Da dumi dumi; Jami’an tsaro sun kama Shaikh Abduljabar.
Wasu rahotanni daga jihar Kano na nuni fa cewar jami’an tsaro a yammacin ranar Juma’a sun yi awon gaba da Abduljabar Nasiru Kabara dake unguwar Filin mushe a yankin karamar hukumar Gwale.
Idan baku manta ba, a makon da ya gabata aka gudanar da wata mukabala tsakanin Abduljabar da Malaman Kano inda aka zargi Abduljabar da yin kalaman batanci ga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam zargin da shi Abduljabar ya kasa karewa.
Bayan kammala waccan mukabalar Abduljabar ya bayar fa wata sanarwa inda yace ya janye dukkan kalaman da ake zargin yayi, yana mai baiwa al’umma hakuri, daga bisani kuma ya janye wannan tuban da yayi.
Tuni dai akai ta kiraye kirayen Gwamnatin Kano ta dauki mataki akansa ko kuma ya fuskanci fushin gamagarin mutane. Sai dai wasu rahotanni sun nuna an cafke Abduljabar a yammacin wannan rana.