Yadda ake Girka Miyar Koda
Abubuwan da za a bukata:-
Koda
Albasa
Tumatir
Garin tafarnuwa
Magi
Kori
Garin citta
Attarugu
Man gyada
Koren tattashi
Hadi:-
A wanke koda ta fita fes. Sannan a yayyanka ta kanana sai a sanya ta a cikin tukunya tare da zuba mata ruwa kadan. Sannan a rufe. Idan ta fara nuna sai a yayyanka albasa da yawa a ciki a zuba yankakken tumatir da magi da garin tafarnuwa da garin citta kadan. Sannan a rage wuta sai a shiga gaurayawa. A zuba man gyada kadan sai a ci gaba da juyawa har sai albasa da tumatir da attarugu sun nuna. Sannan a kwashe a sanya a kwano. Sai a yayyanka danyar albasa da koren tattashi a zuba a kan kodar domin kawata girkin.
Za a iya cin wannan girki da dafa-dukar shinkafa ko kuma farar shinkafa da jus din lemun zaki.
A ci dadi lafiya.