Jam’iyyar APC za ta tsayar da Goodluck Jonathan takarar shugaban kasa a 2023
Buni, Malami da Badaru na neman kujerar mataimakin shugaban kasa
APC za ta bawa dan kudu tikitin takarar kujerar shugaban kasa a shekarar 2023
Ana cigaba daa shirye-shiryen tunkarar 2023
Wasu rahotanni da muke samu ya nuna cewa babbar jam’iyyar APC mai mulki na shirin tsayar Goodluck Jonathan takarar shugaban kasa a 2023.
Biyo bayan zafin da jam’iyyun siyasar Najeriya suka dauka akan kan canja tsarin ya zama na karba-karba bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kammala mulkin shi a shekarar 2023. Babbar jam’iyyar adawa ta PDP na cigaba da fuskantar matsaloli da suka sanyata cikin halin tsaka mai wuya, bayan ta rasa wasu gwamnoninta da suka canja sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulki.
Wani jigo a babbar jam’iyya mai mulki ta APC, wanda ya bukaci a boye sunan shi ya bayyanawa jaridar Legit.ng cewar, shugabannin jam’iyyar APC sun yanke shawarar bada tikitin takarar shugaban kasa a shekarar 2023 ga tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.
Buni, Malami da Badaru na neman kujerar mataimakin shugaban kasa
Majiyar ta ce shugaban jaam’iyyar na kasa mai rikon kwarya, kuma gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, da ministan shari’a na kasa, Abubakar Malami da kuma gwamnan jihar Jigawa, Badaru Abubakar, sune suke kokarin neman kujerar mataimakin shugaban kasa
A cewar majiyar, sabon tsarin na APC, ya riga yayi nisa, domin tuni ya kusa zuwa matakin karshe, domin bawa tsohon shugaban kasar kyakkyawar tarba zuwa ga jam’iyyar ta APC a kowanne lokaci a cikin watan Agustan shekarar 2021.
Jam’iyyar APC
![]() |
Alamar Jam’iyyar APC |
APC za ta bawa dan kudu tikitin takarar kujerar shugaban kasa a shekarar 2023
Majiyar ta cigaba da cewa yanzu haka shugaban kasa Muhammadu Buhari muke jira ya dawo Abuja domin yin murnar “kama babban kifi” daga babbar jam’iyyar adawa, da kuma yiwa shekarar 2023 kyakkyawan tsari.
Tuni dai Buni, Malami, da Badaru, suka fara neman kafa a cikin jam’iyyar, inda cikin sirri suke bin manyan da kuma neman shawara ga masu ruwa da tsaki, manyan kasa, ‘yan siyasa da kuma sarakunan gargajiya a yankunan Kudu da Arewa.
An ce jam’iyyar na gabatar da taro cikin dare cikin sirri a kowacce rana tsakanin masu neman kamun kafar kujerar mataimakin shugaban kasa.
Ana cigaba daa shirye-shiryen tunkarar 2023
Haka kuma anyi imanin cewa shawarwari da masu neman kujerar mataimakin shugaban kasar suke yi na iya kaiwa ga tsara yadda za su gudanar da binciken hada-hadar yadda za a samu kudi yayin da shekarar 2023 ke cigaba da karatowa.
2023: APC ta bayyana wani gwamna a matsayin wanda take so ya tsaya takarar shugaban kasa
APC
Ana sa ran Buni zai yi amfani da farin jinin da yake da shi sakamakon rike kujerar shugaban jam’iyyar APC da yake a yanzu wajen neman kujerar yayin da ake shirin bayyana Jonathan a matsayin dan takarar shugaban kasa a 2023.
Haka suma magoya bayan Abubakar Malami sun bayyana cewa za su yi iya bakin kokarin su wajen ganin na su ya samu, inda suke bin manyan ‘yan siyasa don neman kamun kafa a yankunan Kudu da Arewa.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.
Source: Legit.ng