Dahuwar kazar Turai
Abubuwan da za a bukata
• Cinyoyin kaza/kaza gaba dayanta
• Citta danya
• Danyar tafarnuwa
• ‘Soy sauce’ (yana nan baki a kwalba. za a iya samunsa a manyan shaguna )
• Attarugu
• Albasa
• Magi/gishiri
• Kori
• Zuma
• Man gyada
Hadi
Bayan Uwargida ta wanke kazarta kamar yadda na koya mana a baya, sai ta dora ta a matsami domin ruwan jikin kazar ya tsane. Sannan ta kankare bayan citta kamar rabinta tare da tafarnuwa bayan ta bare ta jajjaga su a wuri daya. Ta dauko attarugu kamar biyu ko uku ta yayyanka kanana. Sannan a dauko albasa ta yi mata yankan tuyar kwai ta ajiye a gefe.
Ta samu roba, sannan ta zuba jajjagen tafarnuwa da citta a ciki sannan ta zuba magi da kori da albasa da kuma ‘Soy sauce’ da zuma kamar cokula uku sannan ta gauraya hadin da cokali ta dauko wankakkiyar kazarta ta tsoma a cikin wannan hadi. Ta gauraya kazar a cikin hadin yadda komai zai shige ta ta dauko leda ta rufe saman kwanon/roba sannan ta bude gidan sanyi (fridge) ta saka na tsawon awa hudu zuwa shida.
Bayan haka, sai ta dauko tukunyar tuya ta zamani (non-stick frying pan) ta dan diga man gyada kadan kamar na tuyar kwai. Bayan ya yi zafi, ta dauko kazar ta sa a cikin tukunyar tuyar tana juya ta gefe-gefe har sai ta yi launin toyuwa. Sannan ta kwashe ta a ajiye a gefe. Ta zuba wannan ruwan hadin da ya rage na hadin kazar a tukunyar ya yi tafasa daya sannan sai ta mayar da kazarta ciki ta gauraya sannan ta sauke. Sai a ci da jus din lemo ko da dafa-dukan shinkafa. A ci dadi lafiya.