Miyar karkashi da kubewa
Abubuwan da za a Bukata:
Ganyen karkashi
Kubewa danya
Tokar miya ko kanwa
Attarugu
Bandar kifi
Nama
Albasa
Danyar tafarnuwa
Garin citta
Magi
Yadda Za’a Hada
A karkade ganyen karkashin tsaf sannan a yayyanka shi kanana sosai. A samu kubewa danya a yayyanka ta sannan a saka a turmi a daka ta yi laushi sosai. In kuma da kanwa za a yi miyar sai a daka tare da kanwar kadan. Sannan a kwashe a ajiye a gefe. A daka attarugu da tafarnuwa a kwashe. A wanke bandar kifi da ruwan dumi a cire kwayoyin sannan a yayyanka albasa kanana. A dora ruwa a tukunya sannan a silala nama har sai ya yi laushi. Sai a kara ruwa kadan a kan romon naman sannan a zuba yankakkiyar albasar da jajjagen attarugu da garin citta da bandar kifi har sai sun tafasa sannan a dauko kubewar da aka daka a zuba a rika gaurayawa har ta fara nuna sannan a dauki karkashin a zuba a dauki maburgi a burga sannan a ci gaba da juyawa. Idan har ba a sanya kanwa a miyar ba, a wannan lokacin ya kamata a sanya tokar miyar sannan a jika magi ya narke sai a ci gaba da gaurayawa har sai dandanon ya fito sannan a sauke. Za a iya cin wannan miya da tuwon semo ko masara.