Gwamnatin shugaba Buhari na shirin fara aikin layin Dogo daga Kano zuwa Kaduna wanda zai lashe Naira bilyan 1.2

 Nan Da Makonni Biyu Gwamnatin Tarayya Za Ta Kaddamar Da Aikin Shimfida Layin Dogo Daga Kaduna Zuwa Kano Da Aka Ware Wa Zunzurutun Kudi Naira Bilyan 1.2

Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya ce nan da sati biyu za a fara aikin layin dogo na Kaduna zuwa Kano.

Amaechi ya ce aikin da aka amince da yin sa tun 2017 zai lashe makuden kudi har Dallar Amurka biliyan 1.2

Minista sufurin ya ce gwamnatin tarayya ta ware kaso daya cikin uku na kudin aikin yayin da sauran bashi za a ciwo daga China

Rotimi Amaechi, ministan sufurin Nijeriya ya ce za a fara aikin shimfida layin dogo na Kaduna zuwa Kano da zai lashe Dalla Biliyan 1.2 nan da makonni biyu.

Amaechi ya bada wannan sanarwar ne yayin wata taron manema labarai da tawagar sadarwa ta shugaban kasa ta shirya a ranar Juma’a a Abuja.

The Cable ta ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta amince da aikin na layin dogo daga Kaduna zuwa Kano ne a Janairun shekarar 2017.

Gwamnatin tarayya za ta yi hadin gwiwa da China don gina masana’antar kera kayan aikin layin dogo

Amaechi ya ce gwamnatin tarayya za ta ciwo bashin akalla naira biliyan 100 domin yin aikin.

Ya ce a yayin da ake jiran bashin daga gwamnatin kasar China, kashi daya cikin uku na kudin aikin zai fito daga kasafin kudin gwamnatin tarayya.

A yayin taron manema labaran, Amaechi ya ce gwamnatin tarayya ya bada Dallan Amurka miliyan 280 domin aikin kuma nan gaba za ta bada cikin Dalla miliyan 100.

Ya kuma ce gwamnatin tarayya ta rattaba hannu kan yarjejeniya da gwamnatin China domin gina kamfanin kera kayan aikin jirgin kasa a Kajola, jihar Ogun da za a rantsar wannan shekarar.

Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top