SAMOSA
Abubuwan hadawa
Fulawa (flour)
Kwai
Nama
Maggi
Onga
Kori (Curry)
Gishiri
Man gyada
Attarugu
Albasa
Karas (carrot)
Baking powder
Yadda ake hadawa
Da farko zaki wanke namanki ki tafasa shi da albasa da maggi da gishiri da dan korinki. Ki yi shi tamkar danbun nama.
Sai ki goga karas din ki, ki kuma soya shi
Sai ki zuba fulawarki a roba ki saka baking powder da dan gishiri ki kwaba. Ki murza ta murzu sosai ta yi fadi.
Sai ki rika yankawa kina zuba namanki da karas kina nadewa kamar dan kwali
Sai ki dora mangyadarki a wuta ya yi zafi
Idan yayi zafi sai ki dinga jefa nadadden samosanki kina kisoyashi
Ana baiwa maigida ya yaje dashi office, ko kuwa yara dan zuwa makaranta. Sannan za a iya duba: Yadda ake sinasir da yadda ake miyar wake da makamantansu.
SPRING ROLLS
Abubuwan hadawa
Filawa
Nikakken nama
Kabeji
Karas
Albasa
Kwai
Magi
Gishiri
Curry
Brush
Man gyada
Yadda ake hadawa
Da farko, Uwargida zaki wanke kabejinki ki yanka da albasa da karas sanan ki soyasu da mai cokali daya, kuma suyan ya zamana sama-sama.
Sannan sai ki zuba nikakken nama, da maggi, da gishiri da curry. Jim kadan sai ki sauke daga kan wuta.
Bayan nan, sai ki hada filawa, kwai, maggi, gishiri da ruwa ki kwaba yayi kamar kaurin wainar filawa.
Sai kuma ki shafa mai a nonstick, sannan ki shafa filawarki da brush. Idan ya yi, za ki ga gefen ya dago sai ki cire a gefe ki tara.
Idan kin gama sai ki dinga dauka kina zuba hadin kabejinki kina nadewa kamar tabarma.
Haka zaki yi tayi har ki gama. Idan kin gama sai ki sa kaskon suya a wuta ki sa manki, idan ya yi zafi sai ki soya.
Idan kin gama soyawa sai ki kwashe ki sawa maigida ya je office dashi ko kuwa yara dan tafiya makaranta.
Fantastic