Yadda ake Farfesun kai da Kafar Rago
Abubuwan da za a bukata
Kan rago da kafa da aka babbake
Attarugu
Albasa
Garin citta
Tafarnuwa
Maggi
Kori da thyme
Kayan kanshi
Tukunyar dafa ganda (Pressure cooker)
Hadi
Bayan uwargida ta wanke ganda da tafasashen ruwa, sai ta dora ta bari ya sake tafasa domin cire maikon da ke jikin gandar. Za ta ga maiko ya yi sama sannan ta zubar da wannan ruwan sai ta kara zuba wani ruwan a tukunyar dafa gandar domin sanyata ta nuna kuma ta yi laushi (idan ana wannan dahuwar a jira naman ya nuna ya yi laushi sosai kafin a zuba kayan hadi daga baya). Sai ta yayyanka albasa, ta jajjaga attarugu daidai misali da tafarnuwa da citta kadan. Ta zuba magi da kori da thyme. Sai ta zuba ruwa daidai misali ta rufe. Sai ta jira ta nuna na tsawon minti kadan sai ta sauke.
Ana son cin wannan girki da safe ko da dare. Wannan irin girki shi ne wanda ya fi dacewa da masu son rage kiba domin ganda ba ta dauke da sinadarin dada kiba illa a ci don dadi. Tafarnuwar da aka sanya a cikin girkin na rage mura da kuma kare wasu cututtuka. Da fata wannan girki zai sanya kunnen mai gida motsi. Ga dadi ga kuma arhar kayan girki. A sha lagwada lafiya.