Gwamnatin shugaba Buhari zatayi Karin Yara Miliyan 5 A Shirin Ciyar Da ‘Yan Makaranta Kafin 2023 – Minista Sadiyya

 Gwamnati Za Ta Shigar Da Karin Yara Miliyan 5 A Shirin Ciyar Da ‘Yan Makaranta Kafin 2023, Inji Minista

Ministar Harkokin Jin ƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar-Farouq, ta bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta ƙudiri aniyar ƙara yawan ɗalibai guda miliyan biyar cikin shirin ciyar da yara ‘yan makaranta, wato ‘National Home Grown School Feeding Programme’ (NHGSFP) daga yanzu zuwa shekarar 2023.

 

Hajiya Sadiya ta faɗi haka ne a lokacin taron da masu ruwa da tsaki su ka yi kan tantance masu amfana da shirin don haɓaka shi wanda aka yi a Gusau, babban birnin Jihar Zamfara.

A sanarwar da mai taimaka mata ta musamman kan harkar yaɗa labarai, Halima Oyelade, ta fitar a Abuja, an ruwaito ministar ta na faɗin, “Sama da yara ‘yan makaranta tara ne su ke amfana da kyautar abinci sau ɗaya a kowace rana a lokacin zuwa makaranta a kowane zangon karatu a duk faɗin ƙasar nan.

“Yanzu, mun samu izinin mu ƙara yawan ‘yan makaranta miliyan biyar kafin shekarar 2023.

“Akwai masu dafa abinci sama da 100,000 da aka ɗauka aiki da kuma ƙananan manoma sama da 100,000 a cikin wannan shiri, da masu amfana ta hanyar su, wanda ya sanya shirin na NHGSFP ya kasance muhimmi wajen kyautata cigaban zamantakewa da tattalin arziki kuma ya kamata a ƙarfafa shi, a inganta shi a ko’ina a ƙasar nan.

“Ina murnar ganin yadda ma’aikatan gwamnatocin Zamfara da Tarayya da ke gudanar da shirin na NHGSFP da kuma sauran masu ruwa da tsaki su ke aiki tare da juna kuma cikin kusanci don tantance yawan masu amfana da shirin kuma su ke gyara bayanan su don samun tasiri da tsare gaskiya.

“Saboda haka, a yayin da mu ke gode wa gwamnatin Zamfara saboda sadaukarwar ta ga aiwatar da NHGSFP, ina kuma ba kan mu ƙwarin gwiwa kuma mu tabbatar da mun ƙara azama domin ganin an samu ƙarin yara masu amfana da wannan shiri.”

Sadiya ta ƙara da bayyana cewa an fito da shirin NHGSFP ne da tunanin zai kasance mai fuskoki daban-daban don ƙara yawan ɗalibai, inganta abincin ɗalibai, mara wa masu noma abinci ƙwarin gwiwa tare da ƙara yawan ɗalibai da samar da aikin yi da kuɗaɗen shiga.

“Hasali ma dai, manufar sa ita ce a samar da abinci mai gina jiki ga dukkan ‘yan makaranta da ke makarantun firamare na gwamnati sau ɗaya zuwa sau uku a rana.”

Ta ce manufar Shugaba Muhammadu Buhari ita ce a yaƙi fatara da yunwa, don haka aka ƙirƙiri ‘National Social Investment Programme’ wanda ya ƙunshi shirye-shirye da su ka haɗa da NHGSFP, N-Power, ‘Conditional Cash Transfer’ da ‘Government Enterprise and Empowerment Programme’. NAN

Source: Arewablogng

Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top