YADDA AKEYIN LEMUN ABARBA DA MANGWARO, LEMUN KWAKWA DA MADARA

 LEMON ABARBA DA MANGORO

Abubuwan hadawa

Mangoro

Abarba

Sugar

Ruwa

Yadda ake hadawa

Ki samo mangoro da abarba ki bare ki yanka su kanana.

Sai ki dauko blender ki zuba su a ciki, ki sa sugar da ruwa ki nika su.

In sun niku sai ki tace ki sa a fridge in ya yi sanyi a sha ko ki sa kankara sai a sha.

 

LEMON KWAKWA DA MADARA

Abubuwan hadawa

Kwakwa 3

Madara 2

Suga

Filebo (flavor coconut)

Yadda ake hadawa

Da farko uwargida za ki fasa kwakwarki ki kankare bayanta ki wanke sai ki yanka.

Ki sa a blender ki markada sai ki tace ki sa madara da suga da filebo.

Sai ki juya sosai sai ki saka kankara ko ki sa a firinji ya yi sanyi.Shikenan sai sha idan ya yi sanyi.

A sha dadi lafiya.

 

LEMON CITTA DA LEMON TSAMI

Abubuwan hadawa

Lemun tsami 6

Citta 3

Suga

Abin kanshi (filabo)

Yadda ake hadawa

Da farko za ki wanke lemunki sai ki yanka ki matse ruwan a roba mai kyau.

Sai ki wanke citta ki goga da abin goga kubewa sai ki sa ruwa.

Sai ki tace da rariya mai laushi ki hada da lemon tsaminki

Sannan ki zuba sugar da abin kamshi ki juyashi sosai .

Sai ki sa a jug ki sa kankara ko kisa a firinji.

 

Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top