Filin Girke-Girke: yadda Akeyin Hadaddun kayan mar-mari da kuskus

 Hadaddun kayan mar-mari da kuskus

 

Kayan hadi:

. Abarba

.  Ayaba

. Kankana

. Gwanda

. Sukari

. Filebo

. Yogot

. Kuskus

Yadda ake yi:

Uwargida za ki fara soya kuskus dinki da man gyada sai ki ajiye shi a gefe. Sannan ki dauko kayan marmari ki yanyanka su kanana irin yankan fruit salad. Sannan ki hada su a mazubi guda.

Sai ki dauko soyayyen kuskus din nan ki zuba a kai. Ki zuba sukari dan kadan a ciki. A karshe sai ki zuba yogot dinki a ciki. Sai ki sa shi a firiji don ya yi sanyi.

Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top