BURIN LEO MESSI YACIKA BAYAN SHEKA 28 , MEZAKUCE GAMEDA BALOND’O NA BANA

 Burin Lionel Messi na tsawon shekaru ya cika bayan samun damar dage kofinsa na farko a wasan da Argentina ta doke Brazil a Copa America a birnin Rio.

Argentia dai ta doke Brazil har gida da ci daya mai ban haushi a wasan karshe na gasar da aka buga a filin wasa na Maracana.

Messi mai shekara 34 ya shiga yanayi na matuƙar farin ciki lokacin da aka busa wusur din kammala gasar inda ya rinka shawagi da murna tare da sauran abokan wasa na tawagar ƙasar, kafin daga bisani aka rinka jefa shi sama cikin bikin murna.

Wannan ne karon farko da tauraron ɗan wasan Argentina Lionel Messi ya lashe wata babbar gasa tare da tawagar ƙungiyarsa a manyan wasa 10 da ya haskawa ƙasarsa.

Ya kuma taimakawa Argentina wajen kawo ƙarshen shekaru 28 da ta kwashe rabonta da lashe gasar, sannan an bayyana shi a matsayin gwarzon wasan sakamakon ƙwallaye hudu da ya zura a gasar.

Messi dai ya kuma so ya samu damar rufe wasan da kwallon karshe da watakil ta bakwana a matsayinsa na kyeftin sai dai ƙwallon ya subuce masa.

Tawagar Brazil da ke kare kambunta ta sha mamaki, musamman lokutan da Emi Martinez ya ceto ta daga hannun Richarlison da Gabriel Barbosa.

Neymar ya yi kusan rashin nasarar daga wa Brazil kofin Copa America

ASALIN HOTON,REUTERS

Bayanan hoto,

Neymar ya yi kusan rashin nasarar daga wa Brazil kofin Copa America

Yayin da Messi ke bikin murna, a ɓangare guda tsohon abokin wasansa da suka fafata a ƙungiya guda wato Neymar ya faɗi ƙasa yana hawaye bayan kammala wasan.

Ƴan wasan biyu da suka taka leda tare a Nou Camp tsakanin 2013 da 2017 kafin Neymar ya koma Paris St-Germain, sun rungumi juna na tsawon lokaci kafin bikin mika kofin.

Related ARTICLES

Man Utd ta kwaÉ—aitu da Di Lorenzo, Chelsea na son É—auko Haaland

Man Utd na iya samun Kane, Man City ta yi magana da Griezmann

An gama duba lafiya É—an wasan Najeriya Etebo da zai koma Watford

Dan wasa Angel Di Maria da ke buga wa kungiyar PSG wasa ne ya zura kwallo dayan da Argentina ta samu kafin a kai ga zuwa hutun rabin lokaci.

Dubban mutane sun bazu a titunan Buenos Aires, babban birnin Argentina domin murnar nasarar da ƙungiyar ƙwallon kafa ta ƙasar ta samu na cin wani babban wasa a karon farko cikin shekaru 28.

Source: BBC HAUSA reports

Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top