DARASIN MATA NA FARKO: Abubuwan da ke hana mata jindadin gamsuwa ko sha’awa a rayuwar Aure

Yawancin mata ba su san dadin aure ba. ’Yan uwa, ko kin san dalilin da ya sa ba ki da sha’awa kuma idan mijinki ya kusan ce ki ba kya jin dadi? Sai ki duba ki gani mai yiwuwa wadannan bayanai za su iya ba ku haske a kan matsalar da ke damunku, domin neman mafita.

Duk da ya ke an fi ganin cewa, mata sun fi maza yawan sha’awa da son jima’i a yanayin halittarsu a kan maza, ba abin mamaki ba ne a sami akasin haka wani lokacin cewa, akwai mata da yawa wadanda ba su da sha’awa ko kwadayin jima’I, saboda wasu dalilai na lafiya. Hakan na faruwa inda za ka sami mace na gudun kwanciyar aure ko ba ta damu da a yi kwanciyar ko kada a yi ba (duk daya ne a gurinta), saboda ko da an yi ma ba ta jin dadin jima’in sam ko kuma ba ta jin dandanonsa irin yanda ta ke tsammanin a ke ji, kamar yadda sauran mata ‘yan uwanta ke jin dadin rayuwar aure da mazajensu.

Tana yin kwanciyar aure ne kawai a matsayin wani aiki na biyan bukatar mijinta ba bukatarta ba, kuma ba don ta na jin dadi ba ko gamsuwa, sai dai kawai don bautar aure ko gudun fushin sabawa al’ada ko addini ko kuma domin kare mijinta daga fadawa tarkon zina,

Hakika akwai mata da yawa da su ke cikin wannan yanayin rayuwar aure marar dadi, wadanda sun hakura da hakkinsu na jin dadin aure, inda wasu matan kuma ke kokarin neman mafita daga wannan matsala ta neman hakkinsu daga mazajensu ko neman magani ko ma kokarin fahimtar matsalar da ke hana su jin dadin da nufin neman warwarar matsalarsu. Wannan kalubale ne babba,

A nan za mu ari wasu bayanan lafiya, domin bada haske ko bayani a kan wasu daga cikin dalilan da su ka saka wasu mata ba su da sha’awa ko ba sa jin dadin jima’i (salam su ke ji) ko ba sa jin dadi sosai ko kuma ma ba su taba jin dadin ba a rayuwar aurensu. Wasu dalilai na da alaka da macen, wasu kuma namijin ne.

Su ne kamar haka.

(1) Ciwon Sanyin Mara Ko Matsalolin Mara Da Mahaifa:

Kama daga sanyin mara (baginities/toilet infections, UTI da STDs), yoyon fitsari, ‘kululun mahaifa (fibroid) da sauran cututtukan al’aura na daga cikin abubuwan da ka iya hana mace jin dadin jima’i. Misali; sanyin gaba mai zuwa da ’yan kananan kuraje cikin farji na sanya mace ta ji zafi wajen jima’i yayin da da maigida ya ke kusantar ta, wanda sau da yawa masu kurajen ba su ma san su na da kurajen ba cikin al’aurarsu, sai dai su ce su na jin zafi lokacin saduwar. Kurajen su na fashewa, saboda da gugar zakari, sai wurin ya zama rauni.

Hakan na sa mata tsoron jima’i da ganinsa a matsayin abin azabtarwa gare su maimakon abin jin dadi. Sau tari ba su san abinda ya haddasa zafin ba, wanda kuma mai yiwuwa ciwon sanyi ne. Ciwon sanyi na iya dakushe sha’awar mace ko namiji. Ciwon sanyi na iya haddasa bushewar gaba, wanda alamunsa shi ne daukewar ni’ima da kaikayin gaba. Idan gaba ya bushe zai yi wahala mace da miji su ji dadin jima’i idan banda zafi. Haka kuma shi ma kululun mahaifa ya kan ci karo da zakari cikin farji, sai mace ta ji wani irin yanayi marar dadi (discomfort) lokacin nishadin aure. Kuma ya na danne mahaifa ya hana haifuwa da kuma sanya yawan zubar jini. Don haka neman magani shi ne mafita

(2) Budadden Gaba.

Rashin tsukakken farji yadda zai damki zakari da kyau, domin samar da jin dandanon fata-da-fata a matse ya na hana mace jin dadin jima’i.

Budadden gaba kalubale ne da ke sanya raguwar jin dadi tsakanin ma’aurata. Sau da yawa ma’auratan biyu ba za su sami gamsuwa da kyau ba, sa’annan macen ba za ta iya jin kololuwar dadi ba (orgasm). Akwai dabarun kwanciya da magani na zamani da za su iya magance wannan matsala. 

(3) Kaciyar Mata (Wuce Gona Da Iri Wajen Yinta):

Kaciyar mata (female circumcision), wacce wanzami ya yankewa belin mace da yawa fiye da yadda ya dace. Yin hakan na kashe sha’awar mace, idan ta girma. Da yawa mata an yanke mu su sha’awa a duniya tun lokacin da su na jarirai. Wasu al’adun a duniya su na yanke beli ne kadan, wasu kuma kamar rabi ne a ke fillewa, wasu kuma cire shi su ke duka, wato yanke shi su ke gabadaya. Yanke beli da yawa ko duka matsala ce da ke hana mace jin dadin jima’i, domin kuwa belin mace (clitoris) shi ne matattarar jin dadin jima’in mace.

Kamar yadda dai malamai su ka yi bayani cewa, yin kaciyar mata mustahabbi ne a Musulunci, Shariah kuma ta yi nuni da cewa kada a wuce gona da iri wurin yankan, ba kamar yadda wasu wanzamai ke aikatawa ba yanzu. To, sai a nemi bayanan malamai, domin fahimtar mas’alar bakidaya. Bugu da kari, za a iya neman magani, domin inganta jin dadin auren, idan hakan ta faru.

(4) Magunguna:

Ko shakka babu akwai nau’in magungunan Turawa ko na gargajiya da za su iya dakushe sha’awar mace. Misali; magungunan da a ke bayarwa domin rage ciwon damuwa ko tsananin bacin zuciyar mutum (antidepressants) da sauransu. Ki na mamakin cewa a da ki na da sha’awa, amma yanzu shiru ne. To, mai yiwuwa wannan maganin da ki ke sha wata da watanni ko cikin makonni shi ne ke sace mi ki sha’awar. Ya na da kyau duk maganin da a ka ba wa marar lafiya a asibiti ko wani wuri ya san tutsun maganin (wato ‘side-effects’ nashi), don kada wani abu ya dame shi bai san abinda ya jaza ma sa ba.

(5) Rashin Ingantaccen Abinci Mai Lafiya:

Idan mace ba ta cin abinci mai kyau ta koshi, wanda zai inganta lafiyarta da jikinta da sinadarai na ni’ima, to sha’awarta tamkar shuka ce wacce ba ta samun ruwa, kuma hakan zai sa ta mutu,

Kifi, naman kaza, madara, yagot, hanta, kwai, zuma, dabino, aya, gyada, kankana, ayaba da sauran abinci mai gina jiki da kuzari tare da ‘ya’yan itatuwa za su iya cika mace da sha’awa da ni’ima bayan daukewar sha’awar. Wadannan abubuwa marmari da abinci tamkar taki ne da ruwa ga shuka, wato sha’awar ‘ya mace. Don haka mazaje su siya wa matansu kayan dadi, domin moruwa daidai gwargwadon hali,

(6) Saurin Inzalin Maigida/Saurin Kawowa/Rashin Karfin Mazakuta:

Wannan matsalar na da alaka da mazajen aure kai tsaye. Wannan matsalar na cutar da mata sosai kuma wani lokacin ta na da alaka kai tsaye da rashin karfin mazakuta. Idan akwai karfin mazakuta ga namiji ko da ba babba ba ne zakarin zai iya gamsar da iyalinsa, kuma zai dade ya na saduwa da iyalinsa har ta biya bukatarta. Haka kuma idan mu ka kalli matsalar ta wata mahangar, hakan na faruwa ne saboda rashin sha’awar namiji, wato sinadaran jima’insa (sed hormones /low testosterone) sun ragu ko sun yi kasa ko kuma hawan jini ko ciwon suga su ke haddasa ma sa matsalar ko ma yawan sinadarin kolesterol ko wasu matsalolin zagayawar jini.

Don haka cin abinci mai inganta lafiya da harkar jima’i ko magani mai kyau da likita ya yi izini da shi zai iya gyara matsalar. Mafi yawan lokuta mata na bukatar tsawon lokaci kafin su kawo (kololuwar dadi, wato ‘orgasm’), sabanin lokacin da maza da dama ke iya jurewa su biya mu su bukata. Don haka yin wasanni, wato yiwa iyali wasa tsawon lokaci (foreplay) na iya fansar lokacin da maigida ba ya iya kaiwa ta yadda mace za ta iya fara biyan bukatarta ko kawowa kafin saduwa da ita.

(7) Rashin Fahimtar Yanayin Mace Da Bukatunta Na Kwanciya:

Kowacce mace da irin bukatunta na jima’i; akwai irin abinda ta ke so a yi mata da nau’in kwanciyar da ta ke jin dadinta, amma da yawa kunya na hana mata bayyana abinda su ke so. Don haka sai su bar mazajensu cikin duhu su na ta kokarin jarraba abubuwan da ba su yi mu su. Don haka matan aure su fidda kunya, domin tattaunawa da mazajensu a kan abinda su ke so wajen jima’i da mazajen; su ma su bayyana irin bukatun nasu, domin fahimtar juna da jin dadin rayuwar aurensu. Haka kuma ya na da kyau maigida ya rika lura da nazari a kan bukatun wasu sassan jikin matarsa, idan mai yawan kunya ce. Yau da gobe zai iya gane abinda ke yi ma ta dadi wajen saduwa. Da sannu za ka tara ilimi mai yawa a kan bukatar matarka, amma idan har ka na lura da kyau.

(8) Wasan Al’aura Da Hannunki:

Idan mace na wasa da farjinta (istimna’i) da yatsa ko wani abu da ta ke sakawa, zai iya sanyawa ta ji ba ta jin dadin jima’i ko gamsuwa da maigidanta, sai dai ta yi istimna’i din, saboda ta fi kowa sanin jikinta da mallakarsa. Ta gano bukatunta na shaidan wanda aurenta ba zai iya biya ma ta ba,

Zawarawa da ‘yan mata wannan abu ne gama-gari a tsakaninsu. Da yawa sun saba biya wa kansu bukata kuma zai iya shafar tarayyarsu da mazajen da za su aura nan gaba. Istimna’i na sa wuyar kawowa ga mace wajen jima’i, saboda ta saba wa jikinta da sai an taɓa wani sashen farji, don ta kawo, wanda mai yiwuwa zakari ba ya taba wurin kai-tsaye a lokacin saduwa – ko ma ba zai iya tabawa ba a zahirin jima’i. Don haka istimna’i ya na sa rashin gamsuwar jima’i ga mace – mijinta zai sha wahala wajen gamsar da ita.

Jikinta ya riga ya koya, saboda ta yiwa kanta horo. Za ta rika tunanin mijinta ba ya iya gamsar da ita ko mazajen da ta aura, saboda sabon da ta yi da koya wa jikinta hanyar gamsar da kanta fiye da hanyar da ta dace, wato jima’i a cikin sunnar aure. Mafita ita ce, dole ta canza dabi’arta, saboda a yawa za ka samu cewa mata masu yawan istimna’i ba su jin daɗin jima’i sai istimna’i ko ma ba su gamsuwa sai sun yi istimna’i. Wannan zai iya kawo babbar matsala a cikin aure.

(9) Aljanin Soyayya:

Aljani na iya shiga jikin mace da sunan soyayya ya dinga saduwa da ita ko ma ya aure ta. Hakan zai sa aljanin ya hana ta aure ko haihuwa ko rashin zama lafiya da miji, idan ta yi auren, kuma zai saka ma ta daukewar sha’awa da ni’ima ga mijinta ko zubar jini ko ruwa mai wari ko ma gaban mijin ya ki mikewa lokacin saduwa. Za ta rika mafarkin a na saduwa da ita, wanda shaidanin zai zo ma ta da siffar mijinta ko wani mutum ko siffar mace na saduwa da ita. Ko ta rika ganin mutum tsirara gabanta. Wadannan su na daga cikin alamomin, kuma dalilin hakan ya na hana mace jin dadin jima’i ko sha’awa.

(10) Rashin Sha’awa Saboda Karancin Sinadaran Jima’i

A Jini Ko Ciwon Damuwa:

Karancin sinadarin jima’i da sauye-sauyen halittar mace (low estrogen) na iya haddasa sallacewar sha’awar mace. Alamomin karancin sinadarin su ne; jin zafi wajen jima’i, saboda rashin ruwan gaban mace, zuwan al’ada ba a kan lokaci ba ko rashin yin ta, karuwar cututtukan mafitsara (UTIs), canjin yanayin rayuwa daga farin ciki zuwa damuwa, ciwon nono, ciwon kai, ciwon damuwa, kasala, wuyar lura ko nazari, rashin kwarin kashi da sauransu. Idan ba a magance matsalar ba, har rashin haihuwa za ta iya sanya mace.

Abubuwan da ke haddasa karancin sinadarin sun hada da ciwon koda mai tsanani, tsananin motsa jiki, zufar dare, gumin jiki, rashin bacci, rashin cin abinci saboda tsoron yin kiba. Haka kuma ga mata wadanda su ka haura shekara 40 na haifuwa karancin sinadarin na iya zama alama ta cewa sun kusa gama al’ada. Don haka sai a ga likita, domin magance matsalarr ko a nemi magani. Allah Ya taimaka.

Ina Mafita?

Ki nemi sassaken jikin bishiyar kuka ki shanya shi ya bushe, sai ki daka shi ya zama gari kuma ki tankade shi ya dawo gari lukui. Sai kuma ki nemi farin garin kwalaba da nono ki debi kwallayen ki zubar. Sai ki bar iya farin garin ki dan kara daka shi yadda zai dawo gari kamar fulawa. Garin hulba shi ma daidai da yawan wadancan din. A na son yawan duka garin ya zama daya. Sai a hade su a gauraye su. Sai a dinga dibar garin maganin cikin babban cokali biyu a zuba a cikin danyar madarar shanu, ki gauraya, ki rika sha safe da yamma. In sha Allahu indai wannan matsalar ce ki ka yi amfani da wannan hanyar za ki sha mamaki da yardar Allah. Allah Ya sa mu dace.

Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top