Yadda ake Girka Miyar “Oha”
Abubuwan da za a bukata
Ganyen ‘Oha’
Gwaza kanana kamar guda takwas
Manja kamar cokali uku
Naman shanu
Kayan ciki
Kifi banda
Busashen kifi
Borkono
Magi
Kifi ‘Cryfish’
Hadi
A dafa kayan ciki da busasshen kifi da bandar ta yadda za su yi laushi sannan a wanke naman shanu a zuba a tukunyar da kayan cikin ke ciki da sauran kifin. A ci gaba da dafa su har sai naman ya nuna sannan a zuba magi kamar guda biyu sannan a ci gaba da dafawa na tsawon minti biyar.
Sannan a zuba dakakken borkono da dakakken ‘cryfish’ sai a ci gaba da dafa su na tsawon minti goma sannan a tafasa gwaza a kwaba ta a ruwa kadan a zuba .
A ci gaba da dahuwar sannan a zuba manja a rufe tukunyar har sai miyar ta dan yi kauri. Za a iya kara ruwan zafi idan miyar ta cika kauri sannan a gauraya sai a tsinka ganyen Oha da hannu kuma a yanka shi da hannu ba da wuka ba domin kada ganyen ya yi baki sannan sai a gauraya.
Za a iya cin wannan girki da sakwara ko tuwon samobita da sauran nau’o’in tuwo. A ci dadi lafiya!