Rundunar sojin Najeriya ta ce ta kama wasu ‘yan Boko Haram da ake zargi yayin wani aiki da suka gudanar a yankin Muna da ke jihar Borno.
Daraktan yada labarai na sojoji Onyema Nwachukwu, ya ce bataliya ta 195 karkashin shirin Hadin kai da kuma hadin gwiwar yan CJTF aka yi wannan aikin.
Nwachukwu an kwace gurneti daga hannun mutanen da ake zargi da gatari guda da mota daya da kuma babura biyar, an karbe wayar saluma biyu kirar (Techno and Infinix) da man fetur da yawa da bakin man juyen ababan hawa.
Ya kara da ce “an kwace kwayoyin da ake shahankali ya gushe da na kara karfin jima’i da maganin kwari da wasu sauran kayan abinci”.
” Dakarunmu sun zagaye duka yankin yayin wannan atisaye kuma sun lalata sansanonin ‘yan ta’adda, sun kuma dirarwa wasu a kauyen Labe, wadanda suka yi kokarin guduwa amma an samu nasarar cafke su,” in ji shi.