Yadda ake hada gasasshiyar kaza da dankali

 Yadda ake hada gasasshiyar kaza da dankali

Kayan hadi:

• Kaza

• Dankali

• Man gyada

• Barkono

• Kayan kanshi

• Magi

• Tafarnuwa

• Gishiri

• Kori

• Ganyen fasili

Yadda ake yi:

Idan uwargida kika samu kazarki sai ki yanyanka ta sannan ki wanke. Daga nan sai ki zuba mata mangyada ki kawo kayan kanshi ki zuba a kai sai ki kawo jajjagaggiyar tafarnuwa ki zuba. Sannan ki zuba barkono da garin kori, sai ki cuccuda naman kazar nan don kowa ne nama ya cudanya da kayan hadin nan na dandano. 

Daga nan sai a ajiye kamar awa biyar ko kuma a yi hadin tun dare a sa shi a firiji. Hakan shi zai sa kayan hadin su shiga jikin naman sosai.

Daga nan sai ki dauko dankalin Turawa ki raba shi kamar hurhudu sannan sai ki dafa shi da ruwa sama-sama sannan ki sauke ki zuba shi a cikin naman kazar nan ki ajiye a gefe. 

Sai ki dauko farantin gashi ki zuba naman kaza da dankalin nan a ciki sannan ki dauko ganyan fasili ki zuzzuba a kai don kwalliya. Sai ki sanya shi a cikin Oben ki bar shi ya gasu zuwa minti 30. 

Idan ya gasu sai a fito da shi a ci.

Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top