SHIN INA DATAN DA NAKEAMFANI DA SHI WAJEN BROWSING YAKE ZUWA? IDAN NASHIGA FACEBOOK KO WHATSAPP DA DATA NA SU FACEBOOK DINNE SUKE DAUKAWA? KASHI NA DAYA (1)
DATA MINING DA BIG DATA,
SHIN INA DATAN DA NAKE
AMFANI DA SHI WAJEN BROWSING YAKE ZUWA? IDAN NASHIGA FACEBOOK KO WHATSAPP DA DATA NA SU FACEBOOK DINNE SUKE DAUKAWA? KASHI NA DAYA (1)
Wannan dai tambayace diyawa daga cikin ‘yan uwa zasuso samun amsarta, na dauko wannan makala ne ganin cewa yanzu hukumomi sun maida alkiblar kasarnan daga man fetur zuwa “Digital Economy”, Musamman tun daga lokacin da aka baiwa mai girma “Sheikh Dr. Isa Ali Fantami” minister a karkashin mulkin Shugaban kasa Muhammadu Buhari. Yana da kyau mu fahimta mafi yawan “Digital Economy” da akeso a maidamu akai ya ta’allaka ne ga “DATA MINING” da kuma “BIG DATA”. A wannan rubutun INSHA ALLAHU zamu duba alfanu
da kuma rashi ko hatsarin da ke tattare “DATA MINING”, tare da dubiya zuwa ga ina “DATAN WAYOYINMU” da muke amfani
dashi wajen hawa yanar gizo ina suke zuwa, haka tayaya manya kamfonuwa irinsu “WHATSAPP” da “FACEBOOK” da
“Twitter” da sauransu ke samun kudade alhali manhajojin nan
duka kyauta muke amfani dasu?.
MENENE DATA?
Ga kowane karatu ko wane irin abu yana da kyau mufara sani
da fahimtar tushensa kafin mukaiga abin kai tsaye, domin
hakan zai buda mana kwakwalwarmu dan mukara fahimtar
bayananda zamu nan gaba. Na’am Menene “DATA”? Kalmar
DATA kalma ce jam’i ma’ana diyawa guda dayansa ana kira
“DATUM”. DATA yana nufin dukkan wani abu da idan aka
sarrafashi yakan iya bada bayani ko yazama bayani ko kuma
yayi nuni da bayani wato (Information) a turance. DATA na
nufin dukkan wani zane, alama, ko rubutu da idan aka karanta
ko aka sarrafashi yadan iya zama bayani. Misali Tun a matakin
primary one ko nursary ko a islamiyya ajin rauda ake fara
koyar da ABCD, KO ALIFUN, BA’UN. Wadanna haruffan duka
zane ne domin kuwa malami zaizo ne akan allo yayi zane
sannan yace wannan abu kaza ne, misali mudauki alifun,
malami zaiyi tsayayyen zane ne akan allo sannan yace wa
dalibai wannan alifun ne, kenan wannan zanen alifun ne, anan
tamkar yana fadawa dalibanne da cewar duk inda kuka irin
wannan zanen indai a rubutun larabci yake to ana kiransa
alifun, haka na ba’un ma zai zana yafada musu haka na Ta’un
ma har zuwa karshe anan zanen da malamin yayi akan allon
“DATA” yake baiwa daliban domin shi yasan ma’anarsa duk
inda yagani kuma yana ganewa, amma kokarin me yake?
Kokarinsa shine ya isarwa da daliban bayani ta hanyar zanen
da yayi bisa allon, ta yadda koda a wani waje sukaga wannan
abin to zasu iya amfani da zuciyarsu da bakinsu su karanta
sannan su fahimta. Tam a yayin da daliban suke karantawa
kuma yana zame musu bayanine domin suna amfanine da
kwakwalwarsu wajen sarrafa zanen domin yazama wani abu
mai bada ma’ana ko ince bayani a garesu.
Misali na gaba ko rubutunnan da nayi ai ba baki da baki nake
baku bayanin ba, amma ina amfanine wasu zane wadanda
idan har kuka kallesu ina tunanin zaku iya amfani da
kwakwalwarku wajen sarrafashi dan yazamemuku bayani ko
wani abu mai ma’ana.
Misali na uku kamar hira da kurma ko wanda bayaji, kurame
suna amfani da alamomi ne wajen hira ko fadawa mutun wani
abu, wannan alamar kaida kake hira da kurman shi kake
sarrafawa don ka fahimci bayanin da kurman yake kokarin
isarmaka. A takaice a lokacinda kurman yake amfani da yatsa
ko wani abu dan baka bayani a wannan lokacin “DATA” yake
baka kai kuma kana amfani da kwakwalwarka ne wajen sarrafa
(Processing) “Datan” dan yazama bayani wato “Information” a
gareka.
.
Idan dai zamu lura da bayanan da muka kawo a sama, Muna iya bada ma’anar “DATA” wanda a turance akacewa “Data is a raw facts, and unprocessed Information.” ko kuma “Data is a facts and figures which will become information after it been processed.” da cewar “Data dukkan wani zane ne, alama ne ko launi da kan iya zama bayani ko yabada ma’ana idan aka
sarrafashi”. Wannan itace babban dalilin da yasa abinda kake amfani dashi dan hawa yanar gizo ake kiransa DATA. Dukkan wani abu a yanar gizo bayanine wato “Information ne.” Idan da zaka/ki siyi DATA na 1GB, Hakan na nufin kanada damar kallo ko kuma sauke bayanin da yakai nauyin 1GB, idan da zamu lura daga lokacin da muka fara browsing a lokacin zamuga datanmu yana kasa, hakan na nufin wannan datan shine wayarka ko kuma computerka ke sauyama su izuwa bayanai da kake kallo a yanargizo. Kamar yadda muka fada da farko da cewar dukkan wani abu da idan sauyashi kan iya zama bayani ko yabada bayani shine DATA ko anan dinma hakanne, domin wannan datan wayarka ko computernka sune bayanan da kake
gani a yanar gizo, domin ai in babu DATA baza ka iya shiga yanar gizo ba.
INA DATA NA YAKE TAFIYA?
Kamfanin sadarwa da tabaka datan ita take sake cirewa, ISP (Internet Service Provider) da mutun yayi amfani dashi misali MTN, KO AIRTEL, KO ETISALAT KO GLO da sauransu da muke amfani dashi sune suke sake daukar abinda suka bamu. Babu hadin Facebook da DATAnka, babu hadin Google ko Whatsapp da DATAnka hasalima kamfanonuwan sadarwan basa basu ko kobo karshe madai basu da alaka ko kadan. To sai dai yanada kyau musani suma kamfanonin da muke siyan DATA a
wajensu ba sake cirewa suke ba domin ko sun cire babu amfanin da zai musu, ribarsu shine katin da kasiya kuma kayi amfani dashi wajen siyan DATAn. Wannan DATAN ba komai bane illa lambobi ne kawai ake turawa wayarka. A yayin da kayi kokarin shiga yanar gizo na’urar kamfaninda kake amfani dashi zai duba layinka ne yaga cewar shin akwai ragowar lambobin datan ko kuma babu a layin? idan kuwa babu sai yahanaka
shiga inko akwai yabarka kawuce. Daga lokacin da kafara ziyartar shafukan a lokacin na’urar zai fara cire nauyin abinda
kasauke, misali kanada 100MB layi sai kuma kashiga shafi mai nauyin 100KB anan abinda na’urar zaiyi shine total = 100MB – 100KB haka zaici gaba da yin subtrating har iya lokacin da zai zama