DANBUN NAMAN KAZA
Ingredients
Kaza
Vegetable oil
Spices
Garlic
Attarugu
Onions
YADDA ZA A HADA
Dafarko zaki wanke kazarki sai ki dorata a wuta tare sa albasa garlic da Sauran spices dinki ki barta ta dahu tayi luguf idan ta nuna sai ki sauke ki ciccire kashin jikinta tare da duk Wani kitse kitse ki zuba attarugun ki da albasa ki a turmi ki daka su sai ki zuba Wannan kazar taki Kiyi ta dakawa har yayi laushi daga nan sai ki zuba a frying pan da Dan mangyda kiyita gaurayawa kina Dan zuba mai kadan kadan har ya nuna idan kisa maggi da Dan curry kiyita juyawa sai ya sayo shikenan
Aci Dadi lafia
Agajahub publishers