Majalisar Dattijan Najeriya ta ce Ma’aikatar Sadarwa ta kafa wata cibiya da za ta rika aiki da butumbutumi da basirar na’ura don yaki da matsalolin tsaro a kasar.
![]() |
Getty images |
Najeriya dai na ci gaba da fama da matsalolin tsaro da suka hada da garkuwa da mutane don kudin fansa da hare-haren ‘yan bindiga musamman a arewacin kasar da ma ayyukan masu ikirarin jihadi a arewa maso gabashin kasar.
Kawo yanzu, sama da dalibai 1,000 ne aka sace daga makarantu a arewacin Najeriya tun daga watan Disamban 2020.
Agajahub publishers