Yadda ake Girka miyar Agushi irin na Ibo
Abubuwan da za a bukata
Agushi
Manja /man gyada
Ganyen Uziza (za a iya samunsa a inda Ibo suke a kasuwa)
Tattasai
Albasa
Garin kifin ‘cry fish’
Daddawa
Kifi
Nama
Kayan dandano
Kayan kamshi
Hadi
A kwaba agushi da ruwa yadda zai dan yi kauri sannan a dora tukunya a wuta a zuba man gyada kadan da manja kadan.
Bayan haka, sai a mulmula kwabin agushi zuwa kananan mulmule sannan a zuba albasa a rika jefawa a cikin man.
Haka za a rika jefawa sannan a juya da cokali na tsawon mintuna uku sai a zuba ruwa a cikin tukunyar da ake soya agushin.
Sai a rufe da marufin tukunyan har sai ya tafasa sannan sai a dan farfasa agushin da cokali a zuba dafaffen busasshen kifi da dafaffan nama da yankakken ganyen Uziza da kayan dandano da na kamshi sannan a rufe.
Bayan mintuna goma zuwa sha biyu sai a sauke.