi baiyi tasiri a kan Rakiya da Yarta ba. Nan ya shaida mata cewa shi dama tsafi ya gaji haka ba wani asiri ko tsafi da zaiyi tasiri a jikin wani dan adam sai da yardar Allah. 

Bayan ta nuna damuwarta kwarai yace mata akwai hanyoyi da yawa wanda zata bi ta jaraba domin kashe su Rakiya da taimakonsa. Amma da hatsari idan zata iya kuma sai ta cire tsoro. Kasancewar zuwa lokacin shedan yayi wa Kubura tofi a kai baki daya bata tuna lahirarta balle karshenta a duniya, gaba daya wani tsoro ya fita daga ranta babu abinda ta sa gaba face ganin bayan Rakiya. Don haka tace ta aminta abi hanyoyin. Da farko bata wani hayaki a cikin bakar leda sannan ya rubuta mata wani hatimi a jiki takarda da sunan Rakiya da yarta Bintu ya bata yace ta bari sai ranar laraba tsakar ta sa bakaken kaya taje gindin bishiyar kuka wacce ke cikin daji ta kalli yamma sannan ta kunna wuta a kasoka tayi hayakin da ya bata tare da kona wannan hatimi hade da fada mata sunan wasu aljannu yace ta runtse ido ta rika karanta su, ya gargadeta tabbas idan aka sama matsala aljannun zasu mata dan banzan duka saboda haka ma ya nanata mata sunayensu sosai.

Tayi kamar yadda ya fadi amma daga karshe dukan tsiya akayi mata, ta dawo gida jiki duk a kunbure. Karo na biyu ta sake komawa, yasa ta samo kwan bakar kaza da kafar farar mage, haka ta kawo mai bayan yayi rubuce-rubucen da tsafe-tsafinsa ya ba Kubura yace ta je ta Binne a gindin shiru, amma ta tabbatar ta binne a inda babu wanda zai gani balle ya tone, domin idan har aka tone ko me ya biyo baya ita ta jawa kanta shi ba ruwanshi, amma idan har ba’a tone ba cikin kwana uku kacalla Rakiya da Bintu zasu kamu da cutar da zatayi ajalinsu. Kubura bata daddare ba taje tayi kamar yadda ya umarta, daga karshe bayan ta binne kwan da ke zagaye da rubutu da kafar mage da aka zagaye da wani zare da farin kyalle. Aka sama akasi batayi rami sosai ba wajen binnewa domin a tsorace tayi ramin gashi tsakar dare bata manta ba ance Shiru gidan macizai ne bata tsoron aljannu kamar macizan.

👹 *TSIGITSILA* 👹

 *Shaidaniya Uwar Shaidanu*

~~~~~~~~~~~~~~~~~

          Short story

~~~~~~~~~~~~~~~~~

{Tsafi Shirka Ne, Duk Mai Yi Ya Halaka}

👨🏻‍💻 KING BOY ISAH ✍🏼

Part 7

°°°°°°°°°°

 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

 ~*NOTE* Labarin Nan Bai Faru A Zahiri Ba, Jan Kunne Ne Ga Masu Mugun Hali~

WAI-WAYE…..

Kwana daya da faruwar haka, ciwo ya kwantar da Rakiya Da Bintu. Aman jini ta hanci da baki, kowa ya rasa kan cutar. Tsautsayi ya ratso da yayan fulani ta wajen da Kubura ta binne sihirinta, suka zaro abubuwan da ta binne. Ko da gani suka ruga suka kira manyansu. Su kuma sukayi wa kayan sihirin fitsari hade da banka musu wuta. Da faruwar hakan Rakiya da yarta suka sama lafiya lokaci guda akaga Rakiya ta warware tamkar ba ita ba, kowa na murna yayin da ita kuma Kubura hankalinta yayi matukar tashi. Ba tare da sanin kowa ba ta koma inda ta binne asirin taga an tone an kona tabbas hankalinta ya tashi gashi ba damar zuwa wajen malam boka Garzali domin da daddare ne kawai take samun damar zuwa wajenshi da rana gidanshi baya rabo da yan kauye masu zuwa koyan karatu da sauran dattawa.

Tun kafin ta koma gida ta fara jin rashin lafiya, ai kuwa tana zuwa bakin kauyen ta zube a wajen tana aman jini cutar jikin Rakiya ta koma kanta sai mutane suka kaita gida. Cikin tsanain ciwo tace Iro yaje wajen Malam Garzali ya nemo mata magani. Malam Garzali yana jin zancen ya gane abinda ke faruwa, dan haka ya shiga nemo makarin asirin, da kyar ya samu ya hada shi cikin kwana biyu, lokacin Kubura taji jiki dan har ta sadaukar ma mutuwarta ce ta zo.

Bayan ta warke batayi saranda ba ta sake komawa dai wajen Malam Garzali da bukatar a kashe su Rakiya, Malam Garzali bai mata musu ba domin baya bukatar kudinta jikinta kawai yake bukata da shi take biyanshi, don haka yake biye mata. Sun gwada hanyoyi kala daban-daban kasancewar mutum ko aljan bai isa ya kashe wani rai ba face kwanansa ya kare. Don haka basu samu ikon Kashe Rakiya da Bintu ba. Kubura ta binne laya a kabari ba iya ka, saboda abubuwan bukata domin yin tsafi sai da ta sayar da dabbobinta baki daya amma bukata bata biya ba. A lokacin Rakiya ta sake Haifar mace aka sa mata suna Haule. Nan take bakin ciki ya kara kama Kubura ganin haihuwar Rakiya ta dawo.

 Ranar taje wa Malam Garzali tana kuka, Daga karshe Malam Garzali ya tabbatar mata da cewa babu wanda zai iya kashe mata Rakiya da Iyalanta face Aljana Tsigitsila shaidaniya uwar shedanu. Cikin damuwa yace mata amma mallaka Aljana Tsigitsila ba abu ne mai sauke ba. Akwai sadaukarwa, kauce hanyar Allah, game da bata lokaci. Kubura tace zata iya yin koma minene kuma zata iya sadaukar da komai ita burinta daya a duniya shine taga gawar Rakiya da iyalanta. Malam Garzali bai mata gardama ba ya fara zayyano mata sharuddan mallakar aljana Tsigitsila kamar haka. 

Domin mallakar aljana Tsigitsila a ranar farko zatayi tsirara yayi mata wani rubutu a jikinta da jinin jaba, zataje gindin tsamiya a tsirara ta rufe idonta ta karanta sunan tsigitsila kafa dubu biyar. Daga wannan rana dole ta daina sallah sai lokacin da take jini, (Waiyazubilllah) kuma duk lokacin da tayi sallar bayan ta gama ta ambaci sunan Tsigitsil kafa dubu. A haka har a cika shekara shekara uku, yace mata idan ta tabbatar shekara uku ta cika cif sai ta koma wajen tsamiyar nan zai bata wasu dalasuman tsafi wanda zataje ta karanta sannan ta kira sunan Tsigitsila hade da mutumin da ta sadaukarwa aljanar. Ya tabbatar mata da cewa idan tayi haka tabbas ta mallaki aljana Tsigitsila. Ya kara da cewa aljana Tsigitsila tana daya daga cikin Ifiritai shedanun aljannu masu bakar zuciya marar imani. Ayar Allah kadai take iya tasiri a kansu. Ya kuma san cewa Rakiya da Yayanta a kauyen suke basu da ilimin addini bale su iya kare kansu daga duk makircin aljana Tsigitsila.  

Ko da jin haka cikin farin ciki Kubura tace ta amince da duk sharuddan nan ba tare da fargaba ba, ko can dama bata damu da sallah ba, balle barinta ya zame mata wani babban aiki. Malam Garzali ya dube ta yace ai bata tsaya taji karshen ba, ita aljana Tsigitsila bata karbar kowa a matsayin sadaukarwa sai jini. Mahaifiyarki ko babanki ko yayanki ko kaninki. Ke kuma baki da yan uwa sai uwa da uba suka rage miki idan ba su zaki sadaukar ba, kuma babban hatsarin a nan shine shekara uku zata iya cika kije ki sadaukar da wani daga cikinsu amma bukatarki ta ki biya na mallakar Tsigitsila. Domin kuwa idan har kikayi kuskure daya zai iya jawo miki wannan asara, ta bata lokaci, ta sabon Allah da kuma rasa mahaifa. 

Kubura ta danyi jim kadan sannan tace ta aminci, kuma a lokacin take so yayi mata rubutun domin ta fara tun daga ranar. Haka kuwa akayi tayi zindir yayi mata rubutun tsafinsa ciki duk da sunan aljannu, daga karshe taje tsamiya ta aikata kamar yanda ya umarta. Bayan shekara uku ta koma ta karanto abinda malam Garzali ya fada mata hade da sunan Tsigitsila. Nan take sai gani tayi gari ya cika da duhu da walkiya can ta hangi mahaifinta a hannun wata aljana ta shake mai wuya jini na kwarara daga idonsa da bakinsa. Aljanar tana gagaba dariya marar dadin saurare ta kalli kubura tace “Bakiyi nasara ba kuma rai da lokaci da kika sadaukar sun tafi a banza”. Nan take aljanar ta bace. Hankalin Kubura yayi matukar tashi ta koma gida cikin fargaba da sassafe aka aiko mata rasuwar mahaifinta……………..

👹 *TSIGITSILA* 👹

 *Shaidaniya Uwar Shaidanu*

~~~~~~~~~~~~~~~~~

          Short story

~~~~~~~~~~~~~~~~~

{Tsafi Shirka Ne, Duk Mai Yi Ya Halaka}

👨🏻‍💻 KING BOY ISAH ✍🏼

Part 8

°°°°°°°°°°

 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

 ~*NOTE* Labarin Nan Bai Faru A Zahiri Ba, Jan Kunne Ne Ga Masu Mugun Hali~

Hankalin Kubura yayi matukar tashi ta koma gida cikin fargaba da sassafe aka aiko mata rasuwar mahaifinta. A cikin shekaru ukun ne kanwar Rakiya dake aure a birni ta roki Iro da Rakiya suka bata rekon Bintu, Dama fitinar Bintu tayi yawa a kauyen kullum cikin kawo kararta ake duk da kasancewarta karama, dan haka suke sa ran shiryuwarta a birni. Kuma Rakiya ta haifi Namiji saboda irin zaman kwanciyar hankali da suke ta mallakawa Kubura yaron mai suna Mahammud. Domin duk shedancin da Kubura take babu wanda ya sani daga ita sai malam sai kuma Allah da baya bacci. Kasancewar da daddare take cin kasuwar shedanunta.  

Ba tare da sake tunani ba Kubura ta sake komawa wajen Garzali ya sake mata rubutu ta sake komawa da bukatar mallakar Aljana Tsigitsila. A wannan shekarar ta cika shekaru uku haka zalika wannan karon tayi nasarar mallakar Aljana Tsigitsila. Duk lokacin da take bukatar ganin Aljanar domin wata bukata, ta kan shiga bandaki ta yi fitsari sannan ta lashi fitsarin, ta daga kanta sama ta kira sunan Tsigitsila sau uku. Bukata ta farko da Kubura ta nema a wajen Aljana Tsigitsila shine sawa Rakiya cuta sannan ta rufe bakinta ta yadda zata kashe duk yaranta a gaban idonta daga karshe itama ta kashe ta. Nan take kuwa aljana Tsigitsila ta zayyano mata abubuwan da zata aikata domin faruwar hakan ciki harda zuwa makabarta tsirara ta debo kasar sabon kabari. Wanda da shi sukayi amfani suka sakawa Rakiya cuta ta hanyar sihiri………..••••••………

Cigaban Labarin

Dare ya tsala gari yayi duhu Haule Da Sale Tuni sunyi bacci. Kubura ce zaune gaban Rakiya da baccin ma baki daya ya gagare gareta saboda zafin ciwo. A gidan Hajja Kulu ta wuni tare suke ta Hidima da karban yan dubiyar Kubura, sai da dare yayi Kubura ta lalabi Hajja Kulu a kan ta tafi gida itama ta hutawa ranta ita Kubura zataci gaba da Jinyar Rakiya.

 Haka kuwa akayi tana zaune tana kallon Rakiya dauke da murmushin mugunta a fuskarta Allah kadai yasan abinda take sakawa. Zuwa can jin gari yayi shiru ta dubi Rakiya tace, “Rakiya nasan cewa yanzu zuciyarki cike take fall da mamaki yadda lokaci guda na rikide na koma makiya a gareki. Sai dai kuma abinda baki sani ba shine tun kafin ki shigo gidan nan na tsane ki, na tsani mai kaunarki. Saboda tsabar tsanar da na miki na tsani mai sunanki Rakiya tunda naji sunanki a matsayin kishiyata. Saboda iyayen Iro na kaunarki ke da abunda zaki haifa nasa aka kashe su. Duk wani kyautatawa da nake miki tamkar zagon kasa ne a gareki. Nasan zaki kadu matuka idan kika san cewa da hannuna na kashe Mahamud, kwarai guba na dura mai a baki ya kamu da ciwo wanda yayi ajalinsa. A tunaninki bani shi da kikayi zai kashe wani radadin zafin kishina a kanki? Na so da ace kin kara bani wani daga cikin yarinki shima da haka zan kashe shi ba tare da saninki ba.

 Ke kuma dama lokaci kawai nake jira domin ganin bayanki. Yanzu kinsan abinda zai faru? Zan sa wa Iro tsanarki da ta ‘ya’yanki. Ta yadda ko kallonki zaiji baya kaunar yi balle ma ya matso kusa dake. Nasan kina murna gobe zai dawo ko? Ki jira kiga zuwanshi zaki sha mamaki Rakiya”. Da gama fadin haka ta kama Kan Rakiya, tana kokarin kwacewa amma ba hali haka ba damar ihu. Wani tsanwan ruwa dake cikin kwalba ta disawa Rakiya a cikin idanu. Sannan ta tsigi gashin girar Rakiya guda biyu ta ko wane ido. Tasa allura ta huda yatsar Rakiya ta disa jinin a cikin kwalbar tana dariyar mugunta tace, “Daga yau zaki rika wari fiye da na Bodari a wajen Iro. Haka zalika zai tsaneki ya tsani ‘ya’yanki”.  

Hawaye ne kawai ke gangarowa daga idon Rakiya domin tana jinta kuma tana kallonta duk abinda take. Gashin ta jefa a cikin kwalbar, bayan ta karasa abinda take ta fice daga dakin ta nufi dakinta, da zuwa ta daga wani kwano ta kamo bodari dake ta kokowar kwacewa. Ta taka shi ta yanka a tsakar dakin nan take ta tsiyaya jinin bodarin a cikin kwalbar. 

Da faruwar haka dakin ya gauraye da dariya irinta shedanun aljannu sai ga Aljana Tsigitsila ta bayyana, “Bukatarki zata biya Rakiya kinyi komai yadda na umarce ki babu kuskure”. Da fadar haka ta mika hannu ta karbi kwalbar ta tofa yawun bakinta hade da fara fadin wasu kalamai da wani yare wanda babu abinda zaka fahimta a cikinsa face sunan Iro da Rakiya. Da faruwar hakan jinin dake cikin kwalbar ya fara tafasa na dan lokaci nan take ya koma baki kirin. Ta mikawa Kubura Kwalbar tace taje ta binne a kofar dakin Rakiya. Nan take aljanar ta bace, ita kuma ta nufi kofar dakin Rakiya domin binnewa……….

👹 *TSIGITSILA* 👹

 *Shaidaniya Uwar Shaidanu*

~~~~~~~~~~~~~~~~~

          Short story

~~~~~~~~~~~~~~~~~

{Tsafi Shirka Ne, Duk Mai Yi Ya Halaka}

👨🏻‍💻 KING BOY ISAH ✍🏼

Part 9

°°°°°°°°°°

 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

 ~*NOTE* Labarin Nan Bai Faru A Zahiri Ba, Jan Kunne Ne Ga Masu Mugun Hali~

*Aslm Kuyi hakuri bisa samun page daya kadai kwana biyun nan, ni kaina ina burin kammala littafin nan kafin azumi amma yanayin yau da kullum ba ko da yaushe nake samun dama ba.*

Fitowarta daga daki yayi dai-dai da sako kafar ido, ko da ganinshi Kubura ta sa shewa hade da nufar shi tana lale maraba. Jakar hannunshi da ledar ta karba ta nufi dakinta a nufinta ya bi bayanta. Sai gani tayi ya nufin hanyar kewayan Rakiya a hanzarce ta juyo tace, “Ina kuma zakaje ai ya kamata ka dan shigo daki ka huta kafin ka shiga nan ko? Tunda ni na fara ganinka”. Juyowa yayi ya dube ta baiyi mamaki ba domin yasan halin kishinta duk kuwa da kokarin boyewa da take. “Haba Kubura kinsan fa wannan zuwan ba zuwan lafiya bane. Zuwan lalura ne kinga kuwa ba bukatar hutawa dama saboda marar lafiya na zo to kinga kuwa dole na fara zuwa naga yanayin jikin nata kafin mu fara neman magani”. 

Yana gama fadin haka yayi gaba, Kubura ta bishi da kallo tare da murmushin mugunta, hade da cewa “Ayi mu gani idan tusa zata hura wuta”. Da fadar haka ta kwashe da dariya yana jinta bai kulata ba yayi gaba. A dai-dai lokacin da ya taka kofar dakin Rakiya wani mugun wari ya daki hancinsa wanda bai taba jin kalarshi ba tunda yake a rayuwarshi. Hannu yasa ya rufe hanci kana ya daure ya karasa cikin daki. Yana shiga suka hada ido da Rakiya nan take yaji kanshi na juyawa hade da wani masifafen ciwon kai na lokaci guda. Da faruwar haka yaji ya tsani Rakiya baya so ya kara ganinta a rayuwa. 

Saude dake zaune tana damawa Sale Fura da sauri ta taso ta nufi mahaifin nata tana mishi sannu da zuwa. Tun kafin ta karasa ya daka mata tsawa hade da fadin “Bace mun da gani”. Tsaye tayi kikam tana kallon baban nata cike da mamaki. Yau duka ba’ayi wata uku da tafiyarshi birni ba. In zata iya tunawa a tarihin rayuwarta bai taba yi mata tsawa ba. Sale ne ya taso da sauri ya nufin baban nashi da nufin ya dauke shi kamar yadda ya saba. Ai kuwa yana karasawa Iro ta hankade shi nan take ya fadi kasa yana kuka. Saude da abun ya bara bata tsoro duk da kasancewarta yarinya, cikin sanyi tace, “Sannu da zuwa babu ina wuni”. “Ban wuni ba dan uwarki, kiyi mun shiru ko in fafasa miki baki yanzun nan. Kun zo kun cika min gida da wari ke da uwarki”. Iro ne ya fadi haka hannunshi rike da hancinshi

Rakiya ba karamin kaduwa tayi ba domin tana jin abunda ke faruwa, zuciyarta cike da kunci hawaye suka gangaro daga idanunta domin tasan cewa ba Ironta bane mijinta ba haka yake ba aikin sihiri ne. Tana so tayi magana ba damar yi. Iro ya dube ta tana kwance cikin mawuyacin hali hade da cewa “Rakiya kin ban mamaki wannan wane irin hauka ne haka zaku cika min gida da wari ke da ‘yayanki? Ko ance miki rashin lafiya hauka ne? Saboda baki da lafiya shikenan kuma sai akace miki ki zama kazama? To tunda haka kika zaba ki Rakiya na tsane ki, na tsani yayanki bana son ganinki haka zalika bana son ganin yayanki, da ace kina iya tafiya da yanzu zan kore ki ku fita ku bar min gidana”. Gabanta ne ya fadi rass da jin kalamanshi, innalillahi kawai ta fara mai-maitawa a zuciya cike da tsoro da fargabar kar Iro ya saketa a cikin wannan hali na asiri domin tasan cewa ba yin kanshi bane.

Nan dai Iro yaita zazaga musu masifa ta inda yake hawa ba ta nan yake sauka ba. Daga jin zancen kai kasan ba na hankali bane. Kubura dake labe a bakin kofa tana jin abinda ke faruwa nan take farin ciki ya kumeta. Tabbas lokaci yayi da Rakiya zata dandani irin dacin bakin cikin da ta shiga a baya a sanadinta. Jahilci yasa Kubura ta manta da Allah, tunda ta mallaki aljana Tsigitsila ji take tamkar ran kowa na hannunta zata iya kashe duk wanda ta so a duk lokacin da taga dama. Sai dai kashe ta manta cewa bokaye da shedanun aljannu makaryata su kan kai mutu su baro shi a yayin da suka gama amfanarshi.

Rakiya ce kwance tana bacci Sale na kwance shima a gefanta suna sharar bacci. A hankali Kubura ta bude dakin ta shigo, a dai-dai saitin Sale ta tsaya yayin da ta fiddo wata filleliyar wuka mai kaifi sai walkiya take. Nan take ta caka wa Sale wukar a ciki, ya kwalla kara yayin da jini yayi Feshi nan take ya mutu. Karar shi ne ya tayar da Rakiya. Kubura tayi saurin tsallakawa kan gado tasa igiya ta shake wuyan Rakiya da karfi. Nan take Rakiya ta fara mimikewa ranta zai fita bayan ta kasa kwacewa.

Firgigit ta farka tare da dafe kirji tana karanto Innalillahi wa’inna Illahir raji’un, neman tsari a wajen Allah tayi daga sharrin mummunan mafarkin da tayi, kallo daya zakayi mata ka gane cewa a matukar kidime take tabbas hankalinta ya tashi. Kuka ta fashe da shi ba dan komai sai dan sanin cewa bata yin mafarki duk kuwa mafarkin da tayi sai ya zama gaske. Tana ganin abubuwa da yawa a mafarki wanda kuma sukan zo su zama gaske. Ta fada a gida idan tayi mafarki yana zama gaske amma ba’a yarda ba. Daga karshe ta daina fadawa kowa saboda taji ance duk wanda yake mafarki kuma mafarkin ya zama gaske to maye ne. Dadin dadawama bata kwanciya sai tayi alwala, kuma ta karanta falaqi da nasi hade da surori uku na karshen suratul baqara domin haka malamansu suka umarce su da yi a duk lokacin da zasu kwanta. 

Shiyasa hankalinta ya tashi tabbas tasan cewa abinda ta gani a mafarki zai zama gaske. “Me yasa Mama Kubura? Taya ma hakan zai faru, kai aa gaskiya hakan ba zai taba faruwa ba. Babu ta yadda za’ayi mama Kubura ta kashe mamanmu, matar da take son cigabanmu fiye da nata. Sharrrin mafarki ne kawai. Gabanta ya fadi da ta tuna cewa tayi mafarkai ba adadi a baya kuma sun tabbata gaskiya. A kan nuna mata abu ko da ta hanyar misali ko kwatance ne a mafarki kuma ya zo ya zama gaske a zahiri. Saboda haka ta kuduri niyar tafiya kauye goben nan. Domin ba zata taba samun natsuwa ba…………………

👹 *TSIGITSILA* 👹

 *Shaidaniya Uwar Shaidanu*

~~~~~~~~~~~~~~~~~

          Short story

~~~~~~~~~~~~~~~~~

{Tsafi Shirka Ne, Duk Mai Yi Ya Halaka}

👨🏻‍💻 KING BOY ISAH ✍🏼

Part 10

°°°°°°°°°°

 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

 ~*NOTE* Labarin Nan Bai Faru A Zahiri Ba, Jan Kunne Ne Ga Masu Mugun Hali~

Kuyi hakuri dai I’m busy wallahi

Nafisa kanwar Rakiya da mijinta, ba yadda basuyi ba su lalashi Bintu game da batun zuwa kauye amma ta nace sai ta tafi. Kasancewar sun san halinta da naciya game da kafiya ba yadda suka iya haka suka kyaleta ta tafi. A gaggauce ta shirya ta hau mota ta nufi kauyen Dan Inna. ji take tamkar motar bata gudu domin kuwa ba karamin girgiza tayi ba da Mama Nafisa tace dama an kirata ance maman nata ba lafiya. Gani take kamar kafin ta isa gidan Kubura ta kashe mamanta da Sale. Sai bayan la’asar ta isa garin kasancewar tafiyar da ake cikin yashi ma bayan an sauka daga mota tana da nisa kafin a karasa kauyen Dan Inna. Da sallama Kubura ta fito da sauri ta tarye ta tana farin ciki. Ita kuwa Bintu bin Kubura kawai take da kallon zargi hade da kakalo yake. 

Saude ce ta fito da gudu dauke da Sale jin Mama Kubura nayi wa Bintu Barka da zuwa. Bintu na ganin Sale ta sauke ajiyar zuciya sai a lokacin ta dan saki fuska. Mama Kubura ce ta dau akwatin suka nufi daki, Bintu na gaisheta, dama ita tana tantamar abinda ta gani a mafarki ace mama kubura ce zata aikata haka garesu. Da shiga dakin halin da taga mahaifiyar tata a ciki ya girgiza ta. Dan haka ta zube gabanta tana kuka tana dubata. Ita kanta Rakiya hawaye kawai take domin ganin yar tata gashi ba halin magana.  

Kubura cikin kuka take korawa Bintu bayani abinda ya faru da Rakiya tun daga haihuwar Bera har zuwa kan rashin lafiya da rashin magana. Rakiya da Ido kawai take bin Kubura da kallo, ga dai girma ya kamata amma makirci a wajenta tamkar wacce tayi degree a makarantar shaidan. Bintu kuka kawai take ta tambayi Mama Kubura wane kalar magani ake bata. Kubura tace mata babu wani magani da ake mata domin duk masu maganin gargajiya sunce basu gane kan cutar ba. Amma Malam Garzali yana aiko mata da rubutun rokon Allah ana bata. Bintu tace “Shikenan nima zan cigaba da yi mata addu’oi da tofi a ruwa ina bata tana sha”. Gaban Kubura ne ya fadi rass! Ta dubi Bintu hade da cewa “Ai inaga ba sai kinyi ba ki barshi kawai tunda dai ga na malam din tana samun sauki sosai. Kinga ke karatun nan ba nisa kikayi ba”. Dan murmushi Bintu tayi hade da cewa “Mama Kubura nayi nisa sosai fa domin na sauka yanzu harda nake izu arba’in da biyu”. Haka zalika na iya addu’oi da dama na neman tsari daga shaidanu da na neman waraka daga Allah”. Nan take kamannin Kubura ya sauya tabbas akwai babban kalubale a gabanta dole ta hallaka yarinyar nan domin kar ta kawo mata tangarda.

Kwana biyu Kubura na hakon Bintu domin ta umarci aljana Tsigitsila ta kashe Bintu, aljanar kuma ta bukaci a samo wani abu mallakin Bintu shiyasa Mama Kubura yanzu wuni take a dakin tamkar jinyar Rakiya take, Bintu tuni har ta fara kauda zargin Mama Kubura da take saboda ganin irin hidimar da take ga Rakiya.

 Abu daya Bintu take fama da shi shine kiyayyar mahaifinta garesu da kuma ummansu tabbas abun ya girgizata, domin tunda aka haifeta bata taba ganinshi a cikin irin wannan yanayi ba. Akwai wata rana da taje tana mishi magana ya koreta taki tafiya nan take ya gaure ta da mari. Abinda tunda tana karama duk rashin jinta da jan maganarta bai taba mata ba sai yanzu da take yar shekara sha shida. Ta ci kuka a lokacin da ta je dakinsu abin tausayi Rakiya na kallonta ba halin magana balle ta shaida mata cewa babanta na karkashin sihiri ne. 

Yau Kubura ta sama nasarar dauke dankwalin Bintu da ta gani a dakin. Da sauri ta fita taje ta ajiye shi a dakinta kafin dare yayi ta koma dakin su Rakiya. Tana ji Bintu ta fito tana cigiyar dankwalinta har tambayarta tayi amma tace bata gani ba. Rakiya na kallonta cike da zargi tasan cewa akwai abinda take kullawa na makirci da zatayi da dankwalin Bintu gashi ba damar ta hana balle dakatarwa. Da Magariba lokacin Bintu bata nan, Kubura ta dubi Rakiya cikin dariyar mugunta tace, “Yau zan kara jefa ki a cikin wani kuncin, ki kara da wanda kike ciki. Ina son sanar dake cewa yau zan kashe Bintu, kiyi wa Bintu kallon karshe idan ta dawo domin daga yau ba zaki kara ganinta ba, su aljana Tsigitsila zasu shanye jininta. Da fadar haka ta tashi ta fice daga dakin ta nufi dakinta. 

Bintu dake labe a bayan karfi fitowa tayi lokaci guda zufa ta keto mata. Dama ta fita da niyar zuwa gidan su kawarta Larai ne, sai ta manta da wani Hijab wanda tayi niyar bawa Larai din ta dawo dauka domin ganin duk cikin kayan Larai ba Hijab sai gyaluluwa. Ta zo daf da kofar shiga ne kunnuwanta suka jiyo mata abinda Mama Kubura ke fada. Kaf jikinta rawa yake duk adduar da ta fado bakinta yi take………………….

Afuwan idan babu natsuwa rubutu baya rubutuwa, I’m busy 👹 *TSIGITSILA* 👹

 *Shaidaniya Uwar Shaidanu*

~~~~~~~~~~~~~~~~~

          Short story

~~~~~~~~~~~~~~~~~

{Tsafi Shirka Ne, Duk Mai Yi Ya Halaka}

👨🏻‍💻 KING BOY ISAH ✍🏼

Part 10

°°°°°°°°°°

 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

 ~*NOTE* Labarin Nan Bai Faru A Zahiri Ba, Jan Kunne Ne Ga Masu Mugun Hali~

Kuyi hakuri dai I’m busy wallahi

Nafisa kanwar Rakiya da mijinta, ba yadda basuyi ba su lalashi Bintu game da batun zuwa kauye amma ta nace sai ta tafi. Kasancewar sun san halinta da naciya game da kafiya ba yadda suka iya haka suka kyaleta ta tafi. A gaggauce ta shirya ta hau mota ta nufi kauyen Dan Inna. ji take tamkar motar bata gudu domin kuwa ba karamin girgiza tayi ba da Mama Nafisa tace dama an kirata ance maman nata ba lafiya. Gani take kamar kafin ta isa gidan Kubura ta kashe mamanta da Sale. Sai bayan la’asar ta isa garin kasancewar tafiyar da ake cikin yashi ma bayan an sauka daga mota tana da nisa kafin a karasa kauyen Dan Inna. Da sallama Kubura ta fito da sauri ta tarye ta tana farin ciki. Ita kuwa Bintu bin Kubura kawai take da kallon zargi hade da kakalo yake. 

Saude ce ta fito da gudu dauke da Sale jin Mama Kubura nayi wa Bintu Barka da zuwa. Bintu na ganin Sale ta sauke ajiyar zuciya sai a lokacin ta dan saki fuska. Mama Kubura ce ta dau akwatin suka nufi daki, Bintu na gaisheta, dama ita tana tantamar abinda ta gani a mafarki ace mama kubura ce zata aikata haka garesu. Da shiga dakin halin da taga mahaifiyar tata a ciki ya girgiza ta. Dan haka ta zube gabanta tana kuka tana dubata. Ita kanta Rakiya hawaye kawai take domin ganin yar tata gashi ba halin magana.  

Kubura cikin kuka take korawa Bintu bayani abinda ya faru da Rakiya tun daga haihuwar Bera har zuwa kan rashin lafiya da rashin magana. Rakiya da Ido kawai take bin Kubura da kallo, ga dai girma ya kamata amma makirci a wajenta tamkar wacce tayi degree a makarantar shaidan. Bintu kuka kawai take ta tambayi Mama Kubura wane kalar magani ake bata. Kubura tace mata babu wani magani da ake mata domin duk masu maganin gargajiya sunce basu gane kan cutar ba. Amma Malam Garzali yana aiko mata da rubutun rokon Allah ana bata. Bintu tace “Shikenan nima zan cigaba da yi mata addu’oi da tofi a ruwa ina bata tana sha”. Gaban Kubura ne ya fadi rass! Ta dubi Bintu hade da cewa “Ai inaga ba sai kinyi ba ki barshi kawai tunda dai ga na malam din tana samun sauki sosai. Kinga ke karatun nan ba nisa kikayi ba”. Dan murmushi Bintu tayi hade da cewa “Mama Kubura nayi nisa sosai fa domin na sauka yanzu harda nake izu arba’in da biyu”. Haka zalika na iya addu’oi da dama na neman tsari daga shaidanu da na neman waraka daga Allah”. Nan take kamannin Kubura ya sauya tabbas akwai babban kalubale a gabanta dole ta hallaka yarinyar nan domin kar ta kawo mata tangarda.

Kwana biyu Kubura na hakon Bintu domin ta umarci aljana Tsigitsila ta kashe Bintu, aljanar kuma ta bukaci a samo wani abu mallakin Bintu shiyasa Mama Kubura yanzu wuni take a dakin tamkar jinyar Rakiya take, Bintu tuni har ta fara kauda zargin Mama Kubura da take saboda ganin irin hidimar da take ga Rakiya.

 Abu daya Bintu take fama da shi shine kiyayyar mahaifinta garesu da kuma ummansu tabbas abun ya girgizata, domin tunda aka haifeta bata taba ganinshi a cikin irin wannan yanayi ba. Akwai wata rana da taje tana mishi magana ya koreta taki tafiya nan take ya gaure ta da mari. Abinda tunda tana karama duk rashin jinta da jan maganarta bai taba mata ba sai yanzu da take yar shekara sha shida. Ta ci kuka a lokacin da ta je dakinsu abin tausayi Rakiya na kallonta ba halin magana balle ta shaida mata cewa babanta na karkashin sihiri ne. 

Yau Kubura ta sama nasarar dauke dankwalin Bintu da ta gani a dakin. Da sauri ta fita taje ta ajiye shi a dakinta kafin dare yayi ta koma dakin su Rakiya. Tana ji Bintu ta fito tana cigiyar dankwalinta har tambayarta tayi amma tace bata gani ba. Rakiya na kallonta cike da zargi tasan cewa akwai abinda take kullawa na makirci da zatayi da dankwalin Bintu gashi ba damar ta hana balle dakatarwa. Da Magariba lokacin Bintu bata nan, Kubura ta dubi Rakiya cikin dariyar mugunta tace, “Yau zan kara jefa ki a cikin wani kuncin, ki kara da wanda kike ciki. Ina son sanar dake cewa yau zan kashe Bintu, kiyi wa Bintu kallon karshe idan ta dawo domin daga yau ba zaki kara ganinta ba, su aljana Tsigitsila zasu shanye jininta. Da fadar haka ta tashi ta fice daga dakin ta nufi dakinta. 

Bintu dake labe a bayan karfi fitowa tayi lokaci guda zufa ta keto mata. Dama ta fita da niyar zuwa gidan su kawarta Larai ne, sai ta manta da wani Hijab wanda tayi niyar bawa Larai din ta dawo dauka domin ganin duk cikin kayan Larai ba Hijab sai gyaluluwa. Ta zo daf da kofar shiga ne kunnuwanta suka jiyo mata abinda Mama Kubura ke fada. Kaf jikinta rawa yake duk adduar da ta fado bakinta yi take………………….

Afuwan idan babu natsuwa rubutu baya rubutuwa, I’m busy

👹 *TSIGITSILA* 👹

 *Shaidaniya Uwar Shaidanu*

~~~~~~~~~~~~~~~~~

          Short story

~~~~~~~~~~~~~~~~~

{Tsafi Shirka Ne, Duk Mai Yi Ya Halaka}

👨🏻‍💻 KING BOY ISAH ✍🏼

Part 11

°°°°°°°°°°

 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*

 ~*NOTE* Labarin Nan Bai Faru A Zahiri Ba, Jan Kunne Ne Ga Masu Mugun Hali~

Cikin dakin ta karasa wajen ummanta tana kuka, “Mama dama mafarkin da nayi ashe gaskiya ne? Me yasa Mama Kubura zatayi yunkurin kashe ni? Yanzu na gane mafarkin da nayi wallahi ba Karya bane, na gane komai, Mama Kubura ce tayi miki asiri kuma tayi wa baba Asiri ya tsane ki, sannan kamar yanda nayi mafarki ta kashe Sale idan bansa ido a kanta ba zata kashe shi”. Hawaye ne suka gangaro daga idanun Rakiya ko a yanzu ta godewa Allah tunda Asirin Kubura ya fara tonuwa. “Mama ki kwantar da hankalinki kamar yadda ba zatayi bacci ba yau nima haka ba zanyi bacci ba. Kamar yanda zata kwana tana tsafi domin hallaka ni. Nima haka zan kwana ina fadawa Allah domin ya kare ni. Na tabbata cewa ita da aljannunta basu fi karfin Allah ba. Ki kwnatar da hankalinki Mama”. Tana gama fadar haka ta daukko Alqura’ni ta cigaba da karanta suratul Baqara. 

Misalin karfe biyun dare zaune take da bakaken kaya, tasa kaskon wuta a gaba, bayan tayi tsafinta na kiran aljana Tsigitsila a ban daki tana jiran bayyanarta. Bayan dan lokaci sai gashi ta bayyana nan take ta karbi dankwalin Bintu suka fara asirinsu da suka saba domin kashe Bintu Kubura na ta ambato wani suna marar dadi irin na aljannu tare da sunan Bintu da Rakiya kamar yadda Tsigitsila ta umarceta da yi.  

Bayan Aljanar ta jefa dankwalin cikin wuta hade da yanka wata bakar kaza ta kwarara jinin a ciki nan take wani irin kara marar dadin saurare ya garwaye dakin, Hade da gurnanin wasu bakaken aljannu da ji kasan ba imani. Kamar yadda aka umarce su kai tsaye suka zama hayaki suka nufi bangaren Rakiya domin kashe Bintu. Tun kafin su karasa dakin take suka saka ihu mai rikitarwa saboda wata irin wuta da ta mamaye jikinsu tana ci basu san ko daga ina take ba. Bintu dake zaune kan sallaya tana ta addu’oi saboda karar da taji sai da ta rufe kunnuwanta a zatonta lokacin mutuwar tata ne ya zo. Bata san cewa rayayyen sarki ya karbi rokonta ba kuma ya kare ta daga duk wani shedani. 

Karar na lafawa ta tashi a hankali ta leko waje. Kubura dake gaban kasko wani irin zafi taji a karjinta tamkar ana soya zuciyarta nan take ta kama aman jini. Aljana Tsigitsila ma ihu mai rikitarwa ta kurma yayin da jini ya fara kwararo mata ta baki ta hanci. “Ina!! Ina!! Karya ne yarinya baki isa kija dani ba, tabbas zanyi maganinki”. Aljana Tsigitsila ce ke fadar haka cikin galabaita. Kubura ma da tuni tayi sanyi saboda wahalar da taji ido kawai take bin Aljanar da shi tana kallonta domin jin abinda zata ce. “Me ya faru uwar shaidanu? Ina fatan dai Bintu ta tafi lahira?”. Cikin bacin rai da kunar rai hade da damuwa Aljanar Tsigitsila ta fara magana da wata murya marar dadi kai daga ji kasan cewa rainta a matukar bace yake saboda yadda muryar ke fita tare da amsa kuwa duk dakin na girgiza, “Barni da ita hatsabibiyar yarinyar nan ta nemi tsari a wajen Allah daga shaidanu da ayar nan mai karfi Ayyatul Qursiyyu wanda dalilin hakan aljannun da muka tura domin kashe ta sun kone sun zama toka”. 

Wasu zafafan hawayen bakin ciki ne suka kwaranyo daga idanun Kubura, tabbas tasan cewa yarinyar nan zata iya basu matsala tunda tace tayi karatun addini domin malam Garzali ma yasha fada mata babu wani mahaluki da zai gagari aljana Tsigitsila sai wanda yayi riko da Allah da adduo’i kuma ya kasance tsarkakkake. Babban tashin hankalinta daya shine kar adduo’in Bintu suyi tasiri asirin da tayiwa Rakiya ya karye. Domin sun hada baki da malam Garzali tawada kawai yake tsiyayawa a cikin ruwa ya danyi baki sai ya aiko wa Rakiya a matsayin rubutun rokon Allah. Bayan Kubura ta fadi wa Tsigitsila abinda ke faruwa, nan take ta fashe da dariya irin ta hade da cewa “Ai in tasan wata bata san wata ba, muna da hanya daya da zamu hana addu’arta tayi asiri ga mahaifiyarta. Hanyar kuwa itace dole ki rika lalata tsarkin ruwan gidan nan ta hanyar zuba fitsari a ciki. Domin mu aikinmu da rashin tsarki yake tafiya. Addua kuma bata amsuwa sai daga tsarkakakke

Ta kareshe maganar hade da wata gigitacciyar dariya. Tabbas zuciyar Kubura ta kekashe haka zalika idanunta sun rufe bata ganin komai a gabanta, ita burinta daya shine taga ta kai Kubura da iyalanta makabarta. In ba don fitsarin da shaidan yayi mata ta kangare ba, yanayin halittar aljana Tsigitsila da irin maganarta dake fitowa ba alamun dadi, hade da dariyar aljanar sun isa su tsorata mutum har ya saki fitsari a wando. Amma Kubura ko gizau bata yi saboda zuciyarta a kekashe take tamkar dutse babu imani a ciki. Ita kanta ba karamin farin ciki tayi ba da jin irin mafitar da uwar shaidanu ta kawo mata wanda a nan take tsakar daren tayi fitsari a kofi bayan jikinta ya dan warware cikin sanda ta nufi bangaren su Rakiya ta zuba fitsarin a cikin randunan ruwansu…………………………

In na sama dama zan karo wani

👹 *TSIGITSILA* 👹

 *Shaidaniya Uwar Shaidanu*

~~~~~~~~~~~~~~~~~

          Short story

~~~~~~~~~~~~~~~~~

{Tsafi Shirka Ne, Duk Mai Yi Ya Halaka}

👨🏻‍💻 KING BOY ISAH ✍🏼

Part 12

°°°°°°°°°°

 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

 ~*NOTE* Labarin Nan Bai Faru A Zahiri Ba, Jan Kunne Ne Ga Masu Mugun Hali~

Bintu dake zaune kan sallaya tana jin motsi ta leka a hankali ta taga, a dai-dai lokacin ta ga Mama Kubura na zuba wani abu a cikin ruwansu. Bayan ta gama ta tafi Bintu ta fito tayi addu’a sannan ta malalar da ruwan a kasa baki daya. Mamaki take sosai a ranta yadda Mama Kubura ta zama Shaidaniyar gaske, lalai yanzu ta tabbatar da cewa shiru-shiru ba shine Imani ba, haka zalika ba ko wanne masoyi ke soyayya dan Allah ba. Idan ta tuna irin aminci da yarda dake tsakanin mamarta da Mama Kubura duk a kauyenma kwatancensu ake irin zaman lafiyar da suke tamkar ya da kanwa ba kishiya da kishiya ba. Amma yanzu ta rikide ta zama muguwa tana neman rayuwarsu ta hanyar sihiri. 

Gari na wayewa Bintu tasa hijab ta bi bayan babanta ganin ya fita nan ta tare shi a kofar gida yana zaginta da kyararta ita kuma tana bashi hakuri da kyar ya tsaya ya saurareta ta. Saida ta gama fada mai duk abinda ke faruwa tamkar abun arziki bayan ya gama saurara ya dauke ta da mari. Nan take kuma ya hauta da fada ta inda yake hawa ba ta nan yake sauka ba. Wai ai duk mamansu ke daure musu gindi to zaiyi maganinta. A cewarsa Rakiya ce ta shiryowa Kubura wannan sharrin haka. Nan dai ya kara gaba yana fada, Bintu kuwa kai tsaye ta wuce gidan Malam Garzali ta kuwa yi sa’a ta same shi a kofar gida tana kuka na ta kwashe duk abinda ke faruwa ta fadawa Malam Garzali. Yana mamaki hade da jijiga kai sai kace na Allah. A zahiri ya bayyana mamaki tsantsa kamar da gaske yayin da a badini kuma babu abinda yake bashi mamaki kamar yadda Bintu tasan dukkan kule-kulen Kubura. A ranshi yayi niyar dole su kawar da yarinyar nan in ba haka ba shi kanshi asirinshi yana iya tonuwa. Kuma ya tabbata idan mutanen garin suka ji irin ta’assar da ya aikata zasu iya daukan mummunan mataki a kanshi zama su iya kasheshi. 

Nan dai ya fadi wa Bintu maganganu masu dadi hade da yi mata alkawarin karya sihirin, daga karshe ya bata wani turare wanda yace ta hayakawa mahaifiyar tata shi da daddare. Ta karba game da yi mishi godiya ta tashi kai tsaye ta nufin gidansu Hajja Kulu ta fada musu dukkan abun dake faruwa a tunaninta ba zasu amince ba, bisa mamaki sai ji tayi sunce biri yayi kama da mutum su kansu sun san cewa aikin bak’in tsafi ne ace mutum ya haifi bera. Nan take Malam Audu mahaifin Rakiya ya tashi a fusace yana huce da nufin zai kai karar Kubura wajen mai gari domin a tursasata ta karya sihirin da tayiwa Rakiya. Bintu tace “Ba haka za’ayi ba domin har yanzu bamu da kwakwarar hujja, idan bamu da hujja kuma babu wanda zai yarda da zancenmu dan haka yanzu ba zamu tunkari kowa da maganar ba. Nama je wajen Malam Garzali na fada mishi komai amma sai ya bani wannan turaren hayakin yace in turarawa Mama da daddare”. Nan dai cike da jimami da kyar suka hakuri ita kanta Hajja Kulu ba karamin kaduwa tayi ba duk da kasancewar ba ita ta haifi Rakiya ba amma ta dauke ta tamkar yar cikinta.

Dare yayi misalin karfe tara Bintu ta fita makwabta domin debo garwashin wuta da zatayi turare wa mahaifiyarta kamar yadda malam Garzali yace tayi. Tana fitowa daga gidan ta hangi Kubura ta fito daga gidan da sauri ta nufi wani waje. Dan haka itama ta ajiye kaskon tabi bayanta. Kubura bata zame ko ina ba sai gidan Malam Garzali, Bintu har zata koma kuma sai tayi tunanin dalilin da zai kai Kubura Gidan Malam Garzali a wannan lokacin. Saboda haka ta yanke shawarar shiga domin samo amsar tambayarta. A bakin window ta tsaya tana jinsu, ba karamin kaduwa tayi ba a lokacin da ta fahimci cewa Malam Garzali shine malami Ko kuma tace bokan Kubura. Kuma ba don komai ya kira Kubura ba sai dan ya gargadi Kubura a kan Bintu. Ita kanta Kubura ba karamin mamaki tayi ba a lokacin da taji cewa gaba daya duk abinda ta aikata Bintu na sane. Don haka ta nema Malam Garzali yaji da lamarin dole su hallaka Bintu. Shi kuma yace mata a iya binciken da yayi idan ana so a kashe Bintu ta hanyar sihiri dole a rabata da tsarki. Domin bakakken aljanun da zasuyi aikin ba zasu iya kusantar tsarkakken Mutum ba. 

Nan Kubura ta kwashe da dariya take fada mai ai tuni ta magance wannan bangaren domin ta zuba fitsari a cikin ruwansu Rakiya saboda haka yanzu ta tabbatar Bintu bata da tsarki, ko ba komai dai tasan cewa ruwa tsarkakkakke kadai ke iya tsarkake mutum.

Malam Garzali yaji dadin hakan dan haka yace gobe da daddare Kubura ta taho mai da bakaken kaji guda uku da farin kyalle yadi biyar ta hado mishi da kitsen saniya. Baya bukatar komai bayan wannan sai sunan Bintu da na mahaifiyarta da na mahaifin mahaifiyarta akwai kullen da zaiyi da rubutu ya ba aljannu kyautar yadi da sadaukarwar kajin nan ya umarci Kubura ta saka bakaken kaya tare zasu je gidan tururuwa su binne layar da ya hada tare da karanto sunan aljannun ya tabbatar mata da cewa idan sukayi haka karshen rayuwar Bintu ya zo. 

Rasss! Gabanta ya fadi bata taba tunanin mutum zai iya aikata irin wannan sihiri ba tare da tsoro ba yayi aiki da aljannu wai domin kawai ya kashe wani, sai gashi taji mutane biyu da bata taba tsammani ba, tabbas tayi matukar kaduwa idan da wani zai fada mata cewa Malam Garzali zai iya aikata sihiri domin kashe mutum zata karyata. A hankali Bintu ta fito daga gidan hankalinta a tashe bata zame ko ina ba sai gidan kakanta Malam Audu baya nan ma Hajja Kulu tasa akayi sauri aka kirashi domin ganin Bintu a kideme. Nan ta kwashe duk abinda ya faru ta fada musu. Su kansu da farko sun so su karyata zancen amma sai Bintu tace su taso suje domin ta tabbatar Kubura bata kai ga Fitowa ba. Haka kuwa akayi suka kwasa suka nufi gidan Malam Garzali suka sama waje suka labe. Sun dan dade a wajen suna lekawa domin ganin Kubura ta fito amma sukaji shiru kasancewar gidan ba cikin gari bane sosai har sun fara tunanin karya Bintu ta zuga musu, sai gani sukayi mace ta fito tana waige-waige alamun marar gaskiya nan take su kuma suka kara labewa. Bayan tayi nisa suka bita a baya a hankali bata zame ko ina ba sai gidan Iro. Innalillahi kawai suke fada tabbas yanzu sun yarda da dukkan abinda Bintu ta fada. Sunyi niyar nufar Iro da maganar Amma Bintu ta dakatar da su a cewarta yana karkashin sihiri ba yadda za’ayi ya fahimta. 

Malam Audu yace tunda haka ne kafin komai ya faru dole suje wajen mai gari Bintu ta fada mai komai domin a san matakin da za’a dauka. Haka kuwa akayi sunci sa’a suka iske mai gari su biyu ne kacal a kofar gidan, daga shi sai abokinsa. Bayan sun gaishe shi Malam Audu ya fadi abunda ya kawo su sannan Bintu ta dora mai da sauran duk abubuwan da taji su Malam Garzali na kullawa. Shi kanshi mai garin yayi matukar girgiza sai dai sanin halin Malam Audu yasan ba zai yi wasa da magana irin wannan ba. Don haka mai gari da abokinsa malam Idi suma ba karamin kaduwa sukayi ba ace mutum irin wannan yana ja musu sallah. Don haka in dai abinda aka fada ya tabbata dole su dau mataki mai tsauri a kanshi. 

Nan dai suka tsara yadda zasuyi goben domin tabbatar da gaskiya, mai gari yace zai gayyato matasa kamar guda biyar wanda zasu sa ido a kan gidan malam din a haka aka rabu kowa na saka da warwara a zuciyarshi……………

👹 *TSIGITSILA* 👹

 *Shaidaniya Uwar Shaidanu*

~~~~~~~~~~~~~~~~~

          Short story

~~~~~~~~~~~~~~~~~

{Tsafi Shirka Ne, Duk Mai Yi Ya Halaka}

👨🏻‍💻 KING BOY ISAH ✍🏼

Part 13

°°°°°°°°°°

 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

 ~*NOTE* Labarin Nan Bai Faru A Zahiri Ba, Jan Kunne Ne Ga Masu Mugun Hali~

Wani bakin mutum ne cikin bakaken kaya wanda ya fi kama da aljani hannunshi rike da wata katuwar kwalba cike da wani jan abu, mutumin ya fito daga bangaren Kubura ya nufi bangaren Rakiya. Yana zuwa kofar dakin ya tsuguna yayi rami ya binne kwalbar nan take ya mike yayi dariya ya kara gaba. Bintu ce zaune gaban Rakiya hannunta rike da wani abu a cikin kwarya fari tass. Nan take ta ba Rakiya a baki tana sha ba’a fi mintuna biyar ba nan take Rakiya taji dukkan karfin jikinta ya dawo maganarta ma haka. Ta tashi zaune suka rungume juna dan farin ciki. Kubura ce ke tsala gudu a tsakar daji mai cike da duhu. Wani murugujejen aljani na biye da ita yana wangame katoton bakinshi yana kawo mata hari da niyar cinye ta. Ita kuwa sai ihu take tana cigaba da tsala gudu domin tsira da ranta. Bata ankara ba ta fada wani wakeken rami ai kuwa nan take wannan aljanin ya rufa mata baya inda ya sama sa’a ya cafko kanta da baki nan take ya gutsere kan jini ya fara malala. Firgigit ta farka tana lumfashi daya-daya. Game da kiran sunan Allah da neman tsari daga gareshi game da wannan mugun mafarki. Ta wani bangare kuma farin ciki ne ya kumeta. Tabbas tana tune da dukkan abubuwan da ta gani a mafarki. Bintu ta tabbatar da cewa kamar yanda tayi istihara ta kwnata bacci bayan ta roki Allah ya nuna mata hanyoyin karya asirin iyayenta shine Allah ya nuna mata yanzu a mafarki.

Ganin asuba tayi yasata tashi ta dauki ruwan da ta debo a makwabta ta boye domin ta sake kwarar da ruwan da Saude ta tara dan ta tabbatar da cewa Mama Kubura ta zuba najasa a ciki. Alwala tayi ta zo ta tayar da sallah adduo’i sosai tayi ta roki Allah ya tona asirin Kubura kuma ya fara sakawa iyayenta tun a nan duniya. Bayan ta gama kai tsaye waje ta fito taje wajen da babansu ke ajiye kayan nomanshi ta daukko fatanya nan take ta zo ta fara tona kofar dakin nasu. Kubura dake kwance kan gado gefen Iro cikin jin dadi da kwanciyar hankali domin tunda tayi wa Iro asiri bai kara waiwayar inda dakin Rakiya yake ba balle yaje ya kwana kullum a dakin Kubura yake kwana wanda ita kuma dama haka ne burinta. Cikin bacci ta rika jin kara tamkar ana saran kasa. Ta tashi tuni gari ya fara yin haske bama tayin sallah take ba, domin tuni aljanar ta hanata yin sallah. Bayan ta murje idonta ta fito kai tsaye bangaren Rakiya ta Nufa domin ta can take jin karar sarar kasar. Gabanta ne yayi mumunar faduwa a lokacin da ta hangi Bintu na faman tona rami wato dai inda ta binne asirin da Aljana Tsigitsila tasa tsanar Rakiya ga Iro. “Lafiya kuwa Bintu ramin me kike haka”.

Da sauri ta dago kai da bismillah sai da gabanta ya fadi. Ganin Mama Kubura ce tama rasa me zatace can dabara ta fado mata tace, wani dutse ne a wajen mutane na tuntube shine ta cire shi. Murmushi kawai Mama Kubura tayi game da cewa “Ai gwara da kika cire shi yanzu sai ki rufe wajen saboda kofar dakin duk tayi wani kala ba kyau”. “To” kawai Bintu tace ta rufe wajen cike da farin ciki domin bisa ga dukkan alamu mafarkinta bai fada mata karya ba don kallo daya zakayi wa Kubura ka gane cewa akwai wata a kasa. Bintu ta yanke shawarar barin tonewar sai Kubura ta bar wajen. Bisa mamaki sai gani tayi Kubura ta shiga dakin ta nema waje ta zaune tasa Rakiya gaba wai tana jinya. 

Murmushi kawai Bintu tayi domin ta gano dalilin Kubura tsoro take ta tafi Bintu ta tone ramin. Ranar haka suka wani a dakin Kubura taki yarda ta fita koina, so take ma Bintu ta bar gida domin taje ta kira aljana Tsigitsila taji me zai faru idan Bintu ta tone asirin

Haka kuwa suka wuni Bintu taki fita ko’ina haka itama Mama Kubura. Can wajen La’asar Ko me Kubura ta tuno oho. Murmushi ta Kalli Bintu tayi wanda yafi kama da na Mugunta, nan take ta tashi ta fice daga dakin ta nufi bangarenta. Bintu na ganin haka ta fito da sauri ta cigaba da tona ramin. Kuka taji Sale ya fashe da shi ya cigaba da kwalla ihu. Da sauri ta shiga dakin dan ganin abinda ke faruwa. Wasu bakakken abubuwa ne duk suka fito a jikin Sale sukayi tambari a jikin nashi kamar wanda ya kokone a jiki. Bintu a kideme ta nufe shi tana taba jikin nashi taji wani bala’in zafi tamkar ta taba jikin tukunya. Addu’ah ta shiga karantowa duk wacce ta fado bakinta tana tofa mishi. Shi kuma sai kara ihu yake yana mirgina a kasa ita tama kasa rike shi. Saude ce ta fado dakin da sauri ganin halin da Sale ke ciki yasa ta rugawa a guje domin kirayo Mama Kubura. Tana zuwa ta tura kyauren katakon da karfi ta fada dakin. A tsugune gindin kaskon wuta ta iske Kubura rike da wani butunbutumi tana kanga shi jikin wutar tana karanto wasu surutai. Duk da kasancewar Bintu yarinya ce amma ta ji a ranta abinda Mama Kubura ke yi ba mai kyau bane. Da sauri Kubura ta dago idanunta da sukayi jawur ta kalli Saude har sai da ta tsorata musamman da taji muryarta na tambaya me ya kawo ta dakinta. Nan dai Saude ta daddaure ta fada mata abinda ke faruwa. Kubura tace taje gata nan zuwa. Saude na fita Kubura ta jefa butunbutumin cikin wuta. Nan take ya kone wani bakin hayaki ya tashi sama. Da faruwar hakan lumfashin Sale ya dauke. Bintu ta cigaba da jijigashi tana kuka. Rakiya na kan gado kwance tana jin duk abunda ke faruwa da taji alamun Sale yayi shiru Bintu kuma ta fashe da kuka tana jijiga shi tasan cewa ya rasu dan haka hawaye kawai ta cigaba da yi.

Mama Kubura ta shigo dakin a kideme kamar da gaske…………..

👹 *TSIGITSILA* 👹

 *Shaidaniya Uwar Shaidanu*

~~~~~~~~~~~~~~~~~

          Short story

~~~~~~~~~~~~~~~~~

{Tsafi Shirka Ne, Duk Mai Yi Ya Halaka}

👨🏻‍💻 KING BOY ISAH ✍🏼

Part 14

°°°°°°°°°°

 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

 ~*NOTE* Labarin Nan Bai Faru A Zahiri Ba, Jan Kunne Ne Ga Masu Mugun Hali~

Mama Kubura ce ta shigo dakin a kideme Kamar da gaske tana ganin Sale a hannun Bintu baya lumfashi ta kwalla ihu, wanda ake kira da ihun mutuwa a karkara. Ba jimawa gidan ya cika da mata wasunsu sun dauka ma Rakiya ce ta mutu shiyasa akayi hanzarin zuwa. Nan dai akayi wa Sale Sutura kasancewar yaro ne karami ba’ayi wani gayya sosai ba. Shi kam Iro nunawa yayi kamar ma baisan abinda ake ba domin lokacin da aka fada mai mutuwar ma cewa yayi Allah yasa Rakiya da yayanta duk su mutu. Dake mutanen garin sunsan abunda ke faruwa tsakanin Iro da Rakiya da yayanta basuyi wani mamaki ba duk da kuwa kowa na mamakin irin canji da yayi na lokaci guda ya tsani Rakiya.

Bayan magariba aka kawowa Kubura sakonta na bakaken kaji guda biyu da ta saya a wajen wani mai sayarda kaji a kauyen. Duk da ana jimamin mutuwar duk abinda Kubura keyi Bintu na sa ido a kanta. Har dare yayi kowa ya watse daga gidan Bintu kuwa na tsakar gida ta kasa ta tsare so take taga fitar Kubura. Ai kuwa shiru dare yayi sosai kimanin karfe dayan dare Bintu taji motsi alamun Kubura ta taho fitowa ai kuwa tayi sauri ta kwanta a kan tabarmar kaban tamkar tana bacci. Sai da Kubura ta zo saitinta ta tsaya ta kira sunanta a hankali Bintu bata amsa ba. Rakiya tace “Hmm yarinya daga wannan baccin zaki zarce lahira ba zaki tashi ba, ai in kinsan wata baki san wata ba”. Da fadar haka tayi waje. Bintu ta tashi da sauri taje daki ta tayar da Saude tana magagin bacci ta girgizata sai da ta tabbatar ta wartsake sannan tace mata ta ruga da gudu gidan su Kaka Malam Audu tace su isketa a gidan malam Garzali kasancewar Saude Rainon kauye ko tsoron dare batayi ba ta fita a guje inda aka aiketa. Abinda bata sani ba tuni mai gari yasa matasa biyar su shiga makwabtan gidan Malan Garzali su rika leken kofar gidan da ko’ina na gidan haka kuwa akayi Bintu da taje gidan bata tarar da Malam Audu ba sai Hajja Kulu da ta kasa ta tsare. Kubura kuwa bata zame ko’ina ba sai gidan Malam

Bayan sun tarkato kayan tsafinsu suka fito domin badda kama Malam Garzali ne ya fara yin gaba daga baya sai Kubura ta bishi baya. Duk abinda suke ana kallonsu kuma mutane na biye da su a labe ciki harda Bintu. Malam Garzali Da Kubura suka ratsa daji suna ta tafiya sai da sukayi nisa sosai sannan suka karasa wani katon gidan tururwa. Malam Garzali ya jefa layar da yayi mai dauke da sunan Bintu da Rakiya a cikin ramin gidan Tururuwar. Na take ya ajiye farin yadin nan a kasa Sannan ya karbi zakarun daya bayan daya ya yanka su a saitin kan yadin jininnya jika yadin yana wasu surutai irin na tsafi. Bintu da ganin haka ta juya da gudu baya domin ta kirayo mai gari da mutanensa ta kawo su wajen su ganewa idanunsu. Har ta kusan isa gari taga zugar su Mai gari ciki harda Malam Audu bata sani ba ashe daga cikin kattin dake sa Ido a kan su Malam Garzali ne wani yaje ya kirayo su, nan suka hadu baki daya suka nufi wajen.

Mai gari manyan gari da ma talawan gari babu wanda zuciyarsa bata kadu ba bisa ganin halin da Malam ke ciki kallo daya zakayi wa abinda suke ka tabbatar da cewa tsafi suke. Sun dora wannan yadin a kan gidan tururuwar sannan suka yanke kai da kafafun kajin suka dora a kan yadin. Inda suka tsugunna a wajen hade da runtse ido suna ta karanto wasu sunaye daga ji kansan cewa na aljannu ne. Babu abinda yayi wa mai gari da mutanen gari ciwo face ganin baban malaminsu wato Malam Garzali wanda yake jansu sallah a cikin irin wannan hali. Dan haka ba tare da bata lokaci ba wasu fusatattun mutane suka afkawa Malam Da Kubura da duka da naushi ta koina. Cikin kankanin lokaci suka saba musu kamanni.

Sun kusan kashe su da kyar mai gari ya dakatar da matasan nan take aka sa igiya akayiwa malam da Kubura daurin huhun goro aka wace da su aka jefasu a daki aka kulle kafin safiya. Da faruwar haka Kubura ta runtse ido tana kiran aljana Tsigitsila……………….

👹 *TSIGITSILA* 👹

 *Shaidaniya Uwar Shaidanu*

~~~~~~~~~~~~~~~~~

          Short story

~~~~~~~~~~~~~~~~~

{Tsafi Shirka Ne, Duk Mai Yi Ya Halaka}

👨🏻‍💻 KING BOY ISAH ✍🏼

Part 15 KARSHE (THE END)

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

 ~*NOTE* Labarin Nan Bai Faru A Zahiri Ba, Jan Kunne Ne Ga Masu Mugun Hali~ 

Ta dade tana kiran aljanar Amma shiru bata bayyana ba. Malam Garzali ya dubeta yayi murmushi hade da cewa “Na fa manta ban fada miki ba dama a duk lokacin da kika shiga wata matsala ko asirinki ya tonu to fa Aljana Tsigitsila zata guje ki haka zalika idan aka karya sihirin da kika aikata ke da Aljana Tsigitsila dole akwai mummunan abu da zai biyo baya. Ki sani Kubura yau fa karya ta kare bamu da matsera na tabbata idan har mutanen nan basu kashe mu ba to Aljannu zasu haukata mu saboda haka ne ka’idar aiki da bakakken shaidanu da bakin tsafi. A duk lokacin da asirin mutum ya tonu to tabbas abubuwa uku zasu same shi. Na farko kunyar duniya da ta lahira. Na biyu azabar duniya da ta lahira. Na uku kyama da tsana da tsinuwa daga wajen Allah da mala’ikunsa da kuma bayin Allah na kwarai haka zalika mutanen gari. Yanzu muna cikin wannan hali lokacin nadama ko tuba ya kure mana. Mun aikata abubuwa da yawa ba tare da asirinmu ya tonu ba. Dama kamar haka Allah yake ba mutum dama ya kyale ka kaita aikata ta’asarka tamkar baya sane da kai a rana daya sai kaga asirinka ya tonu mutane sunsan ko kai waye ne. Kinga mu biyun nan babu wanda ya hallakar damu face mu da kanmu saboda kawai burika irin na rayuwar duniya”.

“Ke nasan cewa ba wani abu ya hallakar dake ba face bakin kishi irin na rashin hankali. Saboda namiji wani lokacin idanunku rufewa suke zuciyarku kuma ta kekashe wanda duk wannan rashin tunani ne da kuma rashin lissafi. Wasunku su kanyi wa kishiyoyinsu asiri su haukace, wasu kuma kurciya suke yi wa kishiyoyin nasu domin su shiga duniya. Ansha kawo min aikin kashe kishiya kuma na aikata, Wasu kuwa wuka suke dauka su kashe kishiyar ko kuma yayanta. Karshe su kare a gidan yari yayin da ita kuma kishiyar da suka kashe tayi shahada domin dukkan zunubanta ke za’a kwashe a dorawa. Abin takaici kuma mijin da kika kashe yar uwarki domin shi idan har ya gano ke kika kashe mai mata ba zai sake zaman aure dake ba. Ke bama shi ba ke da aure a duniyar nan har abada. Bama aure ba ke da zaman lafiya da kwanciyar hankali sai dai kiga anayi idan ma ba’a yanke miki hukuncin kisa kenan ba kin tafi lahira domin tarar da azabar Allah da ya tanadar miki”. “Dakata malam, shin kana so ka nuna min kai na Allah ne? Kai ko kunya baka ji bama? Sau nawa muna aikata zina dakai bayan kasan ina da aure bayan zina sau nawa ina yin tsirara kana min rubutu a jikina. Ko ka manta har laya ka taba saka min a al’aura. Duk wannan munanan ayyukan da ka aikata har kana da bakin yi min wa’azi? To ni bari kaji in fada maka. A munanan ayyukan da na aikata nasan cewa bani da rabo a lahira wuta zan shiga. Duk ban damu da wannan ba burina daya in shafe zuri’ar Rakiya da ita kanta daga doron duniya. Yanzu haka bakin cikina daya shine asirina ya tonu ban kashe Bintu Da Saude ba, nasan cewa ita Rakiya tata ta kare domin kuwa a haka zata tafi lahari, ba zata taba tashi ba na tabbata”.

Murmushin takaici Malam Garzali yayi kana yace “Kubura lalai kinyi nisa duk a cikin shedanun matan ma ban taba ganin kamarki ba. Ki sani ni yanzu nayi nadama duk da kuwa nasan nadamata bata da amfani ke kuwa babu alamar nadama a tattare dake. Ni na fada harkar bokanci da tsafe-tsafe ne sanadiyar rashin godiyar Allah. Da kuma karatu da nayi wanda babu tsoron Allah a ciki. Ina wannan harkar tsafin ne domin in tara kudi ta hanyar aljannu amma tun daga sanda na fara na gwada sihiri da tsafi kala daban-daban na mallakar aljani da zai rika kwaso mun kudi ko satowa ko dai daukko zinari ko kudade daga wasu bankunan amma ina har yau banyi dace ba, aljannu makaryata ne kamar yadda Annabi S.A.W ya fada. Domin nasha cikawa aljannu alkawuransu domin su cika mun burina na yin kudi amma daga karshe sai su yaudare ni su gudu su barni bayan na biya musu bukatunsu. Ko shekarun baya abinda baki sani ba, ba dani kike saduwa ba da wani aljani wanda yayi alkawarin bani kudi kike saduwa”.  

Duk da Kubura na daure da igiya hannu da kafa sai da ta yunkura da kyar ta tashi nan take ta fashe da kuka ta hau malam Garzali da zagi da fadin mai munanan kalamai wai ya cuceta. A haka har gari ya waye. Tuni labari ya zagaye kauyen har da wasu kauyuka makwabtansu. Misalin karfe goma aka fiddo Malan Garzali waje daga shi sai gajeran wando aka daure shi a gindin bishiya. Haka itama Kubura daga ita sai zani aka daureta a bishiyar dake kusa da ta malam Garzali mutane na ta kallonsu suna tsine musu albarka musamman da aka fadi abinda suka aikata. Mutane suka fusata kwarai da gaske, nan take mutane suka fara yi musu ruwan duwatsu. Sai da mutane sukayi musu jina-jina da duwatsu dakyar aka dakatar da mutane karsu kashe su.

Bintu kuwa a daren ma batayi bacci ba. Taje ta tone kofar dakin mamar tasu inda ta tono kwalbar sai dai ta rasa yadda zatayi da ita ta karya sihirin da akayi wa baban nata, duk da haka tayi matukar farin ciki hade da godewa Allah domin tasan cewa mafarkin nan da tayi gaskiya ne kuma Allah ne ya nuna mata kamar yadda ta roka. Abu daya da ta kasa ganewa shine farin abun da ta ba mahaifiyarta Rakiya a cikin kwarya wanda tasha ta warke. A iya nazarinta dai nono ne amma kuma ta ba mamar tata nono tun dazun shiru dan haka ta zauna gaban Gado tana kuka. Zuwa can wani tunanin ya fado mata dan haka da sauri ta tashi ta debo ruwa a kwarya ta zo ta tofa ayatul Qursiyyu falaqi da nasi ayoyi uku na karshen suratul Baqara da la’ilafi nan take tayi bismillah ta ba mahaifiyar tata ruwan addu’ar amma shiru. Kuka ta kara fashewa da shi a haka har bacci yayi awon gaba da ita. Da safe Saude garin daukko wani abu a kan taga ta bige kwalbar asirin da Bintu ta ajiye ai kuwa kwalbar ta fado ta fashe. Nan take wani bakin hayaki game da dariya marar dadin saurare suka fito daga ciki. Saude ihu ta kwalla ta ruga a guje cikin dakin ta makalkale Bintu tana fada mata abinda ke faruwa. 

Itama Bintun a tsorace ta leko waje ta duba amma abun mamaki kwalbar ta fashe kuma gaba daya bakin abun dake cikinta ya fita. Iro dake kwance a daki yana bacci kanshi ne ya fara wani irin ciwo nan take ya rike kan tamkar zai fashe tuni ya fara attishawa. Jibi ya karyo mai nan take kan nashi ya daina ciwo. Dube-dube ya farayi ganinshi a daki, tunaninshi ya dawo nan dai ya tuna abinda ya faru ranar da ya dawo daga neman kudi yama tuna dalilin dawowar tashi Rakiya ce ba lafiya dan haka ba karamin mamaki yayi ba ganinshi a kwance a dakin Kubura. Da sauri ya tashi ya fito waje yana kiran Kubura amma shiru. Ya nufi bangaren Rakiya. Saude na ganinshi ta ruga da gudu cikin daki yana kiran sunanta amma bata tsaya ba. Ciki dakin ya bita cike da mamaki sai ma gani yayi ta lafe can bayan gado tana bashi hakuri karya doketa. Bintu na ganinshi ta durkusa kasa ta gaisheshi. Kallonta yayi itama da alamun tsoronshi a tare da ita. Gaba daya abun ma mamaki ya bashi, bayan ya amsa gaisuwar ya tambayi Bintu yaushe ta zo. Ita kanta mamaki abin ya bata jin baban nata ya amsa kuma ya nufi wajen Rakiya yana dubata. Nan dai ta fahimci cewa asirin ya karye yanzu babanta ya dawo cikin hayyacinta. Dan haka cikin farin ciki take sanadar da shi ai ta dade. Kubura ya tambaya Bintu cikin tsoro ta fadi masa duk abubuwan dake faruwa har da batun kashe Sale da mafarkinta da kuma karya sihirinshi da ta tono yanzu. 

Sam bai aminta da zancenta ba dan haka ta ce idan bai yarda ba su wuce gidan mai gari domin Kubura na can a daure. Iro cikin tashin hankali suka fita suka bar Rakiya kwance tana bacci Saude ta zauna tana kula da ita. Bayan sun isa gidan mai gari ba karamin mamaki Iro yayi ba. Da ganin halin da Kubura ke ciki. Jikinta duk ya baci da jini an kukunbura mata fuska. Mai gari da Malam Audu ne suka kara yi mai bayanin duk abubuwan da suka faru yaji babu maraba da abinda Bintu ta fada mai. Hawaye kawai ya fara kwararo tabbas ya kadu matuka da abinda Kubura ta aikata. 

Karasawa yayi wajenta ya durkusa a inda take zaune cikin jini ita kanta tayi mamakin ganin ya dawo hayyacinsa. “Kubura kin bani mamaki, yaushe kika koma haka? Me Rakiya tayi miki da zaki saka mata da irin wannan? Kin manta irin kaunar dake tsakaninki da Rakiya?”. Cikin tsawa ta dago kai ta kalle shi hade da cewa. “Dallah malam yi mun shiru babu abinda zaka ce mun. Akwai azzalimin da ya wuce kai, saboda bana haihuwa sai kayi min kishiya? to ka sani ban taba nunawa Rakiya soyayya dan Allah ba duk zaman da mukayi tsanarta da kiyayyarta na cikin zuciyata yanzu na tashi bayyanawa kuma nayi nasara domin kuwa Rakiya ba zata taba tashi ba. Na zubar mata da ciki ba sau daya ba kuma na dakar mata da haihuwa haka zalika na kashe mata ‘ya’ya biyu duk ta hanyar asiri yanzu kuma gashi zan kasheta saboda haka ko yanzu kuka kashe ni banyi asara ba. Bakin cikina daya ban kashe Bintu Da Saude ba”.  

Bakin ciki da takaici ne ya kamashi, nan dai ya fara lalashinta a kan ta fada mai makarin asirin da tayi wa Rakiya zai sa a saketa. Amma ina dariya ma ta cigaba da yi cikin farin ciki tana fadin cewa ba zata taba fada ba sai dai su kashe ta wai shi din ma sa’a yaci da ba zai taba dawowa dai-dai ba. Dariyar da take ba karamin fusata Iro tayi ba dan haka ya nemi Mai gari kafin a kashe Kubura ayi mata azaba mai radadi wacce zata sa dole ta fadi makarin asirin da ta tayiwa Rakiya. Ai kuwa mai gari ya umarci wasu katti nan suka shiga jifgar Malam Garzali da Kubura domin su fadi makarin asirin amma Kubura dan tsabar taurin rai a hakan ma dariya take duk da irin azabar da take sha. Ita burinta ya cika tunda ta hallaka Rakiya. Shi dai Malam Garzali rantsuwa yake yana karawa yana fadar cewa baisan makarin ba Aljana Tsigitsila ce ta sani. Amma hakan bai sa an sarara mishi ba. Anyi musu azaba kala-kala. Har karfe aka rika sawa a wuta ana mannawa Kubura amma taki fada ko dake ita kanta bata sani ba domin aljana Tsigitsila ta ce mata wannan asirin baya da makari, abinda basu sani ba kuwa babu abinda ya fi karfin ayar Allah a duniya. Malam da Kubura sunyi suma ya kai biyar biyar saboda irin azabar da akeyi musu. Har wanka da ruwan barkono anyi musu ta kai ga sunyi likis. Amma duk da haka Kubura idan ta dan farfado dariyar farin ciki take. 

Lokaci daya akaga Kubura ta daina dariya tana kallon wani bangare cikin kaduwa da tsinkewar gaba. Nan take suma mutane suka bi wajen da kallo. Rakiya suka gani ta ratso cikin filin ita da Saude tamkar ba itace tayi ciwo ba, ashe ruwan addu’ar da Bintu ta bata cikin dare Allah ya bata lafiya. Bintu na ganinta ta ruga da gudu ta rungume mamar tata hade da fashewa da kuka da dariya na farin ciki. Iro ma ya karasa wajen cikin farin ciki. Mutane kowa ya cika da farin ciki nan take Bintu taja hannun Rakiya zuwa gaban Kubura wacce ke lumfashi daya-daya tana bin Rakiya da Kallo. Bintu ta fara da cewa “Kubura bude idonki da kyau ki kalleta Mamana ce da kike ikirarin cewa ba zata taba tashi ba, kin manta da cewa ba aljannu ke daukar rai ko kuma bada rai ba Allah ne. To ina so ki san cewa dukkan wani asiri da kikayi ya cutar da mahaifiyata har wanda ma kika kashe asirinki ba shine ya kashe su ba dama kwanansu ne ya kare ke kuma kece sanadi dan haka alhakin mutuwarsu ya rataya a wuyanki. A cikin suratul Baqara Allah ya sanar da mu cewa babu wani mai asiri ko sihiri da zaiyi sihiri ya cutar da wani bawan Allah face dai da izinin Allah. 

Shin yanzu ina Aljannun dake taimaka miki a harkar sihirin? Na tabbata sun gudu sun barki dama haka take kasancewa domin shaidanun aljannu makaryata ne da bakakken ruhanai da ifiritai wanda bokaye da ku masu sihiri kuke yi wa Allah shirka saboda su. Su ba komai bane face wasu shedanu dake kaiku su baro domin su dama halakakku ne wanda suke zaman jiran azabar Allah kuma mai isowa garesu ce nan bada jimawa ba tare daku masu yi wa Allah shirka”.

Jikin Kubura ne ya fara kunbura nan take duk sassan jikinta suka daina aiki hatta kuwa bakinta. Wasu bakakken abubuwa masu kamar maruru duk suka fito mata a jikin yayin da cikinta ya fara kunbura yana girma. Babu abinda ya ba mutane tsoro face ganin da sukayi cikin nata na motsi tamkar wani abu ne a ciki yana son fasa cikin ya fito. Nan take Rakiya da Bintu sukayi baya ita kuwa Kubura Allah kadai yasan bala’in da take ji a cikin nata tamkar ana tsaga cikin cikinta da yayan hanjinta gashi ba damar ihu sai matse fuska take alamun tana jin jiki. Cikin nata ne ya barke yayin da jini yayi feshi da faruwar haka ta kwalla ihu nan take idanunta suka firfito waje lumfashinta ya dauke. Wani bakin hayaki ne ya bayyana a wajen cikin dan lokaci kuma ya bace. Bayan faruwar haka Malam Garzali ya bayyana musu zinar da suka aikata da aljanine ciki ya shiga wai yanzu shine ya zo ya dauki jaririnshi dake cikin Kubura dama irin wannan ranar yake jira. A karshe dai aka tattara gawar Kubura aka kai daji aka banka mata wuta ta kone ta zama toka shi kuwa malam baya an yanke mai hannuwa aka kore shi daga garin yana tafiya a cikin daji aljannu suka haukata shi.

Bayan kwana biyu Rakiya ta warke garau haka shima Iro suka cigaba da zaman su lafiya. Mai gari kuma yasa aka nemo wani malami mai tsoron Allah ya cigaba da koyar da mutanen kauyen karatun addini kuma yana jan sallah hade da kara wayar da kan mutane su guji shirka kuma su rika yarda da kaddarar da duk Allah ya jarabce su da ita

TAMMAT BI HAMDULILLAH 

Duka-duka a nan na kawo karshen wannan dan gajeran labarin. Ina fatan Allah ya yafe mun kurakuren da na rubuta a ciki. Allah kuma yasa rubutun nan ya zama izina ga masu aikata shirka ga Allah da mata masu zuwa wajen bokaye saboda rashin yarda da kaddarar da Allah ya aiko musu musamman a kan kishiyoyi, tabbas karshensu ba zaiyi kyau ba. Allah yasa darussan dake ciki su amfane mu. Aljani, ruhani, ifiritu, boka ko malamin tsubbu basu isa su cutar da kai ba sai idan Allah ya nufa. Haka zalika boka ko malam basu isa su baka lafiya ba, Allah shi ke bada Lafiya. Saboda haka yan uwa Addu’a itace maganin komai. In baku manta ba Annabi ya fada mana cewa Addu’a itace makamin mumini. Saboda haka mu daina wasa da adduo’i haka zalika zama da tsarki. Shiga bandaki ba addu’a, ga mata barin kai ba dankwali. Allah ya ka tsarkake mana zukatanmu amin

Kingboy Isah ke cewa a huta lafiya. Allah ya karbi ibadunmu baki daya a cikin wannan wata mai alfarma amin.

Whatsapp 08096831009

Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top