AWARA DA KWAI
![]() |
YADDA AKEYIN AWARE DA KWAI |
waken suya
kwai
attaruhu
albasa
mai
maggi
gishiri
alimun ko Dan tsami
man ja kadan
YADDA ZAKIYI SHINE
Da farko zaki gyara waken suya se ki wanke ki rege ki kai inji a markado idan aka kawo se kisa manja kadan saboda yana hana kullin lalacewa daga nan se ki tace se ki dora idan kin dora a wuta. Se ki jika alimun din a Dan karamin abu idan ya tafaso se kisa alimun dinki zaki ga ya dunkule idan ya dundunkule yayi se ki sauke ki tace idan kika tace se ki fasa kwai a ciki kisa maggi da gishiri da jajjagaggen attaruhunki da albasa amma kisa kwan yaji sosai in ba haka ba baza yayi kyau sosai ba se ki kulle a Leda ki dora a wuta ya Dan dahu idan ya dahu se ki yayyanka ta se kisa a kwai se ki soya.
Agajahub publishers