Yadda ake Faten Doya mai Alayyahu
Abubuwan da ake Bukata
• Doya
• Manja
• Alayyahu
• Nikakken ‘cray fish’
• Albasa
• Attarugu
• Tumatir
• Bandar kifi
• Nama
• Tafarnuwa
• Citta
• Magi
• Kori
Yadda zaki Hadi
A sami danyar doya a fere ta a yayyanka ta kanana sannan a wanke a ajiye a gefe. Bayan haka sai a samu ganyen alayyahu shi ma a yayyanka amma manya-manya a wanke da ruwan gishiri sannan a ajiye a gefe. A silala nama da albasa da gishiri kadan sosai sannan a sauke.
A dora tukunya a wuta sai a zuba manja sannan a zuba yankakkiyar albasa da tafarnuwa da garin citta da yankakken attarugu da tumatir. A yi ta gaurayawa har sai sun soyu. Sannan a zuba ruwan nama da naman da magi da kori a wanke bandar kifi a zuba da ‘cray fish.’ Idan ya dan tafaso sai a dauko wannan yankakkiyar doyar a zuba a ciki. Idan ta dahu ta yi laushi sai a samu muciyar tuwo a dan farfasa doyar sama-sama yadda ruwan zai yi kauri sannan a dauko yankakken alayyahu a zuba na tsawon minti biyu zuwa uku. Idan ya nuna sai a gauraya a sauke. A ci dadi lafiya.