Gwamnatin Najeriya Za Ta Ci Gaba Da Farautar Manyan Ƴan IPOB
Gwamnatin Najeriya ta tabbatar da cewarza ta yi wa Nnamdi Kanu adalci a yayin da ake zargin sa a aikata wasu laifuka a ƙasar.
Ministan yaɗa labarai da al’adu a Najeriya Lai Mohammed ne ya bayyana haka a yayin wani taron manema labarai a Abuja.
Ya ce gwamnatin tarayya ba za ta kyale duk wani da ake zargi da haɗa kai wajen kai hare-haren da ƙungiyar IPOB key i a kudancin ƙasar ba.
A yayin ganawar tasa da manema labarai a yau, Lai Mohammed ya ce sama da shekaru biyu gwamnatin ke bibiyar Nnamdi Kanu wanda ke rayuwa a ƙasashe daban-daban.
Gwanatin ta ce ta na zargin sa da aikata laifuka 11 ciki har da zagon ƙasa wajen jagorantar ƙungiyar da ke ƙoƙarin ɓallewa daga Najeriya IPOB tare da kafa ƙasar BIAFRA.
An kama Nnamdi Kanu A ranar Lahadi yayin da aka dawo da shi Najeriya kuma gwamnatin ke tuhumarsa da laifuka.
A baya an bayar da belin Nnamdi Kanu sai dai ya tsallake sharuɗan belin da aka ba shi.