Shinkafa Ta Wadata A Nijeriya, Saura A Fara Fitarwa Kasashen Waje, Cewar Kungiyar RIFAN

 Shinkafa Ta Wadata A Nijeriya, Saura A Fara Fitarwa Kasashen Waje, Cewar Kungiyar RIFAN

…Ba zai yiwu mu yi kasa da farashin buhun shinkafa ba, inji ‘yan kasuwa

 

Daga Comr Abba Sani Pantami

Kungiyar Manoman Shinkafa ta Nijeriya (RIFAN), ta ce noman shinkafa a kasar ya karu daga tan miliyan biyu a 2015 zuwa tan miliyan tara a 2021, Daily Nigerian ta ruwaito.

Da yake bayyana hakan a Kaduna a ranar Alhamis, Shugaban RIFAN, Aminu Goronyo, ya ce duba da yawan kayan da ake sarrafawa a yanzu, Najeriya ta shirya zama kasar da zata ke fitar da shinkafa zuwa kasashen waje.

A cewarsa: “Kafin zuwan gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari a shekarar 2015, mun saba samar da kimanin shinkafa tan miliyan biyu a shekara.

“A yau, za mu iya alfahari da tan miliyan tara a shekara; akwai bambanci sosai kuma yanzu za mu iya cewa balo-balo Najeriya ta wadatu da shinkafa.”

Game da tsadar abinci: Ba fa zai yiwu mu yi kasa da farashin buhun shinkafa ba inji ‘Yan kasuwa.

Sai dai har yanzu talakawa a Najeriya na kokawa kan tsadar da abinci ya yi, musamman shinkafa.

Source: Arewablog

Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top