Karon farko za’a fitarda rahoton musabbabin hatsarin jirgin tsohon Hafsan Sojan Kasa

wucin-gadi kan musabbabin hatsarin jirgin tsohon Hafsan Sojan Kasa

 Ofishin kula da hadurra zai fitar da rahoton farko kan musabbabin hatsarin jirgin da ya rutsa da tsohon Babban Hafsan Sojan 

Akasari yakan dauki wata 18 gabanin fitar da cikakken rahoton musabbabin hadari Sai rundunar sojin saman Najeriya ta ga dama za ta bayyana wa jama’a rahoton A ranar Alhamis din da ta gabata ne Ofishin Binciken Hadura, ya ce rahoton farko na musabbabin hatsarin jirgin saman soja wanda Babban Hafsan Sojan Kasa, Laftanal Janal Ibrahim Attahiru, da wadansu mutum 10 suka mutu a Kaduna a watan Mayun bana za a fitar da shi a makon gobe. 

Babban Daraktan, ofishin Akin Olateru, ne ya bayyana hakan a lokacin da aka fitar da rahoton hatsarin jiragen sama guda takwas da ofishin ya fitar a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja. 

Sai dai ya kafe cewa ya rage wa rundunar sojin sama ta Najeriya ta yanke shawarar kan ko za ta bayyana wa jama’a sakamakon binciken da ke kunshe a cikin rahoton, yana mai jaddada cewa ba hurumin ofishin ba ne da fitar da irin wadannan bayanan.  

Source: legit hausa

Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top